← Book details Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 80

Sashe 52

Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bar wannan anni,wa yake ta tasa,ba abinda ya iya sai takurawa mutum ba dalili......hamma takurawarsa me dalili ne idan bakayi abinda yace ba ko baka kiyaye dokarsa ba......amma yaa saddiq.....hmmmm....ko wayar nan yanzun ya shigo yana ina dannawa sai yayi challenging dina" Ta qarasa maganar tana zamewa ta kashingida saman kujerar tana maida hannunta kan shafinta na X.

Ita da annin kowa ci gaba yayi da uzurin gabansa,wannan ya bawa falon daman daukan shuru na wani lokaci kafin ta daga kanta. Haka kawai ta qarewa anni kallo sai ta saki dariya

"Anni.....kinsan tsadar kayannan?" Ta fada tana kallon kwantaccen lace din jikin annin dake wani yauqi da santsi duk kuwa da cotton ne. Peach color da ratsin green,bashi da nauyi ko kadan

"Saikin fada 'yar kasuwa......" Ta amsa mata ba tare data dubeta ba

"Anni Allah hamma yana shagwabaki......ki zauna da kaya me tsada haka a gida duk dogayen rigunanki?....amma dai....to,hala abba aka yiwa kwalliya?" Ta fada qasa qasa tana qunshe bakinta da hannu. Kadan ta dubeta ta harareta

"Akwai kayan da sukayi tsadar da zan kasa yiwa abban kwalliya dasu?" Kai ta girgiza tana qoqarin maida kanta ga wayarta tana qoqarin boye dariyarta

"Babu anni.....anni ta abbanmu".

"Amna.... Qoqarin maidani kakarki kike ko?"

"Aah anni wallahi" Ta fada da sauri tana duban anni still tana son shanye dariyarta

"Kici gaba.....inajin zan dauki shawarar farouqu ne,zaki komawa nanna ne kiyi zamanki a can". Kyabe fuska tayi da kyau tana aje wayarta gefe kaman zata saki kuka

"Dama haka yaa farouq din yace?,duk haqurin zama cikin mazan da nakeyi ban da sister?....."

"Oho koma.meye gwara ki koma can,tunda kinga can dinma akwai mata 'yan uwanki sai kinfi jin dadi". Sosai ta sake kwabe fuska tana duban anni

"Da gaske anni zaki iya bayar dani?" Daga kai tayi ta dubeta

"Ba mace bace ke?,wataran ba aure zakiyi ba?" Ta tambayeta,ai kuwa saira soma matsa hawaye tana juyawa annin baya

"Ai dama na sani......gidan nan babu wanda yake sona sai hamma da abba na......shi dama yaa farouq kaman ya bayar dani kyauta yakeji.....ni bazanyi aure ba.....dake zan yita zama". Yadda tayi maganar zata yita zaman da ita sai ya bawa anni dariya amma ta dake

"Sai kiyi kuma" Tace tana ci gaba da scrolling sama tana duba adduo'inta.

"Kinga.....ki daina biyewa ta BB farouq.......indai ina nan ba wanda zai matsa miki.......i swear" Muryar musaddiq ta biyo bayan sallamarshi. Tuni ta miqe ta zauna sosai tana qoqarin goge hawayenta.

"Kaima kana biye musu yaa musaddiq wani lokacin.....amma dai ka fisu" Ta fada tana daidaita zamanta saman kujerar.

Qaramar dariya ta qwacewa anni tana qoqarin ajiye tab dinta a gefe

"Uhumnnn..... Ai dama ba kasafai akewa amna abun arziqi ba.....wanda ke mata abun arziqi kai tsaye a gidannan Muhammadu ne......har kun dawo?" Ta tambayeshi tana duban musaddiq dake dariya qasa qasa.

"Eh anni.....su abban basu iso ba?"

"Sun sauka amma basu qaraso gidan nan ba.....amma na tabbata suna dab da isowa don tun dazu suka tafi daukosu". Ta amsa masa tana miqa hannu ta karbi purse din nata da yake miqa mata.

Tana yunqurin budewa su kuma suna magana tsakaninsu shi da amna. Ta zuge jakar cikin rashin tabbas da yaqini,ta bude ne kawai don taga meye yayi saura a cik,me ta samu?,amma ga mamakinta sai ta samu komai a muhallinsa ba tare da an canzawa komai waje ba bare a cire wani abu,sai wayarta data nuna low battery da alama ba'abi ta kanta bama bare a sakata a charge.

