← Book details Exiled Prince Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 23

Sashe 2

Exiled Prince Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ina ko amsa mishi tambayar shi Azim bai yi ba , ya rungume shi ya na sakin kuka kamar karamin yaro
a hankali shi ma Malik ya zagayo da hannayanshi a baya a Azim ya rungumeshi , da a ce zai iya yin kuka da ya yi shima

sai da Azim ya gaji da kukan nashi sannan ya dago da ga jikin Malik ya na fadin " Ina ka shiga ranka shi dade ? ina ka tafi ka bar mu ? kai da kanka ka ce mu ne ahalinka amma shi ne ka tafi ka bar mu ? ba ka san irin kangin da mu ka shiga bayan tafiyar ka ba , na godewa Allah da ba abun da ya same ka , don Allah kar ka tafi ka sake barin mu a hannun wacen azzalumin mutum " ya fada ya na hawaye bibiyu

a hankali Malik ya mike tsaye , sannan ya taimakawa Azim ya mike tsaye shi ma
hannu ya kai ya fara gogewa Azim hawayen shi ya na fadin " kar ka damu Azim , in sha Allah babu inda zan je , ko zan tafi sai na cire ku da ga hannun wacen azzalumin "

a hankali Azim ya gyada mishi kai ya na sakin wani dan karamin murmushin da har ya manta rabon shi da ya yi murmushi

a hankali Malik ya juya ya nufi motar shi da sauri Azim ya mara mishi baya , su na isa
ya bude gidan baya ya fiddo trolley din su
Malik kuwa ya nufi geffen Inaya , ya bude mata kofar , sannan ya mika mata hannu
ba musu ta daura hannun ta saman nashi , sannan ta sauko a hankali

Azim na ganin cikin Inaya ya saki wani kyawatencen murmushi ya na yi wa Allah godiya cikin zuciyar
cikin sanyin murya ya ce mata " ki shiga ina zuwa , su Ammie duk su na ciki "
gyada mishi kai kawai ta yi , da ga haka ya manna mata kiss saman forehead ya raba ta geffen ta ya shiga cikin motar shi

A hankali ta daga kafa ta fara takawa ta shiga part din MALIKAT HOUDA , Azim na biye da bayan ta janye da trolley

bakin ta da Sallama ta shigo parlourn MALIKAT HOUDA , nan ta tardo MALIKAT INAS , MALIKAT AL'UMU , mama , Tesnim , Nesrine , har ita kan ta MALIKAT HOUDA

Nesrine da mama na ganin ta su ka tashi da gudu su ka nufe ta , su ka rungume , su na sakin kuka
wata yar karamar dariya Inaya ta yi ta na fadin " Ashhhhhh , kar ka ku ji wa babyna , ciwo "

a tare mama da Nesrine su ka daga da ga jikin Inaya su na kallon katon cikinta
Godiya mama ta shiga yi wa Allah cikin zuciyar ta , Nesrine ma haka sai sakin murmushi ta ke

wani kyawatencen murmushi Inaya ta saki , ta nufi MALIKAT INAS da sauri ta na fadin " Ammie "

da sauri MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ka mike su na fadin " yi a hankali baby "
cak ta tsaya ta na murmushi har su ka karaso wajen ta , su ka rungume ta sannan su ka shiga tambayar ta ya jiki , ya hanya

gyada musu kai kawai ta ke ta na murmushi
cen cikin hannun MALIKAT HOUDA ta hango wani baby , ya na barci sai jijiga shi ta ki
washe baki Inaya ta yi ta nufi MALIKAT HOUDA ta na fadin " la mamie , baby ki ka samu ? "

a tare duk su ka yi wata yar karamar dariya sannan MALIKAT HOUDA ta ce mata " ba na son shirme , na Nesrine ne "

dan zaro idanu Ta yi kafin ta juya ta kali Nesrine , da ke tsaye ta na hawaye , irin kallon nan na tambaya
a hankali Nesrine ta gyada mata kai ta na murmushi allamun Eh

zama geffen MALIKAT HOUDA ta yi ta na fadin " mamie ba ni shi na rike " ta fada na mika mata hannu
cikin zolaya Tesnim ta ce mata " wannan katon cikin naki zai bari ki dauke shi ? "

