← Book details Exiled Prince Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 23

Sashe 14

Exiled Prince Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" na gode " Malik ya fada a takaice kafin ya juya ya cire security din kofar ya fice ya bar Diya nan tsaye ya na sakin murmushi
dama ya jima ya na son ya fadawa Malik wannan maganar amma ya rasa ta ina zai fara , amma yau ya samu kwarin guyiwar fada mishi , kuma ya ji dadi da Malik bai dauki abun wani iri ba , ya san da wani ne zai yi mishi wani kallon daban har ya yi kokarin kashe shi , amma Malik ko ajikinshi , shi ya sa ya ke Alfahari kasancewar shi dan uwa kuma amini ga Malik

▪MALIK

bakinshi da Sallama ya shigo room din da Inaya ke konce , nan ya tardo ta zaune saman gadon , ta na rike Nayel wata nurse na gwada mata yadda za ta ba shi nono , Nailah kuma har yanzu ta na barci da allamun ita ma ta gaji

har ya karaso wajen ba su lura ba , a hankali ya yi musu gyaran murya ya na fadin " za ki iya tafiya "

ba musu nurse din nan ta fice ta ba su waje
ta na fita ya janyo chair ya zauna bakin gadon ya na kallon Inaya
ta na ganin ya zauna ta turo mishi dan bakin nan nata ta na shirin magana ya riga ta cewa " no please kar ki min wannan shagwabar taki a gaban babyn mu "

ai ko sai da ta yi mishi shagwabar ta na fadin " ka ce mishi ya sake ni , zafi na ke ji "
" ki bari idan ya ishe shi zai saki " ya na gama fadar haka ko babyn ya sake mata nipple

wani dan karamin murmushi ta saki ta na kallon shi
a hankali Malik ya kai hannu ya dauki babynshi , wani dan karamin murmushin geffen fuska ya saki lokacin da idanunshi su ka sauka cikin na babyn shi

ya na a haka ya jiyo Muryar Inaya ta na fadin " la baby , da gaske murmushi ne ka ke ? " ta fada ta na dan leko face din shi
a hankali ya dago babyn ya kai bakinshi wajen kunnen babyn ni dai ban ji abun da ya ke fada ba

sai da ya gama sannan ya sauko babyn ya kalle ta ya ce " ba za ki gane ba , i'm just Happy to day , specially da ba abun da ya same ki "

marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " amma yaya Zayd ba za mu sake samun wani babyn ba ko ? wlh sai da na ji kamar zan mutu sai da na dinga ganin wutar lahira "

maganar ta ba karamar dariya ta so ta bashi ba amma ya danne kayanshi ya saki wani dan karamin murmushin geffen fuska ya na fadin " don't worry , Nayel & Nailah sun ishe mu , bayan su ba kari "

wani cool murmushi ta sakin mishi kafin ta ce " ta gaske Nayel ka saka mishi ? "

a hankali ya gyada mata kai allamun Eh
wani kyawatencen murmushi ta saki har da dariya , ta na kallon shi rike babynsu

" dubi har ya yi barci " ya fada ya na nuna mata Nayel da ya yi barci a cikin hannunshi
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " ba dole ba , ya na cikin hannun Daddyn shi dole barci ya dauke shi "

bai ce mata komai ba ya ci gaba da kallon Nayel , sai zuba mishi surutu ta ke amma ba ya ma jin ta tuni ya tafi duniyar tunanin shi

ya na a haka ya jiyo Muryar ta ta na fadin " baby , ina gudan babyn mu , ban gan shi ba "

Dum ya ji zuciyar shi ta buga har dan zaro idanu ya yi
da sauri ya dago kai ya na kallon ta , sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " wane baby kuma bayan Nayel ? "

a hankali ta girgiza mishi kai ta na fadin " baby , ni Nayab na ke cewa "

wannan karan har wani dishi dishi ya gani , ya a ka yi ta san sunan da ya yi mishi huduba da shi , dan tabbas sunnan Nayab ya saka mishi

a hankali ya bude baki Muryar shi har kerma ta ke ya ce " Cutie , Nayel ne ba Nayab ba "
da sauri ta katse shi da ta na girgiza kai kamar za ta yi kuka ta ce " baby , ni baby uku ne a cikina , ina gudan babyn , ina jin Muryar shi ya na kira na , in wassa ka ke ka bari please , ni ka kawo min baby na "

duk inda hankalin Malik ya ke sai da ya bi ya tashi ya ma rasa ya zai yi , ya a ka yi ta san da Nayab , bayan ya na da tabbacin ba ta cikin hayacinta lokacin da ya shigo duniya , in ma doctor ce ta fada mata ya a ka yi ta san sunan shi Nayab bayan shi bai fada mata ba

ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya jiyo Muryar mama ta shigo dakin ya na sallama
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya na amsa mata sallamar ta

Inaya na ganin ta ta saki kuka ta na fadin " mama , ki ce mishi ya fiddo min babyna , ina jin shi ya na kira na , amma wai ya ce shi bai san maganar me na ke ba , ni baby uku na haifa ba guda ba , ku medo min da babyna "

a hankali Mama ta rungume ta ta na fadin " Auta , duba ki gani " ta fada ta na nuna mata Malik da ke rike da Nayel

cikin rudu Inaya ta kalle su kafin ta juyo da kallon ta kan mama
cikin sanyin murya mama ta ce mata " kin dai gani , mijin ki ne kuma ya na rike babyn ku , ga guda kuma a konce , ki na tunanin da a ce uku ne ba zai fi ki farin ciki ba , amma kin gani baby biyu ne , kawai tunanin ki ne ya ba ki hakan "

cikin kukan nata ta katse mama da cewa " amma mama ina jin kukan shi , ina jin shi ya na kira na "

a hankali mama ta girgiza mata kai ta kai hannu ta fara goge mata hawayenta ta na fadin " tunanin ki ne kawai , please ki kontar da hankalin ki kin ji auta ? wannan su kadai ne babyn ku a yanzu sai wanda za ku samu a nan gaba , ai ki na so ko ? "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " mama da gaske biyu ne ba ? ba uku ba ? "

" no biyu ne Allah ya Albarkaci auren ku da su , ko ba ki son su ? "
da sauri ta ce " mama ina son babyna mana , fiye da komai "

" har ni ? " su ka tsinci Muryar Malik ya na fada
a tare su ka juya su na kallon shi , ya tsare su da ido
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " ina son ka fiye da tawa rayuwar "

gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya mike ya kontar da babyn saman gadon shi dan ya yi barci , sannan ya dago ya ce musu " yanzu na dawo " ya kai karshen ya na juyawa zai fita

har ya kai bakin kofar mama ta ce mishi " tsaya don Allah ina son na yi magana da kai , auta yanzu na dawo " ta kai karshen ta na sakin Inaya

ta mike ta bi bayan Malik su ka fita ita kuma Inaya ta koma ta konta

sai da su ka yi dan nisa da dakin sannan su ka tsaya mama ta ce mishi " na sani Triplets ne ta haifa , ban ga laifin ka ba dan ka boye mata dan kar ta cutu , amma ina jin wani abu wanda ba zan iya fada maka ba "

cikin rudu ya ce mata " ta ya a ka yi ku ka san uku ne bayan ni da doctor da nurse biyu ne kawai mu ka san triplets ta haifa , ko ita na yi mamakin yadda a ka yi ta san Triplets ne "

" Muryar shi ta jiyo , haka ni ma na jiyo Muryar shi ta haka ne na gane su uku ne ta haifa , but zan so ka koma wajen doctor ka tambaye ta ina babyn ka ya ke in ba ta gan shi ba za ta iya samun sukuni ba , haka za ta yi ta jin Muryar shi "

wani dogon nunfashi ya ja ya na saukewa a hankali kafin ya ce " ki yi hakuri mama , ba zan iya ba , na san in ta ji labarin shi ba za ta iya jurewa ba , shi ya sa na boye wannan maganar , ke ma ina rokon ki don Allah kar ki fada mata "

" amma ya ka ke so ta yi Muryar shi da ta ke ji ? "

" zan san yadda zan yi " ya na gama fadar haka bai jira amsar ta ba ya raba ta geffen ta ya wuce
a hankali ta juya ta bi shi da kallo na dan lokaci kafin ta juya ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya sannan ta koma dakin Inaya

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊

【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】

【 BOOK ________ 4 📚✍💌 】

_______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________

{ P A G E ________ 17 & 18 ✍💕🔥}

▪AFTER TWO DAYS
Chapter 14 · 0% Book details