← Book details Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 80

Sashe 61

Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Batasan yadda akayi ya shammaci rayuwarta har ta soma sabo dashi take kuma jin wasu baqin abubuwa a kansa ba,irin abinda bata taba jinsa akan kowa ba,koda kuwa cikin duniyar mafarkinta ko kuma hasashe.

Cikin qasa da mintuna biyar din daya dauka ya qarasa wargaza duk wani tunani nata. Sanda take takawa zuwa gida dauke da kalamansa masu nauyi.......ji ta dinga yi duniyar tamkar ita daya ce mace a ciki......dama haka zukatan dake da masu furta musu kalamai masu dadi sukeji?. Yau daya ta gasgata kalaman daya taba furta mata

"Har yanxu ke yarinya ce.....ba zakisan dadin rayuwa ba sai kinso kin kuma bada dama an soki......kowacce rai tana da buqatar wanda zai sota.....a lokacinne zaki karanci martaba da darajarki da kuma zamowarki cikakkiyar mace duk da qarancin shekarunki.

Hannunta takai tana shafa qaramar wayar daya bata wadda ke dauke da layi da kuma number dinsa. Ita kanta batasan adadin yawan roqon da yayi mata ba kafin ya karya zuciyarta ta aminta da karbar wayar ba

"Zanyi tafiya me nisan xango,a qalla zanyi watanni biyu ban saki a idanuna ba......bazan iya jurar rashin ganinki ba......" Kai take girgizawa a tsorace

"Yaa sabreen......"

"Ita kike tsoro?,zanje na nema dama a wajenta,kada ta rabani da abinda raina yakeso,zan roqeta ta barni na dinga jin muryarki....."

"Baka da hank......" Taji bakinta ya subuce da fadi.....sai kuma ta yiwa kanta waigi daga furta abinda tayi niyyar fada din a mugun tsorace. Yaa sabreen din da kullum kwanan duniya cikin kwatanta mata ta kaucewa sauraren kowanne d'a namiji har sai ta isa minzali?,yaa sabreen din da bata lamuncewa kowa mu'amala dasu ba komai kusancin dake tsakaninsu?,shine a yanzun yake neman kai kansa da kansa gabanta?.

"Huda......zan iya komai a kanki.....zan kuma iya komai saboda ke,ni kadai nasan zafin sonki da nakeji a raina.....don Allah ki karbi wayar nan......muryarki kawai xanji,daga gaisuwa idan kinso ki kashe wayar" . Ido ta zuba masa a mamakance jikinta kuma yana yin sanyi,wai dama haka soyayyar take?. Qwallar data gani shimfide a idanunsa suka karya duk wani qwarin gwiwa nata,kafiya da kuma dagiya,ta karbi wayar ba tare da tana da masaniyar ta karbi shiryayyen abu da zai wargaza musu rayuwa ba dukkaninsu......

Sake dafa wayar tayi sosai,qasan ranta tana jin qarin tausayinsa yadda yake faman marairaice mata,da alama soyayya ba qaramin kamu tayi masa ba. Dama wannan itace soyayyar?,dama haka akeji?,dama haka take iya canza mutum daga ainihin yadda ka sanshi?.

Ita kanta mamakin kanta takeyi yadda ya iya canzata gaba daya cikin qanqanin lokaci haka,amma kuma hakan fa yana nufin nan da shekara daya ko biyu kenan aure zatayi?. Tayi aure kuma yana nufin tabar yaa sabreen?,tabar nadra tabar haneefa?.

To wai ta yaya ma zata fuskanci yaa sabreen din da shi?,tace mata me?,bayan tsahon tasowarta idanunta basu taba gwada mata yaa sabreen din tana soyayya ba da kowa ma ballantana aure?,kullum zancanta yadda zasuyi zuzzurfan karatu kuma su zama wasu a gaba......wannan qudurin zai cika kuwa?.

Eh.... Wata zuciyar ta bata amsa daga wani gefan

"Shi karatu ai baya hana aure......kaman yadda aure baya hana karatu" Ta tuna da wata hira data jiyo 'yammatan ajinsu sunayi,abinda ya sanyata sakin murmushi kenan dai dai sanda take sanya qafarta cikin falon nasu.
*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 61

Dai dai lokacin sabreen din ke aje wayar mashkur wanda ya sanyata a lissafin yadda komai zaya kasance.

