← Book details Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 20

Sashe 18

Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ranar Litinin aka kai Lefen Ahmad wanda ranar Æ´aÆ´an mama dake É—aki suka cika gidan da yaransu Sai janta suke har Aysha mai bin Ahmad nacewa tazo suje gidanta dake Hotoro ta taya ta zama mama tace Ku rabani da faÉ—an Yayanku Kullum sai ya tambayen ina ajiyar sa babu ruwana.

Sai lokacin tasan ashe yana tambayarta tsabar miskilanci ne ya hana ya na cewa a bata wayar.

Su baffa sun kai lefe lafiya an saka ranar Biki asabar mai zuwa wadda itace ranar ɗaurin aure sun dawo da shatara ta arziƙin tukwici.
Sashin mama har dare dangi na shigowa wanda daga ciki harda Anty wadda rabon da ta shigo wajan mama tun ranar da Amatullah ta dawo koda tazo Ɗinma a tsaye tai wa mama Fatan alheri ta juya mama bata kawo komai aranta ba tunda kowa uzirin gabanshi ya ishe shi haka ta cigaba da amsar Baƙi ƴan taya Murnar tasowar auren Yaya Ahmad.

Washe gari da sassafe Anty ta nufi Sashin Ummah cikin Kirsa da Munafurci a É—age Ummah ta watsa mata kallon banza dama Umma cike take da kowa agidan.
"Hadiza dama nazo Miki da magana ne akan yarinyar ki yanzu Kina ji kina kallo Binta ta É—auke miki ita tana can tana mata bauta Ke ko oho? wato yanzu Dai Binta so take ta mamaye gidan nan ta juya kowa"
Ummah ta É—agawa anty hannu.
"Ke Lami dakata bana son munafurci ba bakin ku É—aya da Bintar ba shine zaki zagayo nan kina gayan maganar banza ko kin zata ban san kowa ce bace Ke wuce ki bani gu kona Tona miki asiri"
Zage zagen Borin kunya anty tahau yi kafin ta kama hanya ta fita burinta bai cika ba dan taso ta haÉ—a gagarumar Masifa ne a tsakanin Ummah da Mamah.
Ita kuwa Ummah abin da yasa batai wa Anty wata maganar arziƙi ba sabida sun gama magana da Imran Ne wanda ta shawo kansa da ƙyar Yace mata ranar Juma'a zai shigo kano asabar Idan ya huta zai Shigo wajan safiya ya ɗauki matar shi wannan tasa ta zubawa su Mama ido bata wani ɗaga hankalinta ba dama tashin hankalinta Akan Imran ne to kuma ya dawo dan bada ban kayan abincin da Ahmad ya kawo mata ba da Tuni ta shiga tasku.

Ko wani ɓangare shirin Biki ake Sosai domin tuni dangin mama na nesa dana kusa da dangin su Alhaji sun soma cika gidan.
Haka zalika daga Ɓangaren Amarya zainab suma shirinsu har yafi  nasu mama.
Daga ɓangaren Anty ma Kullum sai ta fita sun ɗauki hanyar Ɓata ita da Yayah wanda Har ta rame sabida jarabar rashin Hutu.
Sun sami nasarar zuwa wajan wani Boka wanda ya basu tabbacin duk wani aiki da zasu yi akan Ahmad basu da nasara sai dai akan Ita amaryar tashi wadda zasu haÉ—ata da Jinnun da zai hau kanta ta Tubure tace ta fasa auren Ahmad ÆŠin da wannan Murnar su anty suka dawo Gida suna Zuba idanun ganin yadda auren Ahmad zai Juye ya koma kan Ameerah.
 
Abin mamaki itama Ameerah tun da Amatullah ta koma sashin mama shikenan ta daina zuwa dan rabonta da Ameerah harta manta.

Yau ta kama Alhamis wanda su Amatullah suka je Kitso daga nan suka wuce Gidan Ƙunshi ita da Naja da Surayyah tun safe mama take kiran layin naja bata samu ba har akai magariba Lokacin ne suka shigo Gida sai dai Sun bar Amatu acan Tace zata tawo komai dare dan bata cin lalle da wuri mama tai faɗan barin tan da sukai har ta Ce sai sun koma sun tawo da ita.

