← Book details Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 20

Sashe 2

Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga waje duk sallamar da Ameerah ƴar ƙanin mahaifinta ke yi Amatullahi bata jita ba da matiƙar mamaki Ameerah ta zauna a saman kujera tana tunanin ko Wanka Amatullahi ke yi ganin shurun tayi yawa yasa Ameerah tashi ta nufi hanyar Ɗakin Amatullahi sai da ta jima riƙe da handle ɗin ƙofa a hannunta ta kasa murɗawa ta shiga sabida gudun kada taje Ko Mijin Amatullahi na gidan, Sai dai rashin ganin motar shi da bata yiba yasa tai shahadar tura ƙofar.

Idanunta yayi mata tozali da Amatullah kwance kamar gawa a saman gado, da sauri Ameerah ta ƙarasa Gaban gadon tana kiran sunanta.
"Amatullah! Amatullah!!"
Jin shurun tayi yawa yasa Ameerah hawa gadon ta kamo Amatullah jikinta ta zaunar da ita a saman cinyarta tana mai saka hannu tana share mata hawayenta.

"Subuhanallahi! Amatullah Lafiya meke damun ki naga jini a goshin ki?"
Ameerah ta faÉ—a cikin damuwa.

Tashi Amatullahi tai tare da nufar Hanyar falo gudun kada Imran ya shigo yagan su a É—akin Baccinsu yayi cin mutuncin sa daya saba.

Ganin haka yasa Ameerah ta miƙe tabi bayanta.

Zama sukai a falo duk A tsorace Amatullahi take, Amman hakan bai hana ta sakar ma Ameerah fuskarta sosai ba cikin jin daÉ—in ganin Ameeran Amatullahi tace mata.

"Ameerah daga gida kike kenan Yasu Ummammu dasu Anty?"
Ameerah ta tuɓe gyalanta tare da cewa.
"A,a daga makaranta nake, nace bara na biyo ta nan naji yaya Kukai Da Yayah Ahmad É—in? kin kira shin kuwa?"
Jin sunan wanda Ameerah ta ambata yasa Amatullahi ta haɗe fuska tana ƙara jin takaici da baƙin cikin abin da yayi mata a ɗazu wanda a zuciyarta tai dana sani yafi cikin kwando na biyewa shawarar Ameerah data yi harta kira shi.

"Naji kin yi shuru? koba ki same shi ba?"
A zafafe Amatullahi ta kalli Ameerah tare da ce mata.

"Dallah malama rufe min baki daman wannan mai zuciyar mutanan farkon kina zaton zai dube ni, ne da fuskar tausayawa Wallahi Inda ban san Yaya Ahmad ba da sai nace Ba a jininmu yake ba riƙon sa yayi yawa bakiji yadda ya gasan magana ba, wai kada na kuma kiranshi ni matar aure ce bai ma bari yaji mai ke tafe dani ba ya kashe wayar shi"

Tana kaiwa nan ta sakawa Ameera kuka wiwi tana cewa.

"Shikenan yanzu ameerah kowa ya zuba min ido kamar bani da kowa hatta ga mahaifiyata data fi kowa kusanci dani amman ta kasa fahimtar halin da nake ciki acikin gidannan?"

Ameerah ta gyara zamanta sosai tana cewa Amatullahi.

"Maganar gaskiya duk wanda zai ganki cikin wannan daular babu mai kawowa kina cikin wata matsala, Ni kaina iya sanina kawai nasan Imran ɗan tijara ne amman zama da irin su yana da daɗi, Amatullahi ki haƙura duk da nasan Imran zaɓin Ummanki ne ba zaɓin ki ba dan Allah ki kwantar da hankalin ki kodan hidimar da yake da mahaifinki wallahi jiyannan ya ƙara Biyan wasu kuɗin da za'a ƙara duba Ƙafafun baba wanda nasan ita kanta Ummah hakan dataga yana musu ne yasa bata baki fuskar Zuwar mata da ƙarar Imran"

Wata wawiyar faɗuwar gaba Amatullahi taji yaya zata yi da kowa yaƙi fahimtar me take ciki burin su kawai daular da take ciki da kuma Kuɗin da Imran kewa mahaifanta ɓarin su.

Ita kaɗai tasan halin da take ciki ta fito fili tacewa Ameerah Imran na son nemanta ta baya ta daɓawa kanta wuƙa a ciki ta tonawa kanta asiri? Duk tsiya Imran Mijinta ne bazata so wani yaji halin da take ciki akan shiba Iyayenta kaɗai zata gayawa Wanda Ummanta idanunta ya rufe akan Imran bata saurara mata ita gani take kamar auranne bata so, Shi kuma mahaifinta ba lafiyar ƙafa ba Kullum sai an kwantar an tayar dashi Yayan mahaifinta da ƙannen shi da suke Gida ɗaya Ummanta tace musu Ƴan baƙin ciki wannan tasa suka tattara suka zuba musu idanu.

Ahmad datai tunanin zai taimaketa Shima ya bula mata tsakuwa a ido sam yaƙi Sauraranta, Tana gudun ta gayawa Ameerah duk da tasan Ameerah masoyiyarta ce ta haƙiƙa tare suka taso komai nasu tare yake amman Mahaifiyar Ameerah bata ƙaunarta ko kaɗan wanda Gudun ta ɗaya kada ta gayawa Ameerah halin da take ciki ita kuma ta kwashe ta gayawa mahaifiyarta magana ta watsu acikin gidansu wanda ya kasance Gidan yawa mai cike da faccalanci da Ƙyashi da baƙin ciki shi yasanya ko kaɗan bata yarda Ameerah tasan halin da take ciki ba idan ka cire Tijara da wahalarwa da Imran ke mata wannan sune kaɗai tabar ameeran ta sani.

Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannunta.

Ta share hawayenta daya ƙi tsayawa.

A hankali tace.

"Shikenan Ameerah Allah ya bani dangana acikin halin dana tsinci kaina"
Ta faÉ—i kamar zata yi kuka.

Ameerah ta miƙe taje kicin ta ɗebo ruwa tare da ɗan tawul tazo tana Gogewa Amatullah Jinin daya ɓata mata goshinta tana bata baki Cikin maganganu masu kwantar da hankali.

"Amatullahi Ki ƙara haƙuri, Zaman gida idan ya wuce ka ya wuce ka ko wace mace da kika gani acikin gidan Mijinta haƙuri take wadda tace tana samu komai yadda take so ƙarya take"

Amatullahi a zuciyarta tace Ameera baki san dawar garin ba, Amman a fili sai ta Jinjina mata kai alamun gamsuwa sannan Ameerah ta ƙara da cewa.

"Kina kallon Gidanmu kowa kanshi fa ya sani, wallahi Matan kawu wani bin basa girki yanzu, Sabida Babu dan baƙin Hali da Kirsa Irin ta Maman su Yaya Ahmad duk irin aiken da yake musu yace a rabawa ƴan gida bata badawa hanawa take, Shiko Alhaji Babba kinsan bai da magana Haƙuri gare shi sai yayi mata shuru, haka zatai ta facaka da Kuɗi da abinci, Hatta Antynmu da suke aminta bafa ta bata ko kwabo, Ita kwa daman Ummanki Imran dik wata yana mata aike shiyasa bata da matsalar Komai amman mukam muna shan gadara wajan Maman su Yaya Ahmad musamman Yanzu da Naji labarin Auren shi da Yarinyar Uban gidan shi tana ta ƙaratowa Mama ana ta ɗaga kai za'ai suruka ƴar masu kuɗi"

Zare idanu Amatullahi tayi tare da cewa.
"Aure kuma? to kefa Ameerah ya fasa auran naki, Amman kwa da Maman shi bata kyauta Muku ba"

Ameera tayi dariya mai ciwo tare da cewa.

"Amatullah Ina masifar son yaya amman maman shi tai ma anty alƙawarin cewa daya auri waccan nice ta Biyu"
Ta faɗa tana mai yaƙini da maganar tata.

Amatullah tace.
"Yawwa har naji batu"
Tashi sukai jin ana kiran sallah Suka nufi famfo sukai alwala sannan sukai sallah babu yadda batai da Ameerah akan ta tsaya ta ci abinci ba amman taƙi haka sukai sallama Ameerah ta wuce Gida....

LAGOS STATE
_EKEJA BARRACKS_

AUTA 09022260850

*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*
*Ina masu kananan nono?*
*Ina masu yaye?*
*Ina yammata da ake shirin aure?*
*Ina matan gida masuson gyara?*
*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*
*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*
*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*

BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679
IG Bintus-spa-nd-more..
*BAƘON LAMARI...!*🌹
     { Eternal love }

           *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *003*

Zaune yake akan doguwar kujera wadda ya miƙe dogayen ƙafafun shi waɗanda har sun sauko ƙasan carpet sabida yanayin tsayin shi, Ya sanya yayiwa Kujerar Girma.

Jikinsa sanye da singlet army green ta sojoji sai threeqauter jeans, wanda shigar tashi ta bawa kirar jikinshi ta cikakkun maza damar bayyana.

Hannun shi riƙe da Tabar sigari Yana zuƙa ya haɗa ƙaramin Hadari acikin Falon Kunnen shi maƙale da waya wadda yake sauraran Muryar Zainab Budurwar shi wadda aka sanya musu ranar aure nan da wata Biyu masu zuwa.

Dawowar shi kenan daga wajan training ɗin koyar da dabarun yaƙin da suke wa ƙananun sojoji, waɗanda za'a tura Rinduna Shida kwantar da tarzoma a wani ƙauye dake zamfara Wanda har dashi acikin posting ɗin wanda shine ya kasance mai jagorancin rindunar farko kasance warshi ƙwararran captain ɗin soja wanda yasan ta kan dabarun yaƙi sosai.

"Baby yau she zaka shigo Kano ya kamata ka shigo wannan satin Momy nata tambayar ka sabida shirye shiryen auren mu"
Muryar Zee cikin iyayi take masa maganar.

Ya lumshe idanun shi cikin tsananin son da yake mata shima ji yake kamar yayi tsuntsu ya ganshi a kano don ya ganta yau kimanin watanni Biyar kenan baije Kano ba sai dai suyi waya da Æ´an gida dakuma Zee É—in shi.

"Nima ina ishir war son ganin ki My zee matsalar kawai yanayin aikin namu ne, amman idan kika yi haƙuri Very soon zamu kasance tare"
Ya faÉ—i maganar cikin dakakkiyar Muryar shi ta jaruman maza.

Kuka ta soma yi masa tana buga ƙafarta a ƙasa cikin yanayin shagwaɓarta dake ƙara narkar dashi cikin tafkin Kogin sonta.

"Ni yanzu kenan bazan ƙara ganin kaba sai kazo Biki fisabilillahi ka min adalci kenan? zuciyata da gangar Jikina son ganin ka suke amman kai ka zaɓi Ka nesanta kanka dani?"
Chapter 2 · 0% Book details