Shine mutum na farko daya matsanta mata da son ta bishi wani guri wajen garinsu. Da fari yaso ace dubai suka wuce,saidai tayi duk wata hikima tata ta kansile tafiyar da a baya ya tayar dayi musu shirinta gadan gadan. Baisan wace ainihin sabreen ba.....shi yasa ya gaza fahimtar dukka wadannan shirmen basa gabanta. Taqi kadan take jira ta yasar da qwallon mangwaro ta huta da quda.

A matse take.....kuma cikin matuqar buqatar kudaden saboda aikin ayshatu data tabbatar gab zuciyarta take ga kaiwa ga matakin da zata daina moruwa. Ko a jiya data ziyarci gidan jikinta yayi sanyi.......ta kuma sare sosai da yanayin jikin nata,har sun fidda rai da ita a wunin ranar,amma da yake shi rai idan yana da sauran shan ruwanshi a gaba to tabbas fa sai ya sha.

Motsin shigowarta ba tare da sallama ba ya sanyata daga fararen idanunta ta zubesu a kanta.

"Meye hakan kuma yau?" Tayi mata tambayar tana duban fuskarta wani abu yana darsuwa a ranta.

Fuskarta da fara'a ta juya tana fadin

"Au.......mantawa nayi wallahi" Saita tsaya daga qofar tana yin sallamar kamar yadda suka saba.

Sai data danyi jim kadan sannan ta amsa mata,ta bude labulen ta shigo,sabreen ta bita da kallo can qsan rabta wani abu yana kai kawo

"Sannu da gida" Ta fada tana nufar hanyar dakinsu,don sam ba'a sake take ba,Allah Allah take ta samu waje ta yiwa wayartata ajiya me kyau. Tasan halin yaa sabreen din qwarai da gaske,tana da mugun fikira da saurin dago wani abu dake a boye,a yanzun haka kallonta da takeyi din gani takeyi kaman tana kallon wayar ne tarwai bisa idanunta.

Bata iya amsa mata ba,tadai bita da kallo har zuwa sanda ta wuce dakin. Janye dubanta tayi daga bakin qofar dakin tana sauke numfashi. Bataso taji kokwanto ko shakka ko kadan akan 'yaruwarta......to amma haka kawai jikinta yake bata wani yanayi daban wanda bata saba jinsa ba akan huda din.

Duk da tasan ba kowa a dakin amma hakan bai hanata kallon gabas da yamma hagu da dama na dakin ba kafin ta ciro wayar daga aljihunta,ta kuma daga katifarsu daidai inda tafi kwanciya ta jefa wayar. Tana dagowa sabreen na daga labulen dakin ta shigo hade da sallama.

Wani mummunar faduwa gabanta yayi,ta amsa da sauri tana kuma waiwayawa,sai suka hada idanu da ita. Tsoronta ya qaru,ta dinga ji kamar ta ganta ne sanda take ajiyar.

Kanta da taga ta dauke shine abinda ya bata relief,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya ta fara fidda uniform din jikinta.

"Huda" Tayi kiran sunanta sanda ta zauna bakin gadonta.

"Na'am" Ta sake amsa mata tana sakin rigar uniform dinta data kama zata fidda.

Idanunta ta zube mata,kafin tace komai haneefa da nadra sun shigo,wanda already sun rigata dawowa harma sun sauya uniform dinsu zuwa kayan gida

"Gashi yaa" Nadra ta fada tana miqa mata Leda

"Kuje falo a samu plate a juye yasha iska,gani nan fitowa" Ta amsa musu tana binsu da idanu har suka fice kafin ta maida dubanta ga huda

"Zo nan huda" Ta umarceta tana ci gaba da karantarta. Ba musu ta ajjiye dan kwalin hannunta sannan ta tako ta zauna a inda sabreen din tayi mata nuni.

Zuba mata idanu tayi tamkar yau ta fara ganin fuskarta,abinda ya sake sanya ma huda fargaba da shakku

"Kinsan na tsani nayi tambayar meke faruwa?,akwai matsala?......a bani amsa da babu komai....bayan kuma da matsalar.....akwai kuma abinda yake faruwar" Ta qarashe maganar idanunta har yanzu cikin na hudan.

