← Book details Cizon Yatsa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 11

Sashe 2

Cizon Yatsa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ta ina zan nutsu?

Ka san me Alh.

Audi ya ce min kuwa yanzu?"
Haj.

Manga ce ta kar
e wayar don shi ma speaker ya saka.

"Tauhida kin san school
ina?"
"Nanna?" Ta ce cike da mamaki.

"Kin san makarantar?"
"Eh"
"To ki same mu a gidan da yake jikinta daga hannun dama.

Zan sanar da maigadin idan kin rigamu zuwa ya bu
e miki."
Kashe wayar ta yi ta dubi Shaheed da Sariat"
"Ku ha
a abinda zaku iya na kayanku ka
auko yaran daga makaranta yanzu mu tafi.

Alh.

Audi ba zai ha
ura ba tunda ya kawo zancen auren nan sai ya binciko gaskiyar lamari game da aurenta.

A wannan binciken kuma za a iya ganin Aidan."
Sariat ta kalli yadda ya ji
e da gumi da hawaye, "Tunda aka fara wayar
azu da yaji muryar Alhajin yake kuka."
"Na riga na san cewa case
innan yafi yadda muke tunaninsa.

Yanzu dai Shaheed ina da alfarmar da zan ro
a nima a gareka."
Juyowa ya yi don jin me za ta ce sai ta nuna masa hoton wani kyakkyawan matashi wanda kana ganin kayan jikinsa za ka gane cewa likita ne.
ana na fari kenan Ar
am wanda na baka labarin dalilin
atansa.

Abinda ban fa
a maka ba shi ne sun so juna shi da Tauhidat sosai amma aurenta na bazata da Shamsu ya shiga tsakaninsu."
"Amma bata ta
a yi min zancensa ba."
"Abubuwa da yawa sun faru da baka sani ba Shaheed.

Kaine uba ga Tauhidat a yanzu saboda haka za
i yana gareka.

Wa za ka bawa aurenta tsakanin Ar
am Ibrahim Karam da Shamsuddeen Audi Karam?"
ar bakinsa zai bata amsa sai sai jin wayarsa ya yi ta
auki
ara ba zato ba tsammani.

A take
ar guntuwar nutsuwar da da ta rage masa ta kama gabanta.

Yana karata a kunnensa kuwa ta yi masa wani nauyi na musamman a hannu saboda amon muryar Alh.

Audi da ya ji.

A take jikinsa ya
auki rawa, har sai da wayar ta fa
i a
asa ta tarwatse.

Cikin tsoro yake fa
awa Haj.

Manga waye ya kira a lokacin da yake ha
a wayar cikin sauri tana
ara watsewa.

Kar
a ta yi ta ha
a masa ta kunna.

Ya mi
o hannu zai kar
a ta tsare shi da idanuwanta masu tarin kwarjini da haiba.

"Ka nutsu kai ba yaro bane.

Idan kayi abinda zai sa ya zargi wani abu mu duka ne zamu ji a jikinmu.

Na tabbata da Tauhidat ce ba zata yi haka ba saboda rainona ce."
"Gori ki ke yi min?" Ya tambayeta a
arinsa na sako wasa domin ya saita kansa.

Wayar ce ta sake shigowa, ya sake
auka yana bashi ha
uri da cewa fa
uwa ta yi.
orafi Alh.

Audi ya fara yi masa na rashin zuwansa jajanta masa halin da gidansa yake ciki.

Cike da dakiya don ya burge Haj.

Manga, Shaheed ya ce, "jiya na dawo garin nayi tafiya ne tare da mai
akina.

Mahaifiyarta ce ba lafiya tun a can naji labari.

Gani nayi abin yafi karfin waya shi yasa ban kira ba nace sai dai na zo.

Yanzu ma dawowata kenan daga office ko zama banyi ba na zo
aukar matata zamu taho."
Kai Haj.

Manga ta girgiza kawai.

