← Book details Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 80

Sashe 33

Duniya Ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ta jinjina,eh yana da kyau hakan,ko ba komai a karon farko idanunta zasu ganeta komai da kyau......idanunta zasu gane mata yadda akayi amfani da kudi da jini da kuma quruciyar d'iyanta don shimfida kyakkyawan rayuwa ga wasu.

Cikin jin isa taqama gami da izza take taka kowanne step na stairs din,idanunta na sake qididdige mata adadin dukiyar da aka narkar wajen ginin gidan tare da qawatashi da kayan alatu dana alfarma na kecewa sa'a. Irin alatun da ita shine nata mafarkin,irin qawar da shine burinta DUNIYARTA. Yau ga komai a kusa......komai a dab da ita da sunan mallakinta.....amma wani taqi da kuma taku kadan sun hanata isa ga wannan bigiren. Iya lallausan carpet din da aka mamaye ilahirin stairs din dashi aka lullube tsadajje marbles din dake shimfide don kada anni taji sanyi cikin jiki da qashinta......duba daya zakayi masa kasan asalin tsadar da yake dashi. Wani abu ya dinga taruwar mata yana tsaya mata a wuya,wutar bacin rai taba taso mata kamar ta hallakata.

Sai da badawiyya ta fice daga dakin sannan anni ta janye idanunta ta maida kan musaddiq. Suna hada idanu sai ya janye dubansa daga kan annin ya mayar ga wayarsa. Ta tabbatar yaji komai kuma shima ya fahimci wacece tazo din. A karon farko kenan data fara tsomai qafafunta cikin gidan tun bayan data sake bayyana cikin rayuwarsu karo na biyu.

Yanayin yadda ya share din kamar baisan meke wanzuwa ba yadan sanyata murmusawa. A sannu a sannu hali da dabi'ar dan uwansa tana masa naso cikin jiki. Saidai bata da tabbas din shima dama yana da dabi'ar ne ta iya shariya dayin kamar baiga abu ba?,ko kuwa kuma daga bayane zama da madaukin kanwa ya sanyashi koya?.

"Musaddiq" Ta kira sunansa kai tsaye

"Na'am anni,akwai wani abu da kike buqata ne?" Yayi tambayar badon haka bakinsa yakeso ya fadi ba. Kai ta girgiza har yanzu tana duban fuskarsa. Cikin ranta tana jin inama wannan dukka tarin kulawar,.....wannan nuna damuwar da bata muhimmancin zasu rabata ko yaya yake da matar da suke kira MAAMA?. Saidai ta sani,TUN RAN GINI tun ran zane.....bakin alqalami kuma ya riga ya bushe......dawo dashi bisa zarafin aiki da damshinsa don gamsar da buqata kuwa aiki ne ba na yanzu yanzu yau ko gobe ba

"Ba buqatar komai......amma bakaji wadda tazo bane?" Ta sake tambayarsa

"Naji anni.....maama ce" Ya amsa mata kai tsaye. Kai ta sake jinjinawa,ta buda baki zata sake magana amma ya rigata

"Maama ce.....kuma bani da tabbacin alkhairi ya kawota" Ya sake fadi idanunsa na nuna akwai wani abu daya taba zuciyarsa. Fuska annin ta sauya tana rage adadin saketa da tayi a baya tadan tsuketa kadan

"Wato kaima kanason bin sahun dan uwanka kenan musaddiq?" Ta Tambayeshi cikin tsuke fuska. Kai ya jinjina sannan yakai hannunsa ya ture hularsa baya yana shafar sumarshi

"Ba haka bane anni.....akwai wasu abubuwa da wasu lokuta suke iya tasowa dan adam a matsayinsa na dan adam din,duk kuma yadda mutum yaso ya ture ya goge ko ya shafesu ba zasu taba barin zuciya da ruhi su huta ba".

" Ya isheni......tashi muje" Ta fada tana yunqurawa sannan ta miqe tsaye tana gyara lullubinta.

Tana sanya qafarta cikin falon qofar bedroom din anni dake falon ya bude. Anni ce a gaba musaddiq da ya bude mata qofar yana daga bayanta.

Kyakkyawan kallo ta sauke musu a sanda take tsaye tsakiyar falon tana kallon yadda dukiya ke magana da kanta cikin falon. A iya rayuwar da tayi.....a iye shige shige gami da fadin tashin da tayi cikin duniya tasan abu me daraja......tasan abu me tsada kamar yadda tasan abu me aji,don haka bata buqatar batawa kanta lokaci wajen sake nanatawa kanta a nan dukiyar da yaronta ya mallaka take tafiya,da gaske ne.....ba sharri bane.....hakanan ba cikin labarai na qanzon kurege bane.

Sanda suke takowa zuwa falon yana biye da anni saita gaza dauke idanunta a kansu. A hankali taji tashin hankalinta yana sake qaruwa. Kana musu duban farko a yadda suka fito shi da anni din baka isa duk masifarka kace ba diyan cikinka bane. Musaddiq ne.....musaddiq din da tun farar safiyar jiya bata sake sanyashi a idanunta ba bayan zaman jiransa data dinga yi na yazo suci abincin rana ko dare tare,abincin da ta yiwa tanadi na musamman,ta barar da kudade sosai a kanshi duka zai gashi ya tashi a tutar babu,sai gashi a yanzun tare da matar ya zame mata tamkar wani body guard a sanda nata idanun suke mararin son ganinsa tun jiya.

