← Book details Dan Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 11

Sashe 5

Dan Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita ko Hajiya saratu wajen mahaifiyata ta iso ko motar ba ta gama fakin ba ta bude ta shiga gida da hanzari Hajiya lami zaune da Hajiya Marka da su weediyan ta shigo cike da tashin hankali da matsanancin kuka ta tsugunna gaban mahaifiyarta tana rusa kuka kamar yarinya gaba daya ido suka sa ma ta kafin matsanancin tausayi ya kama weediyan saboda ita mutum ce mai tsananin tausayi . mai sanya damuwar wani ta zama tata bata damu da farin cikinta akan na wani da ace wani yana kuka ita tana dariya gwanda ita ta faranta maka ita zuciyarta tayi bakin ciki, Ubangiji haka ya yi ta tun mahaifiyarta na fada har ta gaji, . tsakaninta da ita sai addu'a ta rungume Hajiya saratu ta ce momie lafiya wa ya tabaki ya zaki rinka kuka waye zai sa miki damuwa fada min don ALLAH ki yi shiru mamie ki yi magana don ALLAH fada min me ya ke faruwa da ke zan baki shawara ko in taimakeki cikin sarkewar murya ta ce ku yarda da ni na rantse ba zan kawo rudaniva cikin abinda ba dai dai ba ku dai na yi min kallon mahaukaciya na sani mubarak dana ne yau dan da na haifa ya tsaneni ya fada min mugun kalamai wadanda suka fi kama da sukan kwari da Baka kune 'yan uwana mun fito Iyali daya da ku kun ki yarda da ni to WA ZAI FUSKANCE NI? .

Tambayarku nake. .

Rayuwar saratu rayuwa ce mai cike da rudani babu mai tausayina babu wanda ya daukeni a mutum ku tuna akwai zuciya a kirjina wallahi da ace mustapha na kusa shi kadai yake sona shi kadai yake gane matsalata ya zan yi ya zan yi ku taimakeni wayyo ni Saratu weediyan kada ki damu momie NI CE ZAN FUSKANCEKI!

Kamar yadda musty yake fuskantarki ke da matsalarki, to me yasa ki ka yi fatali da mustapha bayan kina da tabbacin ya fi kowa sonki ga shi mahaifiyarki bata mai da kai akan matsalarki ba saboda me ki ka ki danki momie muna son mustapha Why za ki sanyashi a damuwa yanzu kin san a halin da yake ciki tayi shiru ta ce ban sani ba . shima mustapha ya tsaneni ta ce ba tsanarki ya yi ba ke ki ka ki wulakantashi a idon duniya ki ka ce ba danki bane saboda me ki ka yi masa haka gashi wanda ki ka daura soyayyarsa ba zai soki ba ba zai ji tausayinki ba ba zai ji kanki ba ba zai weediyan saboda dana ne kaddara ta rabamu kuma kaddara ta hadamu a matsayinmu na Iyali daya ku taimakeni don ALLAH ku kwatar mini dana. .

Cikin fushi Hajiya Lami ta ce ba ki isa ba mustapha shi ne namu ba zamu goyi bayan zalunci ba ba in dai bakin ciki da bacin rai ne to yanzu ki ka soma tozali da shi haka kawai kin shiga rayuwarmu kin ga ni kin isheni ki hada yanaki yanaki ki tafi gidanki Hajiya Marka ta ce Hajiya ki yi hakuri ina tsoron kada damuwa tasa ta zautu ai shari'a ta fi gaban wasa saratu ki yi hakuri ki tausasa zuciyarki idan mubarak danki ne to mustapha DAN WAYE? . ki bamu amsa a ina ki ka daukoshi a ina ki ka bar naki? .

Tayi shiru kamar mai tunani ta ce SANIN GAIBU sai ALLAH duk suka kalleta weesal ta ce momie kin yarda da ALLAH kin yarda da kaddara ta gyada kai to ki yi hakuri ki zuba ido mu ga yadda ALLAH zai yi damu ta ce shi ke nan ta kalli weediyan ta ce da gaske ke ki ka shigewa su mubarak ta gyada kai . tace na sani ba su da karfi momie ba ki tsoron ALLAH ya jarabceki da hakkinsu cikin fishi Hajiya Lami ta ce mustapha ne tun yana yaro ki ka kasance azzalumar Uwa a gareshi bai ji dumin Uwa kamar yadda sauran yara suke ji ba amma duk da haka komai nasa momie sai ta sanya kuka ta ce ban taba son jika kamar mustapha ba ko waye shi ina sonsa zan cigaba da kula da shi .

Hajiya weediyan ta fada ta ce momie 'yarki ce kada ki yi fishi da ita akan batun da babu wanda yasan dai dai sai ALLAH ki yi hakuri kin ji ni yanzu zan saka maganar mizanin hankali zan tsananta bincike saboda haka mu yi wa momie addu'a don ita ta cancanta ayi ma ta.A NOVELS DAN WAYE....... 3*7 .