" ni dai sai na dauki babyn Nesi " ta fada cike da shagwaba har da turo baki

" karbi , ba za mu iya rigimar ki ba , ai dama dole ta ce sai ta rike shi , ba mijin ta ba ne " MALIKAT HOUDA ta fada ta na daura Baby saman hannayan Inaya

da sauri Nesrine ta ce mata " yi a hankali kar ki murde min kan baby "
hararrar ta Inaya ta yi ta na fadin " to ina ruwan ki , ai ni ma na kusa samun nawa babyn " ta kai karshen ta na murguna mata baki

a hankali Nesrine ta karaso wajen ta , ta na fadin " ban babyna tun da haka ne " ta kai karshen ta na mika mata hannu

da sauri Mama ta ce mata " Nesrine wai biye mata za ki yi , kin fi san halin ta "

hararrar Inaya Nesrine ta yi kafin ta koma gefe ta zauna ta na tsuke fuska
a tare kowa ya koma ya zauna kafin MALIKAT INAS ta ce " baby , ina mijinki ya yi ? ba tare ku ka zo ba ? "
a hankali Inaya ta dago kai ta kalli MALIKAT INAS ta ce " a tare muku Ammie , ya ce akwai inda zai je yanzu ya dawo "

a tare duk su ka yi hamdallah , sannan MALIKAT AL'UMU ta ce " baby , ya kamata ki je ki huta ko ? "

noke mata kafada ta yi ta na fadin " ni tare da babyna zan tafi "
da sauri Nesrine ta ce mata " wane babyn ? kam , wlh tun wuri ki sauke idanun ki da ga saman babyna , in ba haka ba na yi miki duka kawo ruwa "

cikin nitsuwa Tesnim ta ce mata " Malik ko ya cire miki kai , gwara ki bi ta cikin ruwan sanyi ku rabu lafiya , dan in ta ce ta na son babyn nan ko mutuwa za ki ba abun da zai raba ta da shi "

marairaice fuska Nesrine ta yi ta na shirin magana , ta ga Inaya ta miko mata babyn ta na fadin " amshi , barci na ke ji "
da sauri Nesrine ta kai hannu ta karbi babynta
ta na karba Inaya ta mike tsaye a hankali , ta na dafe da cikinta , ta ce " mama , barci na ke ji " ta kai karshen cike da shagwaba

wani dan karamin murmushi ta saki ta na kallon ta , yau dai ga autar ta da ciki har ya kai watan haihuwa , ga kuma Nesrine da babynta , saura na Abdoul kadai ta ga burin ta ya cika , ga shi ko ta fara jiyo qamshin kamar Tesnim na da ciki

a hankali ta mike ta nufi Inaya ta riko hannunta , ta na fadin " mu je ki yi wanka ki konta ki huta , Nesrine kawo kayanta bedroom di na "

" bari zan kai " Tesnim ta fada , ta na mikewa ta nufi trolley din da Azim ya ajiye a wajen ta bi bayan su mama da su ka shiga corridor

( 🤔🤔 mama ba ki yi karya ba fa , ko ni na ga allamun ciki a jikin Tesnim , 🤣🤣🤣 )

❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤

🔥👑 ( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】

【 BOOK ________4 📚✍❤ 】

_______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________

{ P A G E ________ 3 & 4 ✍💕🔥}

▪MALIK AYMANE

zaune ya ke saman kujerar shi ta Gold
ya na rike da wayar shi ya na latsa , haka zalika duk mutanan wajen kowa na harkar gaban shi , sai hira su ke yi su na dariya

su na a haka Meli ya shigo da gudu babu ko sallama
ya nufi Aymane da gudu , kai tsaye wajen kunnen Aymane ya nufa ya yi mishi rada
a dubu dari Aymane ya mike tsaye har sai da ya saki wayar shi ta fadi kassa
a tare duk kowa ya juyo ya na kallon Aymane da ke faman zaro idanu baki sake har su na hada baki su na tambayar shi lafiya

ba su kai ga gama rufe bakunansu ba , su ka ga Aymane ya kai hannu ya damko wuyan Meli ya na fadin " karya ka ke , ba zai taba dawowa ba "

murya a disashe Meli ya ke fadin " ranka shi dade , ba karya na ke ba , da ido na na gan shi zai shiga part din MALIKAT HOUDA "

cikin bacin rai Aymane ya tura Meli baya har sai da ya fadi
ya na shirin magana idanun shi su ka sauka cikin na Malik , ya na tsaye bakin kofar shigowa Fadar ya rike hannayan shi a baya

a tare kowa ya mike tsaye ya na kallon Malik baki sake , wasu zuciyoyin su na bugawa
cikin bacin rai Aymane ya ce mishi " me ka ke yi a nan ? "

a hankali Malik ya daga kafa ya fara takawa ya karaso tsakiyar fadar ya na fadin " na zo karbar abu na , dama aro ne na ba ka "

wata shegiyar dariya Aymane ya yi kafin ya koma saman kujerar Malik ya zauna , irin zaman nan na qasaita ya ce " ko da HICHAM BIN JAABAR ne zai fito da ga cikin kassa , ba isa ya sauke ni da ga saman kujerar nan ba , bare kai ragon banza "

cikin bacin rai Malik ya ce mishi " kar ka kuskura ka kira sunan mahaifina "
Chapter 2 · 0% Book details