Sashe 1
Dan Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
NDALIN HAUSA NOVELS DAN WAYE........ 3*1 . .
ZARAU BABA YAKASAI . .
ALH.ABDULMAJID yarinka kallon hajiya HAJIYA SARATU yana mamakin halinta shikanshi baya tababa lallai mahaukaciyace, . mamakinshi agareshi bai wuce tsawon shekarar da sukayi ba tana fama da wannan matsalar bai sani ba sai yanzu da abin abun ya bunkasa sannan ya sani. . ya girgiza kai yanajin kaunar MUSTAPHA da tausayinsa a zuciyarsa,anya yadace ya kyale haj.saratu ta cigaba da irin wautartarta ko ko ya zanyi da ita? . kamar tasan tunaninta da yake ta ce mijina nasan kana tunani a kaina ka ji tausayina ka tuna zaman da nayi da cikin dana ajikina na haihu na rasa farin cikina tabbas MUBARAK dana ne wanda nake kaunar gani wanda nake so,alhaji ka zauna kaji kalamai na ka fuskanceni ka gane irin radadin da nake fama da shi rashin dan da nakeso nake kauna ka tuna dadin da zanji lokacin da na ganshi ina ganin dukda kallon da kake a matsayin mai tabin kwakwalwa lallai akwai yiwuwar shari'a sabanin hankali ce. .
Alhaji bani da burin da ya wuce in rayu a karkashinka inyi maka biyayya da duk macen kwarai za ta yiwa mijinta saboda haka ka taimaka mun mu gano shi mubarak jininmu ne ko ya ya shima mustapha dana ne tun da tarbiyata da ita ya rayu kayi tumani ka da ka watsar da ni mijina na sani na saba maka to nafi kowa bakin cikin haka don babban burina in shiga aljanna ga gadona ga naka,kai in zai yiwu mu rayi a gado daya ta soma shisshikar kuka da kowa kowa ya kalleni ni kaina ina kin kaina da zama ba mustapha,mutum ne shi sai dai na kasa gano shi din DAN WAYE? . *** *** *** .
MUSTAPHA yana zaune a kayataccen falon ahmad ya shigo sanye da kayan gargajiyar kasar turkiya,ya zauna yana kallonsa ya yi murmushi ya ce na sake maka ne irin wannan kallon haka ya ce dole in kalleka Abokina ban taba ganin mutum mara tawakkali irinka ba kalli yadda ka rame ka yi duhu hakan yana nuna mun ba ka yi tawakkkali ba saboda ALLAH a matsayinka na mai ilmi shin me ya dace da kai?" . mustapha ya gyara zama idanunsa ya yi jawur ya cije lebensa ahmad ya kura masa ido ya ce kalli me hakan yake nufi ka yi tawakkali domin .
'ASSABARU DIYA'U', . hakuri haske ne!'' . ya ce, ka sani ahmad na yi hakuri nayi tawakkali na kuma karbi kaddara kada ka damu ahmad koda ban san ko ni waye ba kuma DAN WAYE ba,to hakika na yi farin ciki da ALLAH ya sa daddy shi ne ya rikeni ya sadani da abu biyu masu muhimmanci sune TARBIYYA da ILIMI su ne abubuwa da za ka bawa 'ya'ya su ji dadin rayuwa wani hawaye suka surnano fuskarsa hakan yasa kirjin ahmad ya buga da karfi ya sauko kan kujera ya tsungunna a gabansa ya rike masa hannu shima ya yi kalar tausayi ya ce mustapha ina jinka a cikin zuciyata inajin damuwarka na sani walwalarka da jin dadinka duk sun ragu abokina na shiga damuwa mai yawa,haka nima na kasance,saboda ALLAH ya ka ke so in yi hawayen kan fuskar mustapha ya cigaba da tsiyaya ahmad ya ce ka yi kuka ba zan hanaka kuka ba, domin yinsa yana rage radadin da zuciya take fama da shi sai dai kai namiji ne bai kamata ace ka yi kuks ba ya ce,Oh! kana nufin ka ce min namiji baya kuka saboda shi baya da zuciya ko? . ya ce ba nufina ke nan ba a sanina Namiji an sanshi da juriya akan duk abinda ya sameshi, ahmad waye ni ni din DAN WAYE? . su waye zuri'ata su wa za su zama dangina sai dai nayi wa ALLAH godiya idan na kalli wasu jama'ar wasu na rayuwa cikin maraici ga dangin ga komai amma sun rasa gata wasu ko 'ya"yan mahaukata ne wasu Gidan marayu suke rayuwa wasu karuwai ne za su haifesu su yar da su wasu ko hatsari za a yi iyayensu su rasu,to ni din .
DAN WAYE, .
Abokina ka yi tawakkali kai DAN MOMIE ne da daddy,kai da kanka kana tababa akan hankalin momie ina so ka yi hakuri ka rungumi kaddara ka cigaba da rayuwa mai kyau ka ji Abokina ya gyada kai yana faman ajiyar zuciya.ANDALIN HAUSA NOVELS DAN WAYE...... 3*2 .
NA ZARAU BABA YAKASAI . . *** *** *** *** .