Har cikin qashinta taji tambayar tata tamkar taba hango komai tar tar,saidai kuma wani sashe na maganarsa ya bata qwarin gwiwa tare da hikimar kaucewar tuhumarta

"Tunda har akwai tsoron yaa sabreen a ranki,bai kamata ki bari a yanzu tasan muna tare ba,har sai mun sake shaquwa da junanmu.....ta yadda koda ta tashi rabamu,tausayin yadda mukeson junanmu zai sanyata ta haqura......akwai lokacin da na ware da zamu sanar mata......kinga koda kuwa na girme mata nesa ba kusa ba.....amma dole nayi mata biyayya kema na tayaki yi mata biyayya ko ba haka ba?" Wasu daga cikin kalamansa da a yau suka sake sanyawa ta sake masa. Yadda ya mutunta mata yayar da duk duniya bata da abu mafi girman daraja irinsa.....bata jin zata kasa sonshi a ranta.

"Me yake faruwa huda......kome qanqantarsa kada ki boyemin" Ta furta tana kallonta.

Kanta ta girgiza tana narke fuskarta

"Me kika gani yaa sabreen......?" Itama kanta ta kada zuwa gefe guda gami da cije lips dinta na qasa,daga qasan zuciyarta ana gaya mata lallai akwai wani abu da ba dai dai ba.

"Canji nake hangowa dan kadan huda......wanda kowanne canji cikin rayuwa daga kadan kadan yake farawa" Ta amsa mata kai tsaye ba wani kwana kwana.

Zama tayi sosai hudan tana dubanta

"Ba komai yaa sabreen fa.....idan ma akwai din ni bazan boye miki ba"

"Kin tabbata?" Ta jefa mata tambayar da wani nannauyan sauti dake tabbatar mata tambayar me girma ce dake dauke da tarin fassarori da ma'anoni.

Kalamansa sukaci gaba da bata confidence,har ta daga kai cikin tabbatarwa

"Na tabbatar" Ido ta lumshe tana gyada kai

"Shikenan" Sai ta miqe itama tana daukar daya wayar tata wadda ita ta shigo da ita dakin.

Mika'il takeson tabowa.......tana da buqatar fara kawar dashi daga layin,koda kudin visa passport da bill na asibitin ta samu daga gareshi,idanma so samu ne ya zamana komai ya fita daga jikinsa,ta yadda duk abinda zai samu daga bangaren mashkur din zai zamana tamkar ribar qafa ce.

Akwai abubuwa da yawa da yake list dinta wannan karon da takeson yi,wanda kuma yana da buqatar muquden kudade. Akwai mutane da yawa data kwana biyu bata gansu ba,tanason a wannan karon ta jiqa kowa yadda ya kamata.

Kaman yadda ta saba kebe kanta a dukkan lokaci irin haka da ya shafeta. Yanzunma can farfajiyar gidansu ta wuce bayan ta rabbatar ta sallamesu da dukkan abinda ya kamata. Me home work yana yi,me bita da hada haddar da zaya bayar a islamiyya ma yana nashi.

JIB ta kira,kamar ko yaushe layinta layine na musamman da ita kadai ke kiransa dashi,hakan ya sanya baya missing call,don muddin yaga kiran yasan akwai abu me muhimmanci.

Gaisuwar ban girma yayi mata kaman yadda suka saba sannan suka shiga tattaunawa kai tsaye akan ayyukan da takeso ta gama dasu

"Ka sani,ba kasafai nakeson dadewa da mutum ba.....nafison nayi na gama a wuce gurin ya sake sabon lale.....ciwon aishatu shine abinda yafi dagamin hankali najeeb......banason sanadiyyar wani ayshatu ta rasa ranta......inason sama mata lafiya tare da mata tanadin rayuwa da zata manta abinda ake kira da tsanani talauci ko wahala". Can qasan ransa yake hadiye wani abu,yana cika da mamakinta ako yaushe,tana yawan sanya ranta da kanta a risk,bawai don saboda jin dadinta ko walwalarta ba......aah......tana yin komai ne kawai don jin dadin wasu.
Chapter 61 · 0% Book details