Irin wannan dogon sharhi babu ko jan numfashi da yake yi ba shi ne nutsuwar da take so daga gareshi ba.

"Bana gida amma zaku sami Fanna.

Yanzu muka rabu da Tauhida tazo duba Shamsu tana ta kuka."
Kalmar zagin da ta kusa su
uce masa da yarbanci ya yi saurin da
ilewa, sannan ya nuna nasa alhinin na abinda ya sami Shamsun.

Alh.

Audi ya nuna jinda
insa sannan ya koma mitar ya akayi ya aurar da Tauhidat bai aiko masa da kati ba.

Tun rasuwar mahaifinsa ya janye jiki daga gare shi amma ko sun ki ko sun so shi uba ne garesu.

"Ya sunansa kuma aikin me yake yi?" Ya tambaya a zuwan shi fa uba ne dole a bishi.

"Likita ne
an Kano." Ya amsa da sauri.

"Bahaushe ne kenan?

Nan da kwana biyu bayan Shamsu ya tashi zuwa asibiti kana ganin zai iya zuwa gaisheni?

Ko yaya zan so nayi wani abu a matsayin uba ga
ar marainiyar nan.

Ka bar zuwa ta'aziyyar ku zo tare."
Shaheed amsawa ya yi tare da ban ha
uri ya kuma tabbatar masa da cewa zasu zo in sha Allahu.

Fayyacewa Haj.

Manga yadda suka yi ya yi ta ce kada ya damu, amsarsa kawai take jira game da wanda ya za
awa
anwarsa.

Ya san wanda ya kamata ya za
a, amma duk da haka ya ce ta yi masa ha
uri suje gidan ya gana da ita.

Bata
i ta tasa ba ta ce su shirya nan da dare su taho.

Sai ya nuna mata baya son ya bar gidansa zasu zame mata
arin nauyi.

Da yaga ta matsa sai ya amince amma na ranar kawai.

Washegari zasu dawo gidansu shi da yaran sai Tauhidat ta zauna a can tare da Aidan.

Bayan fitarta ha
uri ya bawa Sariat akan abinda ya yi mata sannan suka fara ha
a kayansu.

Ita kuma Haj.

Manga wurin Susu ta tafi cikin sa a babu
ata lokaci aka fito da ita.

Tana son tambayarta game da yaushe ne ta san cewa Shamsu ya saki Tauhidat amma wani
an sanda ya tsaya musu a ka.

Yana cikin wadanda Alh.

Audi ya biya suna fada masa shige da ficen da ake yi a wurin Susu.

Maimakon ta fa
i abinda ya kawota sai ta hau ta da fa
an akan me za ta ha
a baki da ma
iyanta ta ce tare da Jamal suka saci ku
i.

Susu tana
arin kare kanta Haj.

Manga ta tura mata wayarta gabanta.

"Duba wannan list
in ance duka accounts
in da ki ke bu
ewa a wasu
asashen ne ko nayi
arya?

Jamal kuwa ko lokacin da ya yi karatu ban yarda ya bu
e account ba.

Duk abinda zan tura masa ta hannun yayansa yake tafiya."
Idanu Susu ta tsurawa wayar ta karanto abinda Haj.

Manga ta rubuta kamar haka.
(Tun yaushe Shamsu ya saki Tauhidat?

Ki rantse min ya taba shiga
akinta ko sharri ki ka yi musu?

Zan taimaka miki da neman Aidan idan kin fa
i gaskiya)
Tana gama karantawa ta tura mata wayar cikin zafin rai.

Sannan ta soma
aga murya itama tana masifa.

"Wallahi tun a ranar da Shamsu ya fara kaini gidan na sani."
Sai ta dan kifta idanu, "na san cewa bakya
aunata Hajiya amma kada haka ya zama dalilin da zai sa kiyi min sharri.

Abu na biyu kuma da ki ka tambaya shi ma
arya ne.