"Ikon Allah" Ta fada,abinda yaja hankalin amna da musaddiq kanta

"Ba abinda aka rasa a ciki musaddiq.....ba abinda ta taba kota dauka" Ta fada da mamaki idanunta cikin jakar

"Nima dana bude nayi mamaki,amma nace bari na kawo miki ki duba komai bansan ko akwai wani abun daban ba"

"Aiko yadda na zuba kudin a jere ba'a canza tsarinsu ba" Ta fada tana sake fiddosu

"Amma dai ka yiwa yarinyar godiya ka karbamin number wayarta ko?,ko mamarta na sake yiwa godiya?"

"She's not natural fa anni" Ya fada a taqaice

"Kamar yaya?" Ta tambaya cikin rashin fahimta.

"To nidai anni ko qyallinta ban gani ba,a bakin wani waje wani ya tareni ya bani,baicemin komai ba ya juya,nima haka na juya da kan motata na dawo gida"

"Ikon Allah......gashi bata bari ko sau daya na mata godiyar alkhairin data yimin ba.....na kasa manta damuwa da kulawar data nunamin" Annin ta fadi tana juya abun a ranta.

Bai samu ce mata komai ba saboda qarar bude gate da shigowar motocin da suke da tabbacin baqinsu sun iso

"Alhamdulillah" Anni ta fada tana murmurshi gami da ajiye wayar da jakar a gefe.
*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 53

Dukkansu da sallaman a bakunnasu suka shigo. Suka amsa musu suna miqewa tsaye tare da dakon qarasowarsu cikin falon,saidai amna ta kasa jurewa. Da sauri ta taka zuwa bakin qofa ta riqe abbannata da kyau tana dariya idanunta saman fuskar fu'ad

"Abba sannu da zuwa....hamma....hamma sannu da zuwa" Ta furta matsanancin murmushi yana subuce mata

"Sannu 'yar abba qanwar hamma.....hamman dai aka matso a tarba aka fake da abba". Abban ya fada yana lakuce mata kumatu. Dariya suka saki fu'ad yana tayasu da murmushinsa

"Amnee......barkammu" Ya amsa mata cikin kulawa. Sakin abba tayi ta matsa dab da fu'ad din tana karbar briefcase dinsa

"Su amna an iya munahirci" Muryar sadiq ta shiga kunnenta,sadiq din dake tsaye ta bayansu abban. Gotasu tayi kadan tana leqensa,sai ta bata fuska

"Duk abinka bazanyi welcoming naka ba.....abba me yasa baku samu wata bolar South Korea kun yar dashi kun gudo ba?" Ta qarasa tambayar tana kallon abba a shagwabe. Ba wanda maganar bata bawa dariya ba a cikinsu

"Idan muka yar dashi ke zaki fara qorafin muje mu dauko miki shi ai"

"Allah bazan nemi wannan ba....."

"......me qarya?" Saddiq ya datsi numfashinta yana fadi idanunsa a waje

"Dan aljanna" Ta fadi tana juya idanunta abinda zai sake tabbatar maka da sauran quruciya a tare da ita,hakanan kuma tana fama da sakalcin auta da gasken gaske.

Kasa jiran isowar abban tayi,sai ta taka ta ruskeshi a tsakiyar falon. Ta rusuna tana masa sannu da zuwa gami da gaidashi duka tare da qoqarin amsar qananun tarkacen dake hannunsa. Cikin nashi tsananin kulawar da kallon kewa yake amsa mata,fuskarsa ta wadatu sosai da fara'a yana tambayar lafiyarta dama ta jama'ar gidan gaba daya.

Hankalinsa yana kansu,qauna da kulawar dake tsakanin anni da abba sune abu guda daya tak da suka rage wadanda suke bashi hope din wataran qila zai iya aure. Soyayyar da sukema juna wani irin dasashen abu ne da har yanzu yake tasiri a tsakaninsu,babu alamun gushewa sam sam. Yanayin rayuwarsun yana burgeshi,wata irin mu'amala annin kewa abba,irin mu'amalar da bai taba ganinta ba tsakanin MAAMAHnsa da ABBEY dinsa ba. Mu'amalar da bai taba zaton akwaita tsakanin miji da mata ba sai a wajen annin.