Weediyan zaune gefenta weesal,weediyan hankalinta na kan (screen) din Laptop dinta hoton mustapha ne ya yi bala'in kyau gabanta yafadi ta rintse ido tana tuno wasu al'amura da suka shige ta bude idonta ta sake kallon hoton gabanta ya fadi zuciyarta ta harba da karfi lokacin da tayi tozali da hoton yana yi ma ta murmushi kallon da hoton yake ma ta ita kanta ba ta san yadda za ta fassarashi ba bakinta ya furta ina sonka musty sai dai ba zan aureka ba weesal ta bita da kallo amma babu wanda ya iya tankawa dan uwansa weesal ta mike cike da mamakin halayyar 'yar uwart tana ba ta mamaki da ta ajibi tabbas ta san 'yar uwarta na da kirki shin wai me ta dauki kanta ne shin sai kana auran mai kudi za ka taimaki al'umma . . wai me yasa ta fi damuwa da damuwar wani akanta, ita ko weediyan zuciyarta ta yi kunci tunaninta me yakamata tayi wanda zai kawo karshan shari'ar mah dan tana tausayin mah kwarai da gaske bata son a kwace ma ta danta wanda take alfahari da shi haka tana jin tsanar momie don ta wulakanta jininta akan soki burutsun ta shin za ta iya yafewa momie ta wulakanta mustinta anya ta kyale momie, . a lokacin haj marka ta shigo weesal ta tareta ya yin da weediyan ta ce wai ina ki ka je ne hajiya ta ce kai duniya na bani tsoro shi yasa lamarin zaman duniya yake tsoratani in baka rungumi dan uwanka ba to wa za ka runguma,shi yasa kullum nake fada muku ku yi ZUMUNCI ku hade kanku ki duba ki ga yadda lamarin hajiya hadiza ya ke daure man kai weediyan ta ce wai har yanzu bai fito ba ta kada kafada tace hajiya kada ki damu kanki akan abinda babu ruwanki ta ce ai abinda ya damu amininka ya dameka . ke yanzu ba ga shi nan ba kin yi shisshigi abinda ba ruwanki kin yi tsamo tsamo banda muna da kyakkyawan zumunci ai sai ki hadani da 'yar uwata ta ce hajiya ke kanki kin san 'yar uwarki ba ta da gaskiya ta ce to na ji zancen ya isheni haka ke yanzu wane irin taimakon da za ki iya yiwa hajiya Hadiza ta ce su masu kudi ne ni ko taimakona akan talaka ne ko. . *** *** *** *** .
Mah tana zaune tana diba littafin Ahlari da yake da yammaci ne a lokacin mubarak ya shigo ta ce ina ka je ne ya ce naje wani waje ne kin san weediyan ta sama min aiki fatana kawai ki yi min addu'a ta ce gaskiya ban ji dadin barin aikinka da ka yi ba . ai ita gaskiya daya ce babu abinda za mu cewa mustapha domin ina tausayinsa zuciyata tajima tana mamakin halin mahaifiyarsa wai shin masu kudi me suka dauki kansu in giyar kudin ta motsa sai su yi komai kansu tsaye shi kansa mijin nata ya rasa yadda zai yi ne amma in ba haka ba yaushe mace zata iya fita har tayi abu babu yardar mijinta? . mah ki daina duk ire-iren wadannan tunani kin san komai MUKADDARI ne ki yi addu'a ALLAH ya sa mu fi karfin zaluncin azzalumai, . ki dage da addu'a kawai ta gyada kai tace insha ALLAHU zan dage iya yina, ALLAH ya shige mana gaba yace amin. . *** *** *** *** .
IZZATU zaune ta jingina jikin bishiya a harabar Gidansu a zaune take kan wata lallausar darduma kaninta khaleed na gefe yana karatu ya juyo yana fadin Ya Izzatu wai izunki nawa ta ce da kafin inzama kurma Ina izu goma sha uku ya ce yanzu fa ta ce wani ne yake koya min shima kurma ne a zuciyarsa ya ce to ya ake karatun kurame oho . ta ce azatonka mu bamu karatun AL-QUR'ANI ko a tunaninka bamu da cikakkiyar sallah ne'' .
''A'a''.ya fada.
Ya ce, ''ALLAH shi ya san karatun Bebe"Inji Hausawa". .
Duk da ba ta ji me ya ce ba cikin fishi ta ce wai me ya sa masu kunne ku ka fiye GULMA ne in ba ma jinku ALLAH Yana kallonku yana kuma jinku a lokacin suhaila ta karaso tinkis!tinkis!! ta ce a'a lafiya khaleed yana murmushi ta ce babbar 'ya to bizarku ta samu yanzu muka yi waya da abbanki yake sanar mun dukkaninsu cikin farin ciki suka rinka dariya ta janyo Laptop dinta ta bude suhaila ta bude screen din laptop din ta ga hoton Izzar da mustapha sun dace da juna hoton randa ya je kaltungo suka yi hoton gwanin sha 'awa . suhaila ta janyo Laptop din gabanta ta shiga don duba hotuna , gabanta ya bada ras lokacin ta ci karo da hoton BAREK dinta ya dada kyau da wayo wani iri ta rinka ji a zuciyarta ta rasa yadda za ta fidda soyayyarshi a zuciyarta dan kuwa ita ta hakura da shi ta zo tashi izzatu ta ce mata ga hoton wacce zai aura komai ya kwance mata ai twnice ne to wacce a ranta ta ce sai dai weesal don weediyan ita MATAR MANYA ce! .