← Book details Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 80

Sashe 60

Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A silent wayar take,amma hasken da take fitarwa ya ratsa rufaffun idanunsa a cikin duhun dakin.

Kamar bazai bude idanun nasa ba amma sai ya budesun a hankali yana saukesu akan wayar. Yayi tsammanin ya kashe duka layukan,sai a sannan ya lura guda daya ya kashe. Sunan daya gani saman wayar ya sanyashi sauke qafafunsa a hankali yana maida hankalinsa a kanta,ya miqa hannu ya daukota daga inda take ajiye yana qoqarin dagawa.

Sallama yayi amma muryarshi ta maqale,yadanyi gyaran murya sanda yajiyo muryar abban yana masa sallama

"Ina ka shiga ne?" Alhaji hamza ya tambayeshi

"Ina cikin gida abba"

"To fito......inason ganinka.....ka sameni falon anninka"

"To abba" Ya amsa masa a ladabce. Remote ya laluba ya dauko ba tare daya tashi a gun ba ya maida hasken dakin. Take yayi tarwai da haske kaman yadda ainihin dakin yake

"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla.....wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla" Ya furta muryarsa can qasa,yana jinsa gaba daya ba kuzari,tun daga zuciyarsa har zuwa gangar jikinsa.

Bai wani bata lokaci ba ya sauya kayan jikinsa sannan ya wuce sassan annin. Sallama yayi hankalinsa na kaiwa fuskar anni. Tun bai zauna ba jikinsa ya bashi akwai wani abu,don ba kasafai kake ganin fuskar annin a haka ba. A nutse ya qarasa shiga ciki,kai tsaye kuma ya nufi inda Alhaji hamza yake,wanda bai motsa ba daga wajen tunda maamah din ta fita ta barsu.

"Bismillah.....zauna" Alhaji hamza din ya masa nuni da kujerar dake kusa dashi. Sanda ya zauna din ita kuma anni ta miqe da zummar barin wajen,abban ya maida dubanshi kanta

"Zama kema zakiyi......ina zakije?" Duban abban tayi,kaman zatayi magana sai kuma ta fasa,ta koma ta zauna ba tare data sake cewa komai ba.

"Muhammadu" Abba ya kira sunanshi kai tsaye,abinda ba kasafai hakan ke kasancewa ba. Mamakin ya hanashi amsawa saidai ya daga kai kawai yana duban abban.

"Muhammadu ya ina yabonka sallah zaka kasa alwala?" Abban ya sake fada idanunsa still akan fu'ad din,tausayinsa kuma yana ratsa zuciyar abban.

"Abba....." Fu'ad ya motsa labbansa a hankali da zummar yin magana

"Me dame mariya tace maka tana da buqata wanda bakayi mata ba?" Ya masa tambayar Kai tsaye don sauqaqe masa wahalar tunani.

"Abba.....ba wani nauyi ko haqqi daya kamata na bawa maamah wanda bana bata shi......bana tunanin akwai wani abu da ya zama nauyi ko haqqi da ubangiji ya doramin wanda na gaza dauke mata shi". Har cikin zuciyarsa abban ya gamsu da wannan,saboda shi kansa ganau ne bawai jiyau ba akan hakan

"Na sani Muhammadu......amma don me yasa idan tana da buqatar kudi daga hannunka kake hana mata?". Sam baima kawo wannan zancan bane,sai ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana sauke kanshi qasa.

Rashin amsawarsa ya bawa abba amsar tambayarshi

"Me yasa kusan ko yaushe matsalarka da ita akan tana neman kudi ne ka hanata?,bayan Allah yayi maka wadatar da zaka iya bata ko nawa ne Muhammadu?" Ya qarashe maganar ta sigar tambaya idanunsa a kanshi,can qasan ransa yana mamakin abinda ke kawo musu matsala akan abinda yasan ya jima da fin qarfinsa.
*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 60

"Ka sani cewa......duk d'a aljannarsa tana qarqashin qafar iyayensa?,kuma haramunne jayayya dasu bare su buqaci abu aqi ayi musu?"

