← Book details Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 80

Sashe 56

Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hamma....." Amna ta kirayi sunansa tana murmushi idonta a kansa.

"Lovy dovy" Ya fada yana xuba hannunsa a aljihun rigarsa yana jin karsashinsa da duk wani walwalarsa yana ja baya tamkar wanda aka tura gidan kaso.

Murmushi tayi,tsokanarsa takeso tayi amma kwarjinin nan nasa ya taso ya danneta

"In fada hamma?" Tayi masa tambayar tana dubansa

"Say it amna....." Ya maida mata cikin caring din daya kusa sanya matashiyar narkewa. Bata taba zato koda a mafarki yana da wannan siffar ta kulawa haka ba......bata taba hasashen akwai dabi'a ta sauqin kai a tattare dashi har haka ba

"Muhammadu.......yi tafiyarka......ku wuce ciki keda unaisa ku wankemin bottles dinnan,suna kitchen basu da yawa".

Duk da yaso ya wuce din kamar yadda anni tace amma dole sai daya dan tsaya a farfajiyar gidan suka gaisa da ma'aikatan gidan,sannan kuma me sunan malam yayi masa tattaki suka fice daga gidan bayan ya shaidawa security dinsa ba nisa zaiyi ba baya buqatarsu.

Yana takawa a nutse yana sake fuskantar gidan wani yanayi yana riskarsa,abubuwa masu tarin yawa da suka saba dawo masa a duk lokacin da zai gifta ko ya shiga gidan.....al'amura masu nauyin dake iya motsa zukata qwarai da gaske. Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka sanya yake janye jiki da rayuwarsa sosai daga gidan. Duk da komai na fasalin gidan ya canza,ba wani abu da yayi saura dangane da ainihin ginin gidan na baya,to amma dai wannan filin....wannan gurbin da wannan muhallin da aka aza tubalin ginin gidan har yanzu dai shine a wajen. Har yau har kwanan gobe idanunsa basa mantawa da tsarin gininsu na asali,wannan ya sanya idan ya kalli wasu guraren sai ya tuna da JADDA sai kuma ya tuna da ABBANSA,duk da guraren a yanzun sun sauya sun koma wasu abubuwan na daban,amma tambarinsu yana nan kafe qasan ransa da zuciyarsa.

Cike da girmamawa,martabawa tare da kallon Cikakkiyar kima da darjtawa malam sa'idu yake miqewa sanda ya fuskanci dosowarshi gidan.

"Barka da zuwa yallabai.....sannu da zuwa" Malam sa'idu yake fadi cikin mutuntawa.

"Barkanmu da warhaka baba.....mun sameku lafiya?" Fuad din ya furta shima cikin tsananin bada girma. Malam sa'idu bawai me gadi bane kadai a gareshi,yana da wani role da yake takawa da kuma wani ajiyayyen matsayi da fuad din ya bashi ba tare da sanin kowa ba.

Malam sa'idun da asalinsa me saida kayan marmari ne a bakin titin tsohon layinsu,wanda a yanzun layin ya koma tacan katangun gidansu yake,qofofin sun dawo bayan gidansu na asali,inda kusan gaba daya fuad din ya siye layin sai tsirarun gidajen da suke mazauna ciki suna da buqatar zama a ciki. Tun asali bayan layin nasu suna kiransa ne dama da layin 'yan gayu,don kusan manyan gidaje ne ata wajen,kamar yadda kusan mafi rinjayen unguwar tasu layinsu ne kadai keda qananun gidaje jifa jifa. To a yanzun layin duka ya zama qarqashin kulawar fuad da wani irin kwalta da aka zuba,gate a farkonsa da qarshensa da manyan fitilu jere reras.....cctv cameras da masu gadin layin saboda tsaron dukiyar mazauna layin da rayukansu.