"Bismillah mana maama ku zauna" Anni ta fadi fuskarta lullube da murmushi sanda musaddiq yake dauke mata pillows din dake saman kujerar saboda taji dadin zama.

Tana jin kamar ba zata zauna ba,to amma kuma wani sashe na zuciyarta idan bar bata zauna daidai da nata zaman da tayi saman kujerun da tayi imani da dukiyar d'anta aka siyesu ba....lallai ta sake zama me daraja a kanta.

A nutse ya qaraso gabanta ya kuma rusuna har qasa a ladabce yana gaidata

"Barka da safiya.....mun tashi lafiya?"

"Lafiya qalau......ya mukayi da Kai jiya?" Ta jefa masa tambayar tana son boye fushinta don kada amina ta fahimci tarin galabarta a kanta ta kuma karanci rauni da ciwon da ta haifarwa zuciyarta.

*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997

PAGE 34

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 34

"Kiyi haquri......jiya mun fita da hamma farouq ne,mun samu baqi masu yawa a company,so kuma nike kula da fitar da kayan da kamfani ya sarrafa dole na tsaya har dare muka kammala muka sallamesu". Dubansa take sosai,sam harkar kayan gona da kayan abincin da yakeyi batayi mata ba,gani take kamar akwai wata maqarqashiya da shiri cikin abun. Taso ace shima kamar dan uwansa harkar diamond da gold yakeyi......ga kayan masarrufi da ma'adanai me zaa tsinta a kayan abinci?.

"Kai wai me ya hanaka bin sawun dan uwanka ne ma?,bayan duk duniya kaine mutum na biyu bayanni da bashi da kamarka?,don me zaka tsaya kamfani harkar kayan abinci?,kana zaune a Nigeria ya dauki bare ba dangin iya bana baaba ya tsallaka dashi yana nuna masa manyan harkoki kai kana zaune kana fama da sabgar shinkafa?". Boom yaji furucin nata ya masa tsawa saman ka,sai yakejin kamar ta samu ruwan zafi tana kwarara masa tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafukan qafafunsa..

A dabarance ya jefa idanunsa sashen da anni take,sai yaga kwata kwata hankalinta da idanunta baa kansu yake ba,ta aza dukka idanunta ga makekiyar tv plasma din dake aiki suna watso labaran abinda ke faruwa da mutanen Palestine. Yasan sarai taji,tana da wani irin matsanancin kara,ba sanin jiya ko yau ya yiwa anni ba......ballantana tana zaune a falon.....da zazzafa kuma kakkaifar muryar da maama take magana zaiyi wahala ace koda a bedroom dinta take ace bataji komai ba.

"Kalleni nan" Ta fadi cikin nuna zafinta ainun tana karantar yadda yake kaffa kaffa da kunnuwan anni

"Ka tashi ka bani guri,kuma indai ni na dauki cikinka.....nayi naqudarka,na kuma haifeka to tabbas anjima inason zama dakai.....dole nasan me kuke ciki don ba wani ya haifamin ba"

"Wannan gaskiya ne.....ai ita uwa tafi gaban komai" Zuwaira ta fadi tana satar kallon musaddiq daya miqe. Kallo daya yayi mata ya wuce yana yin gaba don bashi da lokacinta,hasalima baisan fuskarta ba baima gane wacece ita ba.....duka bama wannan ke damunsa......zafafan kalaman da ta soma fesarwa gaban anni su sukafi sanya masa damuwa,tun yanzu kenan?,me zata fada a gaba?,me kuma tazo dashi?.

Wannan tunanin ya tilasta masa jan burki akan rukunin kujerun dake dab da qofar sauka daga stairs din. Yana jin kamar ya zama dole ya tsaya din,kamar idan ya tsaya din zai iya tsaida wata barnar da dukka zata fito daga bakinta.

"Musaddiq......sauka zuwa qasa" Anni wadda tana kallonsa cikin qasa da second biyar ta karanci abinda yake shirin aikatawar. Idanunsa ya zubawa anni,ta karanci yana roqon ta barshi ne amma saita wofantar da roqon ta sake maimaita masa

"Ka wuce zuwa aikinka.....Allah ya bada sa'a,ka dawo lafiya" Ta furta a nutse kaman yadda ta sabawa kowannensu addu'a a kowacce rana,a fili ko kuma a boye.

Idanuwan mutum uku ne suka rakashi har sai daya kufcewa ganinsu. Nata idanun ta janye tana jin suna mata yaji yaji. Wato abun har yakai matakin da ita bata isa ta basu umarni ba subi?,abun yakai lalacewar da maganar wata itace gaba da tata maganar?.

"Barka da shigowa mariya.....fatan mun tashi lpy". Anni ta furta fuskarta qunshe da murmushi.

"Ba gaisuwa ce ta kawoni ba.....zuwa nayi na tambayeki sai yaushe zaki sakarmin yara na su dawo gareni kamar kowacce UWA?" Sautin kalmar uwa din yadan bada amsa kuwwa kadan cikin falon yayin daya dauke kowanne motsi da yake gilma falon na wasu sakanni. Tamkar me nazari haka anni ke kallon fuskokinsu ita da zuwaira,sai kuma ta gyara zama tana cewa

"Gwara da kika ce UWA baki ce MAHAIFIYA BA......wanne abu aminatu tayi kuma?" Tayi tambayar hankalinta kwance,tamkar yau ce rana ta farko data fara sanin wata me suna mariya kaf rayuwarta.
Chapter 33 · 0% Book details