Saukar Ahmad kenan agidan Yayi shiri Cikin Royal Blue Boyal mai yankan sugari ya ɗora Hula kalar Ɗinkin Jikinsa yayi masifar Kyau sai baza ƙamshi yake Zeje Gidansu Zainab ne shida wasu Abokan shi wanda zasu ɗauki amarya su wuce wajan Kamun da ake yau wanda Zainab ɗin ta adda ba masa da waya akan dan Allah yazo badan yaso ba ya sauka ayau wanda ko mama bata sani ba sai da ya shigo yanzun.

Ya duba agogon hannun shi.

"Mama sai mun dawo akwai abokai na dake Jirana a waje"
Mama tai masa fatan alheri har yakai Bakin Ƙofar fita ya dawo kamar yayi mantuwa.
"Ina Amatu?"
Kamar mama na jira ta hau gaya masa ai su naja sun baro ta gidan lalle.
"What lallen me kuma? dan basu da hankali zasu bar ta da yarinya a wani waje"
Ya shiga Kiran surayya wadda tana zuwa yahau yi mata faÉ—a kamar zai daketa Sannan yace ta bashi numbern mai lallen.
Jiki na rawa ta karanto masa ko mama baiwa magana ba ya fita wajan motar shi ya shiga yabar Layin da wani irin gudu batare daya bi takan abokan shi dake tsaye zaman Jiran shi ba.

Yana tafe yana kiran Numbern mai lallen wadda tai masa kwatance nan Rafin ɗan nana ne Haka ya dinga bin kwatancen har ya Samu ya ƙarasa ƙofar Gidan.
"Ki ce ma Amatu ta fito ko ba a gama lallan ba"
Daga haka ya katse kiran.

Mai lallan ta dubi Amatullah tana  mai sakin dariya.
"Au ashe baban iman keta min waya tun ɗazu to yana ƙofar Gida"
Da yake suna ta hira ne da Amatullah harta gaya mata sunan Iman É—in.
Duk wayar da Ahmad kewa mai lallan ta É—auka ko matarsa zai kawo dan suna haka da mutane sai da yazo yace mata ta kira masa Amatu.

Jikin Amatullah yay sanyi ko kamawa na ƙafar bai yi ba ta cire ta Goya Iman ta fita waje tana raba idanun waye yazo ɗaukarta ita dai tasan IMRAN bai san tazo lalle ba to ko mama ce ta turo yaya kamal ya ɗauketa.

Da haka ta ƙarasa Ƙofar gidan ta tsaya tana waigen inda zata hangi wanda yazo ɗaukar nata..............*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*
*Ina masu kananan nono?*
*Ina masu yaye?*
*Ina yammata da ake shirin aure?*
*Ina matan gida masuson gyara?*
*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*
*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*
*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*

BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679
IG Bintus-spa-nd-more..
*BAƘON LAMARI...!*🌹
     { Eternal love }

           *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *17*

Tun da ta fito ya zuba mata idanu ta cikin motar yana kallonta Goyon yayi mata kyau sai dai ba zaka ce nata bane zaka É—auka Æ´ar wani ta goya.
Gajiya yayi dan kanshi ya haska saitin ta da fitilar Motar yana mai danna mata Horn mai ƙarfi.
Idanunta ya haske mata dan haka ta sanya hannu tana karewa Harta ƙaraso gaban motar Gabanta ya faɗi Lokacin datai idanu Huɗu da Ahmad acikin motar Ba ƙaramin kyau yayi mata ba.
Da ƙyar ta kame kanta tana Kiran sunan Allah acikin zuciyarta haka ta Buɗe Ƙofar motar ta shiga ta zauna bakinta ɗauke da sallama.

Amaimakon yayi mata magana sai ma Zira hannun shi dayayi ya Kunce Goyon Iman ya É—orata saman Cinyar shi yana mai satar Kallon lallan dayay mata jaa sosai a hannunta.

Haka ya tashi Motar batare daya Ce mata ƙala ba.
Itama batai masa magana ba taja bakinta tai shuru wani Fitsarin tsoro ne ya kamata Lokacin data ga  ya karya kwanar Shiga jambulo third gate bata gama Tantance komai ba har saida tagan shi yana zuba Horn a bakin gidan da sukai ta zarya da Sabuwa mai kai ƴan aiki Ta cika da mamakin yadda taga masu gadi na rawar Jiki wajan Buɗe masa Gate Ɗin gidan zare Idanu tai tana tasbihi ga Allah lallai Wannan gida ya tsaru kamar ba'a wannan ƙasa tamu ba.
Chapter 18 · 0% Book details