Sashe 3
Dan Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka ta gama zagayawa ta iso Office din shugabar wajen ta zauna ta kalleta jikinta a sanyaye jiya an kawo Jaririya Gidan nan sai dai ba mu da Madarar Yara a gidan weediyan ta ce ina mamakin yadda rayuwar marayu take kasancewa wai Gwamnati da masu kudinmu suna mantawa da su ne . ma'aikaciyar ta yarfar da kai ta ce Gwamnati na iya na ta kokarin kin san abun ne da yawa shin in tambayeki da ace ni mai kudi ce ina da 'yanci ko damar da zan iya gina Gidan marayu da na gina don na taimaka musu ta ce kina da wannan damar abun da har yanzu manyan Attajiranmu suka kasa ne shin da za su iya daukar dawainiyar bude irin wadannan Gidajen su cigaba da kula da su lallai da sun yi sadalatul Jariya yakamata ace mun dinga kulawa da bukatunsu ta mike ta ce bari inje in kawo muku madaran ta fice a motarta bata jima ba ta dawo dauke da madarar mai yawa ta ce insha ALLAHU zan ci gaba da taimako dai dai iyawata. .
A lokacin weesal ta kirata a waya ta sanar da ita ta yi ma za ta dawo Gida ta yi baki, ta yiwa shugabar Gidan da ma'aikatar gidan da yaran sallama ta tafi. . . *** *** *** *** .
A Gidansu weediyan iyayen Abduljalil dara-dara ne suka kawowa weediyan ziyara sam ta san tana son kudi kuma burinta bai wuce ta taimaki al'umma ba shin ta wacce hanya hanya zata fara a gaskiya zuwanta Gidan Marayu a yau ya sake sanyata son kudi kwarai wai ace kamar madarar da za a bawa jaririn da aka tsinto tana wuya shin ina kudin al'umma suke ina masu kudi ina 'yan siyasa haba bayin ALLAH me ya sa bama kai ziyara irin wadannan gurin da manyan Asibitoci ? . mutuna ma'aiki (S.A.W.) a cikin Hadisinsa mai daraja ya ce imanin dayanmu baya cika hai sai ya sowa dan uwansa abinda ya sowa kansa, . amma me ya sa mu ka yi watsi da wannan umarni da koyarwa ta Annabin Tsira muka fifita son kanmu fiye da kowa, muka sowa kanmu kyakkyawar rayuwa amma mu ki taimakawa wani ya yi kyakkyar rayuwa idan mun gan shi a cikin rayuwa mara kyau ko wadda yake bukatar tallafi? .
Da irin wadannan tunane-.tunane ta shiga gida Tun a kofar Gidan ta ci karo da manyan motoci ta shiga ciki ta sami weesal tana ta fama a kicin ta ruko hannunta ta ce iyayen abdu dara-dara ne suka zo ta kalleta ta ce 'yar uwata daga ina ki ke kina da damuwa me ke damunki ta ce babu lokacin sanar dake yanzu ki bari sai anjima. .
A lokacin Hajiyarsu ta karaso ta ce'YAN BIYU lafiyarki kuwa ta ce babu matsala ta ce ki shirya ki zo falo sirikarki ce ta zo ita da 'yan uwanta ta ce lafiyarki kuwa ta ce yes ta ce weediyan ya ya dai ta juya ba ta yi magana ba saboda zuciyarta a cunkushe take. . *** *** *** *** .
Cikin takun isa irin na wayayyun mata masu Aji wadanda suka yarda da kansu ta daga Labulen Falon ta shiga murmushi a fuskarta tana daga kafarta tamkar tana kan kaya a tsanake take Samiha ta karaso ta ce oh!
Matar Bros kin iso ta isa da ita inda Hajiyan Abdul take ta rungumeta a jikinta tana jin kaunarta tana ganin za ta bata farin ciki 'yata ba ki kirani a waya ko ba ki bukatar albarkata ta ce a'a ina son albarkarki Samiha ta ce matar yaya sunana SAMEEHA yau na zo in ganki sai na ga kin fi inda Bros yake fasalta min ke murmushi tayi an kawo musu duk kayan bukata. .
Hajiya marka suna falo ita da Hajiyan Abdul ta ce ba ki sanar da mu zuwa ba ta ce mun zo kan batun Biki saboda ba zamu iya jiran har sai an hadasu ba shi ne na zo in sanar da ku ayi mana alfarma ta ce wannan batun Iyaye maza ne ta ce alfarma zamu nema Abdul yana bukatar Iyali a kusa da shi don na san yin hakan zai sa ya dawo gareni shi ke nan zan sanar da mahaifinsu yadda muka yi shi kenan haka suka zuba musu garar arziki . . weediyan taji dadi don tana bukatar kudi ba ta boyewa mahaifiyarsu ita kanta ta san halin weediyan tun tana yarinya ta ce shi ke nan amma ki taka a sannu na san ALLAH yana tare da ke tunda ya san zuciyarki amma ita duniya komai a sannu ake tafiya da ita ki dage da addu'a ALLAH ya cika maki burinki koda yaushe nima kullum addu'ata ALLAH ya cika burin weediyan.DAN WAYE....... 3*4 .
NA ZARAU BABA YAKASAI . .