Don Allah ni dai ki taimaka min ko Aidan ne ki nemo."
'Da wayonki ashe', cewar Haj.

Manga a zuci sannan ta mi
e tsaye.

"Banyi al
awarin fitar dake daga nan ba amma zanyi bakin
arina in ga cewa gaskiya ta yi halinta."
Daga haka ta fice
an sandan na biye da ita.

Susu kuwa murmushin jinda
i ta yi saboda a iya zamansu idan da akwai abinda ta karanta dangane da ita bai wuce
iyayyarta ga mijinta da kuma kasancewarta mutum kaifi
aya.

Tunda ta ce za ta nemo mata Aidan ta yarda za ta yi.

Sai yanzu ma ta gane idan tana son ta tsira ya zama dole ta ha
a kai da ita.

Tunda aka sako Jamal a cikin lamarin za ta yi abinda ya dace domin bayyana gaskiyarsa.

Maigadin gidan ko sunanta bai tambaya ba ya bu
e mata gate cikin girmamawa.

Bayan ta yi parking ta fito ya zagayo da sauri suka gaisa sannan ya yi mata jagoranci zuwa falon gidan.

"Ki jirata a nan tana hanya.

Sai dai babu masu aiki tukunna ta ce idan kina jin yunwa ki shiga kitchen."
Godiya ta yi masa ta juya ya fita.

Sai a lokacin ta
aga kai ta
arewa tamfatsetsen falon girma.

Ba sai an fa
a ba komai na gidan sabo ne hatta fenti.

Ya yi kyau sosai amma hankalinta bai wani kwanta ba.

A iya saninta Haj.

Manga ta dena sonta tun bayan aurenta da Shamsu.

Ga kuma tsoron kowane lokaci asirinta zai iya tonuwa na
aryar aure, Alh.

Audi yaje ya
aba mata
ansa.

Yanzu ba Shamsun take gudu ba kamar yadda take tsoron mahaifinsa.

Ta yi nisa cikin tunanin abubuwan da suke faruwa a cikin
an kwanakin nan da suka sha kanta taji wani
amshi ya ziyarci hancinta.

Da sauri ta tashi daga kan kujerar ta juya baya inda take jin
amshin.

Jamal ta gani tsaye jikin wata
ofa yana ta zuba mata murmushin nan nasa.

Ya zama babban mutum ba kamar ha
uwarsu ta
arshe ba.
aure fuska ta yi tamau, don bata manta zafafan kalamansa gareta ba ranar da aka yi mata sharri.

"Nanna nake jira."
Ta ce a gimtse bayan ta koma ta zauna ta juya masa baya.

Dariya ta bashi ya zauna a kujerar da take kallon
angaren da ta zauna sai ta sake juyawa.

Sunyi haka ya kai sau biyar ta gaji ta juyo rai a
ace,
"Wai meye ne?"
Marairaicewa ya yi, "haba
anwata fushi shekara tara ke kuwa baki gaji ba?"
"Ka kalli idona a gaban mutane sun fi biyar ka ce wai ni, ni...ni" kasa
arasawa ta yi sai kuka da ya
wace mata.

Yana bata ha
uri tana cigaba da mita cikin kuka,"na zata ko gaske ne kai ne mutum na farko da zai rufa min asiri."
Bai fasa bata ha
urin ba ya ce, "Lokacin ma dole ce
anwata."
"Haka za ka ce mana.

Kuma da Nanna ta dena kulani ko ka bata ha
uri.

Dama can baka wani damu dani ba sai kawai kaima ka shareni."
"Ki tsaya kiji ba yadda ki ke zato bane."
Bata yi shiru ba ta dinga
irgo masa laifukansa
aya bayan
aya.

Idan ya fara kawo hujjar wanke kansa bata bari ya gama sai ta karanto wani.

Suna wannan diramar Nanna na bakin
ofa tana kallonsu tana murmushi.
Chapter 2 · 0% Book details