"Na sani abba.......amma bazan iya bawa maamah ko sisi ba". Sosai maganar ta bawa abban mamaki,har anni dake zaune daga gefe itama ta daga kai tana kalleshi

"Akwai abubuwa masu yawan da baka gama saninsu ba abba akan maamah......akwai boyayyun sirrikan dana ajewa cikina abba.......akwai wasu abubuwa masu yawa wadanda ba zasu fadu ba......amma koma meye cinta shanta lafiyarta dama suturarta wani abu ne da bazan taba iya hana mata su ba ko don albarkacin haihuwa da Allah ya bata........amma batun kudi abba........bazan iya bata ba"

"Dalili?,dalili nakeso naji Muhammadu" Abba ya sake tambaya cikin tsananin mamaki. Bai taba umartarsa da abu ba ya saba.....sai gashi s yau yana qoqarin bijire masa.......tabbacin akwai wani qaqqarfan dalili da kuma hujja kenan

"Abba...." Ya kirayi sunansa yana jin nauyin abinda zai furta din. Shurunsa ba abinda zai harfa tsakaninsa dashi sai gurguwar fahimta,bayaninsa din kuma bawai abu bane me dadin ji ko sauraro ba.

"Kasani Muhammadu.....koda baka bayar ba ni zan dauka na bata da kaina"

"Zan bayar abba.....zan bata amma bawai don zuciyata tana so ba......"

"Zuwa yaushe kenan?" Ya sake tambayar sa

"Zan yiwa sadiq magana,zai saka mata"

"Kirashi yanzu yanzu" Ya sake bashi umarni kai tsaye. Dole ya fidda waya ya turawa sadiq din saqon umarnin fidda kudaden,sannan ya aje wayar yana duban abban

"Zai sanya mata in sha Allahu". Ajiyar zuciya abban ya sauke. Shi kansa yasan akwai qalubale masu tarin yawa cikin rayuwarsa,to amma ko meye zaiyi yana yine saboda kyautatuwar rayuwa da kuma gobensu.

Kamar yadda ya saba lokaci bayan lokaci baya gajiya da yi musu nasiha dukkaninsu,yanzunma nasihar ce dai yayi masa.

Haka kawai sanda yake barin falon yaji hankalinsa bai kwanta ba. Muddin maamah tazo gidan to ya tabbatar akwai wani abu maras dadi daya biyo baya. Ko mene kuma ya farun yasan babu me gaya masa cikin gidan,daga amna sai musaddiq wanda baya gidan.

Yana takawa a farfajiyar gidan yana lalubar number amna din. Bugu daya ta daga tana amsa sallama a nutse

"Fito waje inason magana dake"

"To hamma" Ta amsa masa tana sauke plate din hannunta data gagara cin abincin ciki. Wayar tabi da kallo har yanzu muryar matar tana amsa kuwwa a kunnenta. Maganganunta sun girmi kunnuwanta,batasan komai a kanta ba amma tana ganin rashin kirki qarara daga dukkan wani motsi nata.

A tsaye ta sameshi idanunsa saman qananun shukokin dake bawa wajen iska me kyau da yanayi me dadi

"Zauna" Yace da ita yana nuna mata kujerar dake gabansa tare da qoqarin karantar fuskarta. Ba musu din ta zauna tana jin jikinta yana qara sanyaya daga kallon da taga yana yi mata

"Akwai baquwar da tazo gidan nan dazun?" Ya tambayeta yana kallon tsakiyar idanunta. Kallonsa itama tayi sai tayi qasa da kanta tana tuna gargadin da anni tayi mata

"Ba ruwanki da abinda tazo ta fadi,wannan ba abinda ya shafeki bane.....ba'a gaban kowa kuma akayi ba saike kadai...... Kada na soma jin zancan nan ya fita" Gargadin annin kenan bayan ta bar falon ta isketa a kitchen.

"Ehnnnn......kina nan sanda ta shigo na tabbatar......akwai wasu abubuwa data cewa anni da abba?" Ya sake tambayarta yana kallon fuskarta. Ba zata iya kallonsa kuma tayi masa qarya ba......hakanan ba zata iya saba maganar anni ba,don haka ta zabi sunkuyar da kanta ta kuma girgiza masa kai. Qaramin murmushi ne ya subuce masa wanda ba komai cikinsa sai bacin rai

"When kika fara yiwa hamma qarya amna?" Tambayar tasa saita rudata gaba daya,taji bata da sauran zabi illa ta shaida masa gaskiya.