NA ZARAU BABA YAKASAI . .

Alpha ya kalli mustapha ya ce aminina ya ce ka zo mu je majalisa ba zam fita ba domin na zama abin zunde a gari kowa kowa so yake ya san ni din DAN WAYE? .

Alpha ya yi kalar damuwa ya ce yau zan nuna maka hali da damuwar da zuciyata take ciki ina ma wani na ganin zuciyar wani lallai da ka ga yadda zuciyata ta cika da tsananin tausayinka a matsayinka na dan Adam ka yi hakuri ita kalmar hakuri ana bawa mutum ita ne a lokacun da abu ta sha kansa,ina so ka yarda da duk tsarin da ALLAH ya hukunta a kanka, . wani a Bola ake tsintarsa kuma ya yi rayuwa haka ne Alpha tashi mu je amma kafinmu je ina son ganin mahaifiyar mubarak saboda me ka ke son ka rinka dawowa da kanka damuwa ya yi murmushi tare da tsare gida mu je kawai. . *** *** *** *** *** .

Alpha ke tukin motar mustapha yana kallon Gari kowa yana harkan gabansa baya tare da damuwa, sun yi parking gurin mashin din mubarak, ganin mashin din nasa ne ya sa suka san yana cikin Gidan. .

Kamar an sashi ya fito,haka ya fito daga cikin Gidan hannunsa rike da Hula yana murzata zai sanya baki bude ya kura musu ido zuciyars na matsanancin bugu sai da hular ta fada jikinsa ya kama rawa lokaci kankani hawaye ya wanke fuskarsa yana kuka ne saboda ramar da mustapha ya yi lallai na zamarwa mustapha kadan garan bakin Tulu! .

Alpha ya fito ya dafa kafadunsa ya ce mubarak ya ya dai ya dago idanunsa ya ce mustapha ka yi hakuri na rantse ina cikin damuwa na tsani kai na na tsani wacce ta sani a cikin wannan halin kada ka zargeni murmushi kawai ya yi zamu iya shiga gidanku mu je sun tarar komai na gidan ana jibgesu gefe suna shigowa Mah ta kalli mustapha ta ce, "A'a yaushe ka dawo koda yake dama ina tunanin zuwanka saboda gobe shiga kotu ko?" Ya ce, "Mah barka da gida ya na ganki kina aiki ta ce mustapha zamu koma kauye dama ina son mu hadu mu nemi yafiyarku ya ce mene kuka yi min, ni babu abinda kuka yi min kuma babu inda za ki Daddy shi ne mai kudi ba momie ba kuma Daddyna ba shi da burin matsanta muku don girman ALLAH kada ku je ko ina ta ce kayya ka yi hakuri sam raina da zuciyata ta fita daga birni gwanda in koma can kauyenmu in yi rayuwata cikin salama .

Mah kin ce kina son ganina shi ya sa na zo in ji lafiya? .

Ta ce dama ina son magana da kai ne akan dana mubarak kada ka daukeni mai son zuciya ko mai son kanta hakika mistapha babu abin da zamu ce maka kasomu baka kyamacemu ba na fi kowa bakin cikin halin da muka shiga don ALLAH kada ka dauki mubarak a makiyinka duk da na san mahaifiyarka ita ce ta janyo komai da ni da mijina da dana za mu bar maraya zamu koma karkara kada ka zargemu muna sonka ban taba tsanarka ba tausayinka shi ne a zuciyata . don mubarak dana na ne to kai din DAN WAYE, shi ne abinda ya dameni, tabbas kai ba dan Hajiya Saratu bane domin an san Uwa da kaunar danta da tausayinsa to shin me yasa ita bata da wannan abu kuka sosai take ta shafi fuskar mustapha ta ce ina ma ni me arziki ce ina ma zan iya cigaba da dawainiya da kai da mubarak dan hada in rikeku ita ta rasa duk wanda ya haifi da kamarka kyakkyawa mai ilimi da mai tausayi mai hankali da hangen nesa burin dukkan Uwa danta ya samu ilimi da tarbiyya akan me za ta ce kai ba danta bane . na san mubarak dana ne da na haifa amma ka fi shi komai ba wani abu yafika ba balle ace . . shi ta hango ka yi hakuri hawaye mustapha da mubarak da Alpha sake ita kanta Mah kuka take ta ce ina sonka mustapha zan rikeka kamar ni na haifeka bana son kukanka don ALLAH ku daina kuka mubarak ya ce ya zan daina kuka uwata abar soyiwa a gareni tana zubda hawaye a dalilin abotata na janyo miki kuka mustapha na yi da na sanin samunka da na yi a matsayin aboki har abada zan rayu ni daya ban ji dadin Abota ba ku zo ku fita ko na daina ganin kukan mahaifiyata". .
Chapter 5 · 0% Book details