← Book details Dan Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 11

Sashe 11

Dan Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kun sani tunda 'yar uwarki ce uwa daya uba daya
don girman ALLAH ki fada min gaskiya ita kanta
Hajiya marka idanunta na hawaye ta ce mustapha
muna sonka kada ka sa mu yi karya mu barwa
ALLAH ikonsa mu yi addu'a
.
ya ce gaske ne bikin weediyan za a yi ina sonta
saboda bani da asali za a bawa wani ita ta ce
mustapha ko yanzu weediyan ta ce kai take so
bikinta zai koma da kai
.
wallahi Hajiya ban san ina yi mata MAHAUKACIN
SO ba sai yanzu da ta zabi wani zan sanar da
Daddyna ina son weediyan ta ce mustapha yaro
ne kai mata biyu sunyi maka yawa bana zaton
kwakwalwarka za ta dauki hayaniyar mata biyu
ya ce zuciyata tana son su duka biyun duk sun
zama barin jikina na rantse zan rikesu cikin
amana duk wacce na rasa ta cikinsu na yi
babban rashi
.
ki tuna QUR'ANI da biyu ya fara don ALLAH
Hajiya na yi alkawarin zan rike amana ki
taimakeni zuciyata za ta fashe
.

Hajiya ta dafa kanshi cikin lallashi ta ce zan yi
magana da weediyan da Abbansu mustapha ya
kalleta ya lankwashe kai idanunsa jawur!
.

A lokacin yaro ya shigo ya ce wai Alpha yana
jiran mustapha a waje ta ce.......
.
je ka ce ya shigo yana shigowa ya kalli mustapha
ya ga yadda yake ya rikice yana bukatar lallami
da kulawa ya zauna a kasan kafet ya ce Hajiya
ina kwana ta amsa ya dafa mustapha ya ce kaine
Abokina tun kuruciya duk fadanka duk griman
kanka da ake fada mun rayu tare kuma ni
masoyine gareka
.
yanayin da ka ke ciki ya fi komai tafasa mun
zuciya Hajiya ya zan yi ina damuwa ta ce ku duk
ku yi hakuri addu'a ita ce takobin momini itace
abu na farko da ya kamata mu dage amma Alpha
bai kamata ka yi nesa da shi ba
.
hawaye Alpha ya rinka zubarwa ya ce momie ta
cuceni ta cuci kanta danta akan dan wani ta ce
kuyi shiru kun ji
.
sunyi shiru babu mai iya cewa komai a lokaci
Abban su weesal ya shigo Hajiya marka ta mike
cike da so da kulawa dama shi mutum ne mai
tattali da iya kulawa daga iyalansa ya sumbaceta
mustapha ya mike ya yi masa gaisuwa irinta
mutanen kasar TURKEY
.
ya rike hannun mustapha suka zauna yana
kallonsa ya ce,
.

"Wai ko lafiya ka ke ya kalleshi sai ya sunkuyar
da kai ya shafi kansa ya ce haba mustapha
komai ya samu bawa da sanin ALLAH kai namiji
ne namiji jarumi ne ya yi murmushi ya ce haka ne
Abba amma lamarina akwai abu mai ciwo to ya
zan yi na gode ALLAH
.

Abba ya yi murmushi ya ce yaushe za ka koma
TURKEY ne?ALIN HAUSA NOVELS DAN WAYE......... 3*17 .

LAST POST IN BOOK THREE .

NA ZARAU BABA YAKASAI .

Ya ce Abba na fi so in gama ganin karshen shari'ar nan sannan ga Daddy ba shi da lafiya domin hawan jininsa ya yi karfi kwarai ina bukatar kula da mahaifina ya ce ka yi gaskiya ALLAH ya shige mana gaba . ya ce amen ya mike shi da Alpha suka fito kowa ya shiga motarsa a kokarinsu na yin kwana ne motar su weesal ta karaso suna da yawa ko kallosu mustapha bai yi ba ya soma kokarin barin gurin ko gyara fakin ba tayi ba ta tsayar da motar weesal ta ce ke zaki kashemu ina ta je ta sha gabansa dole ya tsaya ba don ya so ba ya leko da kansa ya ce matan manya lafiya idanunta suka kawo kwalla . ta ce me ya sa za ka ki saurarena me na yi maka don ALLAH ya ce ba ki yi min komai ba ta ce to me zai sa ka ki saurarena ka tuna kai din fa wani mahadi ne a rayuwata ya dubeta da jan ido ya ce karya ki ke ba kya sona ba kya kaunata kina kyamata saboda ni din ba a san ko ni DAN WAYE ba! .

Ki je ki auri wanda ya fi ni amma ki tuna ko dan mahaukaciya ne ni asalina na ki ne tunda duk tare aka rainemu idanun weediyan ya kawo kwalla ya ce na barki lafiya ban san yadda sonki ya shigeni ba ni dama mijin Izzatu ne, . wani irin kishi ya shigeta taji kanta ya sara sai ta matsa daga inda take aguje ya shia geta sai ta durkushe tana rusa kuka. .

Ashe SO yana da zafi to ya akai ta kamu da son musty ya za ta yi da wannan abun da ke zuciyarta . wanda burine babba wanda ya jima a zuciyarta to ya za ta yi meye abinyi sai ta sake rushewa da kuka . a lokacin Hajiya marka ta shigo ta ce ke lafiyarki ta dago kanta tana kallon mahaifiyarta ta ce Hajiya ku yi min addu'a a duk kan lamarina na wahala sosai raina ya shiga rayuwata ta kasa sukuni na san SO shi ne yake damuna, .

Hajiya ta zauna kusa da ita ta tsura ma ta ido ta ce wai ke wacce irin mutum ce damuwar wani ita ce taki ya za ki dami rayuwarki baza muyi miki auren dole ba ta ce Hajiya ki taimakeni da addu'a ALLAH ya cire min kaunar mustapha Abdul zan aura shi ne ya dace da tsarina ba zan taba mai da iyayena su yi karamar magana ba . mustapha mijin Izzatu ne Hajiya ta mike ta kalli baki da tausayi kamar yadda na dauka saboda me ki ke son Abdul ga dan uwanki Hajiya ba zan iya zaman kishi ba na fi son in rayu da mijin da yake sona ba wai wanda ni nake sonsa ba da hanzari Hajiyanta ta dubeta ta ce ko zan san dalili . ta ce Hajiya da dai kin rabu da batun mustapha ba tare da ta sake kallonta ba ta fice ta bar dakin. .
Chapter 11 · 0% Book details