Tambayar farkon data jefawa abban ita ta sanya fuad jan kujera shima ya zauna wani nauyi yana saukar masa. Ya ilahi.....wannan wacce irin jarabawa ce?,me yasa UWA take jin tasu jarabawar rayuwar?.

"Tashi kije" Ya bata umarnin daya sanyata miqewa da sauri tana barin wajen.

Tafin hannunsa ya sanya yadan daki goshinsa yana lumshe ido. A mizanin hankali da tunani da sanin ya kamata......yayi zaton maamah zata kasance ne cikin sahun farko na mutanen da ko kansu sukan sanya a gaba suka yanka ba zata ce komai ba.

****A hankali take takawa cikin layin zuciyarta na bugawa a hankali a hankali. Bugun zuciyartata ne batasan meye ainihin dalilin faruwarsa ba. Tsoron ganinsa takeyi ko kuma shauqin ganin nasa?.

Tun daga wancan ranar daya aike mata wasiqa ta qarshe bata sake jinsa ko kuma ganin motsinsa ba,har kawo yau da suke shirin cinye satin gab daya a kuma shiga sabon sati.

"Assalamu alaikum" Sautin sallamar daya sanya zuciyarta wani irinn bugawa ta ba zata,mamaki kuma da tsoro suka hanata amsawa saboda yadda taji alamun muryarta a shaqe take. Kasa waiwayawa tayi har zuwa sanda ya tako yana cimmata a inda take,ya zagaya kuma yana yiwa kansa matsaya a gabanta dab da ita. Yanayin kallon daya rutsata dashi ya hanata janyewa baya kaman yadda takeyi a duk sanda ya tsaya kusa da ita kamar haka

"Banga alamar kinyi kewata ba......inacan soyayyarki zata kasheni?" Ya furta yana karyar da wuya tare da komawa kalar tausayi ainun.

Idanunta ta fiddo waje tana dubansa

"Me ya sameka?" Ta samu bakinta da subucewa gami da tambayarsa kai tsaye.

"Ciwon sonki" Ya fada wani mayaudarin murmushi yana subuce masa. Nasararsa yake hange muraran daga idanun yarinyar,ya tabbatar yana dab da cika burinsa......yana kuma gab da daukan fansa.

Wata ajiyar zuciya taja tana sauke numfashi

"Bakiyi kewata ba huda sam sam" Ya sake fadi yana kalmashe wuya idanunsa cikin nata,yanason ya sake dasa mata dafin da zaiyi wahalar gogewa daga ranta. Yanason ya cimmata sosai,ya kuma nutsar da ita cikin tafkin qaunarsa fiye da yadda yayarta ta jefa masa qugiyar da har yanzu ya gaza zameta daga ruhinsa. Baya jin akwai wata mace da zata iya kashe masa qishirwarta. A kanta yakejin komai kuma ita kadai zata iya sama masa da wannan nutsuwar.

Saidai kuma ya karanci hakan wani abu ne da bazai taba samunsa ba.....don haka gwara yayi daukan fansan da zata gwammace bashi rayuwarta yayi yadda yaga dama da ita.

"Don Allah me kyau kice wani abu mana" Ya fada yana marairaice mata

"Nayi kewarka mana....." Ta samu kanta da furtawa. Yadda ya fidda idanu yana gwada mata mamakinsa ya sanyata jin kunya gami da mamakin kanta. Wani abu ne da yake faruwa da ita karo na farko a rayuwarta da bata taba tunanin zuwansa a nan kusa ba

"Da gaske kike?" Ya fadi har yanzu idanunsa a waje,sai tasa hannunta kawai ta lullube fuskarta dasu tana sakin qaramin murmushi,abinda ya sake fidda kamanninta sosai da sabreen.

"Don Allah yau daya ki bani aron mintunanki biyar" Ya fadi yana hade hannayensa waje guda. Mintunan biyar din da yake sanya ran a cikinsu zai qarasa dashen da ya dauko.

"Don Allah karkice aah,bazan sake neman wata alfarma ba daga wajenki ba daga wannan" Ya sake maganar yana qara marairaicewa da kyau.

Rabuwa biyu zuciyarta tayi,wani sashe na zuciyar tata yana cewa ta bashi damar.......yayin da wani sashen kuma yake cike da tsoro,tsoron da kusan kullum a cikinsa take.
Chapter 60 · 0% Book details