Bayajin malam sa'idu zai iya ficewa daga tarihin rayuwarsa ko zuciyarsa. Yadda mahaifinsa baya iya cin komai haka malam sa'idu zai hada fruit ya bashi daidai qarfinsa lokaci bayan lokaci duk sanda Allah yakai wucewar fuad ta wajen,ana tsaka da haka malam sa'idu yaje ganin gida,bai kuma dawo ba har sai bayan wasu shekaru. Bai manta da yadda malam sa'idu ya nuna jin ciwon rasuwar abbansa ba,wannan ya sanya ko da rayuwa ta kawosu inda suke a yanzun ya nema malam sa'idu. Kyautata rayuwarsa yayi da gasken gaske ba tare da mutane sunsan da hakan ba......amma sai ya ajeshi a mazaunin me gadi bisa shawararsu da amintarsu shi da malam sa'idu din,kuma hakan bai hana ya bashi albashi ba duk wata,saidai ba irin albashin da ake jifan gamagarin masu gadi ba. Malam sa'idu baisan wace maamah ba bare anni,tun a baya wajen sana'arsa yake lazimtar zama,bai tara jama'a bare gulma dayi da gidajen alumma ya shigo ciki har yasan abinda gidan wani ke ciki,abu daya ne dai da har yau bai fahimta ba,jaddada gadin gidan da kula da shige da ficen matar gidan daya kasa tantance matsayinta a wajensa. Da yake bame damuwa da abinda bai shafeshi bane bai taba tambaya ba,yana dai aikinsa yadda akace,duk kuma abinda muhammad din yake da buqatar sani yana sanar masa.

"Mu zauna daga nan" Fuad ya fada yana neman wajen zama saman bencin da malam sa'idun kan dan kashingide akai wani lokaci.

"Aa haba yallabai.......ai sai ka bata kayanka kuma......bari a dauko maka kujera daga cikin gida kafin mutanen gidan su qaraso"

"Yi zamanka" Ya fada cikin ko in kula. Mamaki ya sake kashe malam sa'idu. Duk uwar dukiyar daya mallaka,kyau....ilimi duk basu sanyashi jin ya bambamta da sauran jama'a ba.

"Ita kadai ta fita?" Fuad din ya tambayeshi yana zaro wayarsa

"A'ah....su biyu ne" Ya amsa masa kai tsaye,don ba tambayar da zaiyi masa da zai boye masa wani abu. Kai ya daga yana duban malam sa'idu din jin ya ambaci ita da wata.....Allah yasa abinda yaketa qoqarin kaucewa da fatan kada ya faru ba shine ya soma faruwa ba

"Sun jima da fita?"

"Eh ya kusa awa biyu zuwa uku haka" Ya sake amsa masa. Idanu yadan zubawa malam sa'idu din kamar yanason fahimtar wani abu daga gareshi,sai kuma ya janye idon yana fesar da iska daga bakinsa,sai ya samu kanshi da Maida wayar aljihunsa kawai ya miqe daga zaman da yayi niyyar yi da,ya dawo gaban gidan ya tsaya sosai jikin realer da aka yiwa gaban gidan adon flowers da ita,idanunshi bisa hanya zuciyarsa na karanta masa abubuwa iri daban daban.

Tun dazun tunani da hankalin maamah yana kan hajja,har zuwa lokacin da mintuna kadan suka rage musu su isa ga unguwar

"Yarinyar can fa hajja kin kaita wata unguwar tana jira". Murmushi hajja ta saki da qaramin tsaki a hade

"Bari ki gani" Ta fada tana daukan wayarta daga saman cinyarta.

A hands free ta saka wayar,bugu daya ta daga. Akwai qaguwa sosai cikin muryartata,amma kuma bata isa ta nuna hakan ba koda da wasa kuwa

"Hajja na qaraso"

"To yayi.....na bar wajen,zan turo miki address na inda zaki sameni,na gaji gida nakeso na wuce,kada ki wuce minti biyar baki iso ba"

"To hajja" Ta amsa mata a sanyaye. Katse kiran tayi,murmushi na subuce mata ta kalli maamah

"Yanzu nan zata zo cikin minti biyar?" Maamah ta tambaya cikin mamaki

"Kuma mijinta shi zai maidani gidanma a gabanta ba....da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne". A gajarce ta tura mata adress din,sannan ta fara qoqarin kiran yahaya daidai sanda suke karyo kwanar da zata sadasu da shimfidadden jadda street din dake rubuce jikin wani qaramin allo dake kafe a farkon layin.

