Sashe 9
Dan Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Matarsa na manne da shi yake sanar da ita ranar lahadi mai zuwa za'a daura auren weediyan da Abdul ta yi guda saboda cikar burin diyarta ta auri wanda sunansa yake jerin masu kudin kasar nan. .HAUSA NOVELS DAN WAYE..... 3*13 .
NA ZARAU BABA YAKASAI . . *** *** *** *** *** .
WEESAL na zaune tana waya da Barek taji Guda.
"Ina zuwa zan kiraka yanzu zan danyi wani abu ne ". .
Ta kashe wayar ta mike da sauri ta nufo falon, tana sallama ta ce Hajiya me ke faruwa a Gidan nan? .
Abbanta ya sanar da ita abinda yake faruwa ta ji wata muguwar faduwar gaba ta juya zuwa dakinsu. . *** *** *** *** *** . .
Mah na zaune a cikin Gidansu na kauyen nan mahaifin Malam Bala kewayansu daki biyu da bayi a babu kicin suna hura wutar Itace a Tsakar gida maganar gaskiya ba su saba rayuwar KAUYE ba amma ta fi musu dadi saboda zasu tsira da mutuncinsu . taimakon ALLAH da ya yi musu dama suna yawan ziyarar garin shi yasa mah tana zaune da 'yan gidan lafiya mubarak ne dai ba shi da wani tartibin ABOKI a Garin don shi bai fiye zuwa ba GARIN PANDA akwai shi da jama'a wanda babu laifi zuwa yanzu akwai 'yan boko saboda haka akwai cigaba a cikinsa haka yaransu mata suna zuwa karatu don yawancinsu sune Daliban SUMAILA, ALBASU da KACAKHO haka yanzu matasan suna zuwa JAMI'AR WUDIL saboda haka akwai 'YAN BOKO a garin babu laifi yau da gobe ta sa mubarak ya soma sabawa da matasan garin. .
Akwai karamin daki wanda mubarak ke amfani da shi karauni ce a ciki sai gidan sauro sai 'yar karamar Rediyo a lokacin ila ya shigo dan wan Malam Bala ne Likitane a Asibitin Wudil haka yana duba 'yan GARIN PANDA a duk weekend Dr.Isma'il ya shigo dakin mubarak yana kallonsa cike da tausayi ya ce anan ka ke kwana mubarak ya gyda kai ya ce me zai hana to ka dawo dakina ya ce ni bana son rayuwar ma gaba daya don komai ya fice min a rai ya ce kada ka damu duk jarabawa ce mu shiga ciki mu gaida mah . ko sun isa sun tarar da ita tana faman hura wuta hayaki ya turnike wajen Dr.Isma'il ya ce mah ina Risho dinki ba sai a siyo Kalanzir ba amma tunda ba ku saba amfani da wannan ba za ki cutu mubarak ya ce mah bari in zo in fiffita miki ta ce haba dai ai sai ka yi kaurin hayaki nima ruwan wanka na dora ta shinfida musu tabarma ta zubo musu kunun da ta dama ta ce ila ga kunu ku sha murmushi mubarak ya yi ya ce Likita kana shan kunu kuwa . daganan suka soma hira akan shan kunu, haka suka cigaba da yi har suka gangaro kan shari'ar Dr.Isma'il ya ce babu komai zai sa ayi bincike insha ALLAHU za a samu fayel din in ma ba a samu ba ai akwai gwajin da za a yi wanda zai warware komai shine gwajin . kwayoyin halitta da kuma gwajin jini (N.D.A.) shi kadai in anyi zai fidda komai za a gane DAN WAYE? .
Dadi ya rufe mah ta ce gaskiya matar nan ba zan yafe mata ba Isma'il ya ce na ji an ce kun sa gidanku a kasuwa bai kamata ba kada ku siyar in komai ya lafa za ku koma ta ce anya kuwa? .
Banjin haka ila saboda na tsorata da masu kudi, mubarak ya ce Barr Lu'u Lu' u tana son ganinki kuma weediyan ranta ya baci, . wai me yasa za mu taho ba ta sani ba. .
Mah tayi murmushi ta ce yaro man kaza, kyaleta ya ce za su zo ta zaro ido har nan kauyen lallai wannan yarinyar 'yar arziki ce ni ban san in zan sanyata a zuciyata ba kai kowa da yadda ALLAH ya yi shi amma weediyan yarinyar kirki ce mubarak ya ce ai ita haka take ko balle da kowa ma za ta iya taimakonsa .
Isma'il ya ce akwai irinsu a duniya sai dai ba su fiye yawa ba. . *** *** *** *** *** .
Mustapha ya bude wayarsa ya ajiye ya shiga wanka ya fito yana shirya jikinsa Mustapha mutum ne dan kwalisa yana shirya sai da ya shirya tsaf yana kokarin daura agogonsa a lokacin Daddy ya shigo ya ce ka shirya zamu fita ya dan rusuna yana kwasar gaisuwa ya rike hannunsa ya ce na ji dadi domin a yanzu na ga ka yi tawakkali hakan ya nuna min addu'a ta ta amsu mustapha ya dora glass a fuskarsa shi ne yake tukin motar Daddy a gefensa suna tafe suna hira irin ta da da mahaifi ...........DAN WAYE...... 3*14 .