Gabanta ya qarasa shima kaman ko yaushe,cike da ban girman nan da yake jinsa har cikin ruhinsa ya tsugunna yana gaidata. Bata iya tsaiwa saman kanshi ba saboda girman shima da take bashi sakamakon sunan MUHAMMADU da yake dashi......da wata ajiyayyar kima da martaba da take ganinsa dashi saboda dattakon halinsa data sani tun bai cika shekara sha takwas bama a duniya.......uwa uba yadda yake tattalin farincikinta kadai ya sanya kowanne lokaci takejin tamkar jikinta ya tsaga ya fito.

"Lafiya alhamdulillah me babban suna.....jiki na warware tun tuni......dama ta jima bata tashi ba,akasi kawai aka samu a ranar,nafi tunanin kuma matar da mukayi salla tare ne turarenta yayimin qarfi da yawa".

Dan qwarya qwaryar zama sukayi cikin falon na duba lafiyar juna,qananun zolaya tsakanin amna farouq da musaddiq abban yana shiga yana raba gardama kafin daga bisani anni tayi umarni

"Abinci ya zama ready.....zaku shiga ku watsa ruwa tukunna ko?" Ta fada tana duban abba me gayya me aiki

"Hakan yana da kyau ko me babban suna?" Ya maida tambayar ga fu'ad. Murmushi kadan ya saki,suna girmama ra'ayinsa qwarai,sunan da yake dauke dashi ya bashi wannan girman a iyalin da suka san girma da martabar sunan. Wani abu da sam sam bai gani ba ga maamah,tana iya kiransa a lokacin quruciya da sunan ta kuma zabga masa zagi fada da sauransu

"To abba" Ya amsawa Alhaji hamza yana miqewa. Farouq ne ya miqe ya dauki luggage din fu'ad din yana nufar qofa

"Muje na taka maka badon halinka ba......don wallahi ka shiga uku duk sanda mukayi aure muka barka kai kadai a gidan nan". Yayi maganar qasa qasa yadda su abba ba zasuji ba.

Harara fu'ad ya zabga masa yana jan qaramin tsaki

"Sannu tattabara sarkin aure?,yanzun ma idan kaga dama ka koma mana ka gani?......ni gwara fa ku qara gaba ku barni daga ni sai anni ko mayi kumari". Dariya ya fashe da ita harda buga qafa kadan

"Kayi asara wallahi.....kai ta qara qiba ma kake,kaci gaba da gandamewa a gaban annin?,idan bakayi wasa ba gaba gaba sadakarka za'a bayar Allah......"

"Munyi asara dai ni dakai mayen aure......idan kun tashi kuyi shelata a masallacin juma'a".

"Basai munkai ga nan ba......owner na diamondchore resources company guda.......ko a sirrance akayi shelarsa mugun ciniki zamuyi Allah,a zaba maka guda hudu qwarara......matsalar kawai har yanzun ni kaina bansan color na macen da kakeso ba.....". Shammatar farouq din yayi yakai masa wani wawan duka sai daya qame,don maganar ta fara isarsa,yasan kuma farouq baisan bari ba,baisan ya isa ba.

"Kaci bashi......sai na dauki fansa.....ka qarasa cikin da kanka na fasa rakiyar" Ya fada yana jingine masa luggage dinsa daidai qofofin sassansu

"Tafi nono fari" Fu'ad din ya fada yana zura key ma qofan sassansa yana budewa,saidai fuskarsa kwance take da murmushi yana juya halin farouq din. Shi daya farouq din yakewa haka.....kamar yadda shima farouq din kawai ke akwai 'yar hakan a tsakaninsu.

"Alhamdulillah" Ya furta a sarari murya can qasan bayan ya isa ainihin bedroom dinsa,yana jin ma'anar godiyar daga qasan zuciyarsa. Tarin godiya ce fal zuciyarsa game da ubangijinsa,godiyar da har wani lokacin ya dinga jin baisan ta yadda zaiyiti ba takai gurbin da akeso. Ubagijinsa ya gama masa komai.....ya kyautata rayuwarsa fiye da yadda yake tsammani.
Chapter 52 · 0% Book details