← Book details Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 20

Sashe 20

Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Dariya Ummah ta kwashe da ita kana ta Dubi Imran.
"Mai kake Jira da bazaka tafi da matarka ba ka tsaya wani ƙaton banza na baka doka da order'
Imran na Ƙoƙarin kama Amatu Ahmad ya kuma kai masa duka kana yace.
"Wannan ta haramta agare ka har abada ba matarka bace zan yi nisa da ita zan ɓatar da ita daga Duniyarku yadda daga kai har Uwar tata zakuyi rashin ta na har abada babu wanda Amatu ta dace dashi kamar Ni nina san wace ita nina raini abata nina san ciwon ta da mutuncin ta da darajarta kuma sai na tafi da amatu tafiya ta har abada Kai kuma ka jirani haɗina da kai babu alkairi ke kuma sai kinyi Kukan nadamar wannan kwaɗayin naki a lokacin da Kika buɗi idanu babu Amatuhhhhh"
Ahmad na kawai nan ya Finciki Amatu yay waje da ita bai damu da mutanan dake kallon su ba ya cillata a mota ita da Iman sannan yaja Motar da Gudun tsiya yabar Unguwar.

Duk yadda Alhaji yaso kamewa abun ya gagara Lokacin daya ji Kiran Alhaji idiris wanda ke bashi haƙuri akan fasa auren Zainab da AHMAD wanda sai da Suka bari mutane suka haɗu sannan za'a kira waya ace sun janye Alhaji ya yarfe Gumin da yake tsatstsafo mashi kawu ya Dubi Baffa Baffa ya dubi liman suka ɗan zanta Irin  na sirri kafin Masallacin yay shuru Liman ya ɗauki lasafika.

"An daka ta da tafiya Gidan su waccan amarya sai dai za'a ɗaura auren da Ƴar uwar shi kamar yadda iyayen shi suka Umarta jama'a a saurara An Ɗaura AUREN AHMAD ALI MAKAMA DA AMARYAR SHI..............wadda Alhaji Ali makama shine ya zama waliyin Amarya Malam Yusuf makama ya zama waliyin ango tare da Cikakken sadaki naira dubu Ɗari lakadan ba ajalan ba shedu ku shaida aure ya ɗauru da ikon ALLAH"
Nan da nan masallaci ya É—auki surutai wanda sam surutun ya hana jin wacece Amaryar AHMAD É—in.

Adai dai wannan Lokacin Kuma Ahmad ke sheƙa gudun Halaka da Amatu wadda take ta kuka kamar ranta zai fita.
A hankali ta É—ago ta kalle shi tausayin sa ya kamata Ita ma kuma tausayin kanta ya kamata sabida maganar da zata faÉ—a masa daidai take da wargaza dukkan kwanciyar hankalinsu.

"Yayah Imran bai sake ni ba wallahi da auren shi akai na yayah"
Da wani irin sauri ya juyo Da idanun shi masu aman wuta.
"Amatuh Kin cucen mai yasa baki gayan ba! Amatu kin cuci kanki a karo na Biyu wannan shine zai zama na ƙarshe! Macuciya azzaluma mayaudariya, Kin wa kanki Kin cuci kanki zan barki da Mijinki Yayi duk yadda yaso dake Tunda ke shasha sha ce wawiya marar tunani ya zama Dole Ki koma gidan Jiya!"

Ya faÉ—i maganar yana mai sakin kan Motar, a gigice Amatullah ta saki Iman tayi kanshi ta cakumo shi ta faÉ—a Jikinshi tana mai rungume shi sosai Cikin kuka ta Furta masa YAYA AHMAD..............
*LAST FREE PAGE*
Wannan shine ƙar shen shafin kyauta.
*Akwai tarin abubuwa agaba wanda sai wanda ya Biya kuÉ—i ne zaiji su*
*TIRƘASHI INA MAFITAR AHMAD AMATU YAYA CAKWAKIYAR TASU ZATA KASANCE NA WANNAN BAƘON LAMARI DAYA KUTSO...?*
*DA WA AKA ÆŠAURA AUREN AHMAD*?
*SHIN YAYA MAFITAR AMEERAH DA UWARTA*?
*YAYA ZAINAB ZATA TSINCI KANTA A GABA*
*WANI SAKA MAKO UMMAH ZATA GIRBA ITA DA IMRAN*?
*WAI WACE DANGANTA KAR CE A TSAKANIN AMATUH DA AHMAD ADA*?
*INA TARIHIN LABARIN WAIWAYE ADON TAFIYA*?"
*YAYA AHMAD ZAI JI IDAN YASAN AN FASA AUREN SHI DA ZAINAB AN ÆŠAURA DA WATA....?*
To bamu ji komai ba har yanzu akan wannan Labarin shin mene ma BAƘON LAMARIN? Soyayya Yaudara makirci kirsa munafurci duka suna ƙunshe Cikin wannan labari zaka more da Jin daɗi idan ka Biya domin akwai tarin abubuwan da bamu bayyana suba a free page's ba maza hanzarta Biyan naka Kafin ai babu kai/ke.
Ƙofar Biya na nan a buɗe.
*NA KAMMALA LITTAFIN BAƘON LAMARI GA MAI BUƘATAR COMPLT ƊIN SA 500 NAIRA NE KACAL. ZUWA ASUSUN BANKIN 9022260850 OPAY BANK SHAIDAR TURA KUƊIN ZUWA 09022260850*
Chapter 20 · 0% Book details