Tunda ya hangi motar ya ganeta kafin takai ga isowa. Yaci gaba da bin motar da idanu har ta qaraso qofar gidan,tayi kuma yi tsaiwar bawa malam sa'idu umarnin bude mata hanyar shigewa,sai a sannan ya sauke hannayensa yana duban tayoyin motar da sukayi bududu abinda zai shaida maka ba qaramar tafiya akayi da motar ba,tafiya me tsaho kuma cikin guraren da basu da shimfidadden titi ya saka kai yana wucewa ciki kafin malam sa'idu ya kammala bude musu gate din.

Kansa a qasa yake takawa cikin gidan,haka kawai zuciyarsa yakejin bai gamsu da yanayin fita da kuma shigowar motansu a yanzu ba. Cikin falon ya yiwa kansa gurin zama. Ba kowa a ciki,don dama muddin idan bata nan din bata aminta da masu aikin nata su kusanci falon har sai ta dawo.

Tun tsaiwarsu bakin gate din ta ganshi,wannan ya sanya driver yana aje motar qasan rumfar aje motocin ta bude ta fito

"Ya da sauri haka ko duk gajiyar ce?" Hajja ta tambayeta sanda take tattaro jakarta

"Yaroncan Muhammadu na gani,yana ciki yana jira,bansan tun yaushe ya shigo gidan ba.....banyi zaton jirgin safe zasu biyo ba" Ta fadi hankalinta yana yin cikin gidan. Da kallo hajja tabi maamah din ganin yadda duka hankalinta yayi cikin gidan,sai kawai ta jinjina kai ta soma yunqurin fita a motar itama tabi bayanta.

Qafafunsa na harde cikin juna yayin daya jingina bayansa da makarin kujerar,ya zube idanunsa duka a bakin qofa yana jiran ganin shigowarta. A wannan yanayin ta murda qofar ta shigo,tanata qoqarin azawa fuskarta rashin sukuni da gasken gaske. A wannan karon batajin zatayi masa da wasa akan dukka buqatun da zata bijiro masa dasu.....dole yayi yadda takeso wanda shine zai zama cikamakin burin MALLAKAR 'YA'YANTA.

Duk yadda taso tayi diban watsin tsiya dashi amma sai kwarjininsa yakeson bugar da ita. Hausawa sukace kuma wanda yayi me kyau ya sani haka wanda yayi maras kyau. Idanun da yake binta dashi sai ta dinga jin kamar yanason karantar daga ina take?,me kuma taje yi?.

"Sannu da zuwa" Ya fada a nutse yana zare qafafunsa daga cikin na juna daidai sanda take aje mayafinta da jakarta

"Ai kaine da sannu" Ta fada a taqaice tana ta tattalin fushinta da bacewar fara'a daga fuskarta,saidai kuma wani bangaren na zuciyarta yanata saka mata tsarguwa da kuma shakku.

Hada ido sukayi a karo na uku,sai ta kasa jurar kallon da yake binta dashi din

"Kana mamakin na baka umarni baka bi ba kazo na sameni a raye ban mutu ba ko?" Ta fake da wannan,don batasan da abinda zata iya qalubalantar kallon nasa dake mata wani irin nauyi da kwarjini ba. Idanun nasa ya sauke a qasa yana girgiza kansa,baikai ga cewa komai ba ta sanyo kai da tata sallamar.

Ita dinma dashi suka fara hada idanu,saidai nata kallon yafi na maamah tsini a nata idanun da zuciyar. Kwarjininsa ya cikata fal,hakanan alfaharin ganin farko wa mamallakin jadda diamondchore resources ya cikata.

Sunansa ya jima da shiga kundin nata lissafin,saidai a dukka hasashenta bata taba tunani ko zaton samunsa a nan kurkusa ba.....bata taba kawowa cewa yana da wata alaqa ta jini me kusanci irin haka da tsohuwar qawa kuma aminiyarta mariya ba.....bata taba hasashen mariyan tana da nasibin haifar babban mutum har kamar Muhammad jadda ba.
Chapter 56 · 0% Book details