NA ZARAU BABA YAKASAI . har zuwa kamfanin robobinsu da ke unguwar sharada, shigarsu ma'aikata suka rinka kawo gaisuwa sun isa OFFICE din yau za su yi meeting ne Daddy wani dadi ya cikashi saboda ganin mustapha ya saki jiki ya kwantar da hankalinsa haka suka gama meeting daga shi sai shi a Office yau dama ina son in ji ya ku ka yi da yarinyar da ka ke so saboda ina son ayi bikinku tunda ba karatu take ba ya ce to ai Daddy kaine mai magana ya ku ka yi da mahaifinta ya ce dama wai aiki za ayi ma ta ni kuwa ALLAH ya sani da za abi shawarata da an kyaleta saboda kada a janyo ma ta wani ciwo Daddy ba a kurma aka haifeta ba ya ce to ya aka yi suka sake ya ce ai da ba a hannun mahaifinta ta ke ba kuma sakaci aka yi . to amma yanzu yaushe ne aikin mustapha ya ce zan je gurinta Daddy ya ce zuciyata tana son in aurar da kai saboda haka zamu tsayar da magana da yarima musbahu . ok Daddy duk abinda ka yi shi ne dai dai. . *** *** *** *** *** .
Izzatu tana kwance akan kujera idanunta na kwararar da hawaye yanzu take son mustapha kuma ba za ta bari a rabata da shi ba don ita kanta tana mamakin yadda har ta bari soyayyar mustapha ya shigeta haka a lokacin Surayya ta shigo tayi kasake tana kallonta mamakin yanayin da ta ganta take ta furta ma ta lokacin da suka fuskanci juna ki je mustapha na jiranki . ta zauna tana kallonta ta ce ki je ki shirya taro masoyinki daga hannun 'yar fashin miji cikin kwarin guiwa ta shirya sanye da doguwar Riga yellow da adon marum a jikinta . ta yane kanta da mayafin marum haka flat shoe dinta marum ne Surayya tayi ihu wow yayata za ta ruda mun mustapha kin san duk ajinsa ki ruda mun shi ta ce Surayya mustapha na mai kyau ne yana da aji na san sona yake ke de kawai kin ga yadda mata ke sonsa . ta ce ma za je ki furta masa kaunarsa ta rinka jin dadi a haka ta rinka taku har ta isa inda yake ajingine yake da motarsa tabbas mustapha yana da kyau da iya tsara kwalliya hansome guy ne kafin ta karaso ya karasa yana murmushi ta ce amincin ALLAH ya tabbata a gareka . murmushi yake yana dubanta kawai yana tura ma ta SAKONNIN KAUNA ta idanuwansa ta ce mu je ko sun isa wajen aka ajiye kujerun roba kasan bishiyar mangoro ya zauna yana dubanta don ya san yau rigimace za su yi amma sai ya ga sabanin haka murmushi ne akan kyakkyawar fuskarta ta ce sannu da zuwa ya ce ya mutan gida ta ce lafiya ta ce ina yar fashin miji dariya ta kwace masa ya ce AMARYARKI ce ta rufe idanunta sai kuma ta budesu gaba daya ta ce kai kana nufin mata biyu za ka aura ya ce na sani zan fuskanci wata rayuwa kila ta zo da sauki kila akasin haka ta girgiza kai ta ce ba zan bar mata kai ba za mu yi yaki ni da ita wanda yaci gari shi ne mai mustapha da ayi haka ta ce yau zan fuskanci sabuwar rayuwa don yau na gano ba ni daya ba ce a cikin zuciyar mijina dariya ta kwace masa yace Izzatu . gaske ne kina sona yau mafarkina zai zama gaskiya yadda Izzatu ta nuna masa kauna da soyayyarta abin ya firgitashi don ta nuna masa babu gudu babu ja da baya shi din take so kuma ba ta tsoron su yi tarayya da wata a kaunarsa wata irin murna ta kamashi koda bai san shi DAN WAYE ba lallai ya tabbata dan gatan Izzatu ko haka ALLAH ya barshi kam ya ji dadinsa Izzatunsa ke furta kalmomin soyayya a gareshi bai san lokacin da nishadi ya kamashi ba. .
Ya isa gida cike da nishadi haka kawai yake jin wata annashuwa zuciyarsa fes cikin haske ba ya jin bacin rai ko kadan yana shiga dakinsa ya yi tsalle ya haye gadonsa yana shafa kirjinsa ya kalli Gadonsa ya na fadin wannan gadon akanka nake kwanciya inyi mafarkin Izzatu lallai yakamata ace na fada maka dunbin son da Izzatu ta ke mun, . anya kowa ban zauce ba kila son Izzatu ko farin cikin da ta sani yana neman zautani ya mike zuwa cikin gidansu a falo Daddynsa ne a harde ya durkusa gabansa yana dariya yace fuskarka ta nuna abinda ke zuciyarka ke dauke da shi na nishadi wanda ni dama babban burina bai wuce inganka cikin farin ciki ba shi yasa nakeson wannan Izzatun ita ce sanadin mantar da kai matsalar da muke ciki ya ce Daddy tana so na fiye da yadda ka ke zato ya shafi kansa yace ni na san na haifi da tamkar da dubu ni na san babu macen da ALLAH zai bata kai ta ki ansa hawaye ya gangaro a fuskar mustapha ya uwata bata so na ta tsaneni shin in ni din ba danta ba ne to ni din DAN WAYE? .
Daddy ALLAH ya dora mun kaunar iyayena shin ya zanyi ?