Weesal ta ce hajiya kuma yaushe ne za a tsayar da bikin weediyan ta harareta sannan ta ce hajiya ina so in ga karshan shari'ar su mustapha saboda in na yi aure kila ba zan zauna a kano ba kila Ma ba zan zauna a kasar nan ba ni shi ne babban abin da yake damuna gaskiya su yi hakuri Hajiya ki taimaka in ga karshen abin da yake faruwa ta ce ki nemi ZABIN ALLAH weediyan lamarinki na tsoratani. . *** *** *** **** *** .
Hajiya lami zaune gefe Hajiya saratu ce itama duk jikinta ya yi laushi don ta rame Hajiya Lami ta ce kalli inda ki ka tashi hankalinki haka kin tada namu haka kawai kin sakamu cikin masifa cikin rudin al'umma ta inda mutane suna ta zaginki haka kawai kin san baki bala'i ne. .
Hajiya saratu cikin tsananin sanyin murya ta ce Hajiya ke uwata ce kowa ya juya min baya ke ya kamata ki ji tausayi na wallahi mubarak DANA NE! .
Ran Hajiya Lami ya kara baci ta ce kin ga abinda bana so ki fada haka kawai kin cutar da mijinki kin dawo gida kin barshi saboda ba ki mai da ni a bakin komai ba a to ai duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan doka,jama'da suka dauki niyyar taimakon baiwar ALLAH da ki ka dauki hakkinta suna da yawa,ga shi jibi za a koma kotu ni na matsu in ga karshen tatsuniyar nan ta ki. .
Kuka Hajiya saratu ta fashe da shi ta ce Uwa ta fi kowa son danta shin me ya sa ke ki ka ki yarda da ni ta ce ina gwwajin kwakwalwarki ko baki je ba ta ce ni ina da hankali ba sai na je ba ta ce zancen banza ance miki Alkalin wasa ne ai dole ka bi fadar Alkali in dai kina son cigaba da shari'ar dole ki je ki yi ta girgiza kai ta ce Hajiya nima fa wani lokace se in ganni kamar tababbiyar hakika ina zaton ba kaina daya ba lokaci ya yi da zan nuna muku cewar ni din motsattsiya ce Hajiya ta bita da kallo tana mamakinta. . *** *** *** *** .
Likitan da yake kula da Alhaji Abdulmajid ya ce ALH ka yi hakuri ka cire komai a ranka saboda damuwa na illata rayuwar dan adam. .
Ba zaka taba gano damuwata ba hakika ALLAH shi kadai ya san abinda yake damuna Likita ya ce to abinda na ke so da kai ka huta kwana biyu ya ce ina tunanin hukuncin kuliya ina tsoron yadda zamu kare a kotu Alhaji ka yi addu'a ALLAH zai bayyana gaskiya ka ji babu yadda Alhaji abdulmajid ya iya dole ya kwanta Likitansa Dr.yassir Ibrahim ya kira wayar mustapha ya sanar da shi hankalinsa a tashe ya ce insha ALLAHU zan zo dama jibi ne zan zo Likita ya ce don ALLAH babanka jininsa ya hau sosai ina jin tsoron kada ya taba masa zuciya kada ka rinka nuna masa damuwarka ka zama jarumi ka ji ya ce na gode Dr. yassir . zan kula da Daddy bana so in rasashi shi kadai ya rage min ya ce ka kwantar da hankalinka tada hankalinka za a yi biyu babu saboda haka ku yi hakuri mijin Izzatu murmushi ya yi don jin dadinsa. . . *** *** *** *** .
Izzatu an sauka kasa mai tsarki don za su je ganin yadda ake gabatar da GASAR MUSABAKA ta duniya sannan za ta je ganin likita don soma bincike suna zaune a masaukinsu tana kwance tana hutawa ta hau online ta tura masa; .
''me sona lokaci ya yi da zan fada maka ina sonka son da ba zan misalta ba ina tausayinka bana so ka dami zuciyarka izzatu na tare da kai ruwa ko iska gumi ko dari ba za su rabani da kai ba ko ka san sonka tunaninka tsun matsawa zuciyata. .
I wonder why i'am missing you so much. .
A lokacin da sakon ya sameshi suna tattunawa da Alpha murmushi ya yi ya mayar ma ta da da amsa yana jin sonta da kaunarta na sake samun mafaka a zuciyarsa. .
"Izzat ina tsananin sonki, ina tsananin son kasancewa da ke ba nida burin da ya wuce ace ni da ke mun zama ma'aurata ina son in gammu a matsayin ma 'aurata.
I Love you too! . ko da ta karanta tamkar yana gurin duk sai ta ji kunya ta kamata.
Ta sake tura masa da wani sakon. .
"My one ina kasa mai tsarki mai girma wato saudiyya, ka yi min addu'ar samun nasarar abinda muka je nema (Aikin kunne)" . koda sakon nata ya isa gareshi yana murmushi ya sake mayar ma ta da sakon. .
Ina miki addu'a ALLAH ya sa ayi nasara,zan fi kowa farin ciki abar sona za ta ji sautin muryata wata rana!" .
Wani dadi ya rufeta anya akwai wanda ya fi ta jin dadi dai-dai wannan lokaci. .
Haka suka kasance cikin aikawa juna sakonni da zukatansu suke ciki har sun manta matsalar da mustapha yake ciki wannan kenan. . *** *** *** *** .