← Book details Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 20

Sashe 14

Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amman taji zuciyarta tayi sanyi tana Jin Ahmad shine rabin rayuwarta ta yarda ta kowace hanya mahaifiyarta tabi Idan har Burinta zai cika ta sami Muradin zuciyarta.
*********************
Ya tashi da tsananin mamaki acikin Zuciyarsa na yadda Amatu tai ko in kula da ƴar Cikinta haka ya shirya ya fita yayi sallar asubahi ya dawo ɗaki Lokacin Iman ta tashi tana ta tsala Ihu Jin Kukan yake na juyar masa da kanshi da sauri ya ɗauketa da madararta yayi Falon Mama yana Kiran Naja'atu wadda ta fito da Hijabin sallah a jikinta ta zube tana gaisar dashi ya Miƙa mata Iman yana cewa ta bata madara ta Goyata.
Amsar Yarinyar tayi cike da Bin Umarninsa haka ta Juya É—aki shikuma ya Nufi ÆŠakin Alhaji Domin su gaisa.

Zaune ya tarar da Mama da Alhaji suna hira a ɗaki yayi sallama suka amsa ya zauna a ƙasan carpet yana gaishe dasu Bayan sun gaisa Alhaji ya dube shi Cike da kulawa yana cewa.
"Ɗazu muka gama maganarka da kawunan ka Ina ganin yau zasu je Gidan su yarinyar nan kawai zamu kai Lefe Jibi idan muna raye tunda Lefan ka daman yana ƙasa Idan yaso nan da wani satin in suna shirye a ɗaura aure matarka ta tare agidan ka dake Bayan layi abin da baka ƙarasa ba sai ka Ƙarasa Da wuri Tunda zaka jima anan Ɗin gwara ka zauna da matarka"
Tunda Alhaji ya soma maganar yayi ƙasa da kanshi Jin maganar yake daga sama Sam baze iya musu da maganar Alhaji ba amman yaso an ɗan ɗaga Bikin an barshi kamar yadda yake ada sabida yana da shirin da ze a ƙasa amman Tunda Alhaji yace ayi Ɗin hakan za'ai babu ja.

"Baka ce Komai ba Babana ko kana ganin abar shi kamar yadda yake? ni abin da yasa nace ayi Yanzu sabida naga ka sami Lokaci ka dawo Kano Komai zai zo maka da sauƙi"
Cewar Alhaji wanda yake maganar Cikin dattako.
"Alhaji ba wani abu abar shi hakan Allah ya ƙara Girma"
Daga haka yaja Bakinshi yayi shuru Mama ta bishi da kallo tana yaba tsananin Biyayyarsa.
Duk Yadda baya son abu idan suka umarce shi dayi baya Musu tana addu'ar Shima Allah ya bashi masu yi masa Biyayya kamar yadda yake Yi musu.
"Binta ke baki ce Komai ba?"
Cewar Alhaji.
Mama tayi dariya Ta kauda kanta Gefe.
Alhaji yayi dariyar shima yana mamakin wannan alkunya da Mama kewa Ahmad.
Ya jima suna É—an tattaunawa da Ahmad É—in kafin Suyi sallama ya wuce ÆŠakin sa.

Alhaji ya kalli mama yace mata.
"Kinga yaron nan naki badai zurfin Ciki ba koda abu bai masa ba baze Fito fili ya faÉ—a ba sai yace to"
Mama batai magana ba ta miƙe ta fita waje dan ita a tsarinta taso abar Ahmad yay Bikinsa anutse amman Tunda Alhaji yace ayi a yanzun hakan za'ai babu ja.

Da Naja taci karo tana Faman damben bawa Jaririya Madara.
Mama ta dube ta tana cewa.
"To farin shiga kada ki shaƙawa ƴar mutane madara a hanci Ina kika samo ƴa da wannan safiyar?"
Naja tai dariya tana É—aga Iman tana Cillawa tana cewa.
"Wallahi Yaya ne ya kawon ita tun ɗazu Nima ban san A ina ya samo Ƴar nan ba mai kyau da ita"
Cikin ɗunbin mamaki Mama ta saka Hannu ta karɓi yarinyar tana kallonta.
"Ai wannan Æ´ar Gidan Amatu ce haka ta Girma Ma sha Allah"
Mama ta faɗa tana Ƙurawa Iman Idanu.
"Lah Dama ƴar gidan Amatullah ce ƙwarai kuwa sabida Naji ameerah tace tana Gida Tun ɗazu Yaya ya kawon Ita yace na kula da ita"
Mama ta riƙe haɓa bayan ta ɗora Iman kan cinyarta tana cewa.

"To in ban da abin sa ya za'ai ya rabo Ƴar da take shan Nono da mamanta fisabilillahi zaizo ya same nine"
Mama ta faɗi bayan ta tashi riƙe da Iman a hannunta tayi Cikin Bedroom Da ita.
Ahmad wuni yayi a É—akin sa bai fita ko Ina ba Sai da akai la'asar sannan yayi wanka cikin wata Blue shadda ya shirya kansa ya fita.
Kai tsaye sashin su Amatullah ya nufa domin ya duba Jikin baba.
Yadda ya sami Baba abin ya ɗaga masa hankali Waya yay ma wani likita abokinsa akan zai kawo baba ya duba shi abokin nashi yace baya kano amman zai dawo Next week Bayan sunyi sallama ya kuma yiwa baba Sannu ya tashi ya fita A tsakar Gida suka haɗu da Umma wadda ganin Ahmad yasa ta daburce taƙi ma haɗa idanu dashi Shiko ya saki Jiki da ita sosai suka gaisa.
Sannan ya kama hanya ya fita part ɗinsu ya koma Kai tsaye yayi falon mama wadda tun kafin ya zauna ta rufe shi da faɗa tana cewa ya ɗauki Ƴar Amatu ya kai mata kayarta.

Ya saki ƙayataccen Murmushi tare da cewa.
"Mama ai ta bar min tunda Taƙi zuwa ta karɓe ta"
Daga haka yayi mata sallama ya Nufi Mota domin zuwa gidan su zainab wadda ta ishe shi da waya.

Tafe yake yana tuƙi yana sauraran Wa'azi acikin Motar tashi Karaf kamar ance ya ɗaga kanshi ya hangeta ta tattare zani zata tsallaka titin daze Shigo da ita layin.

Amatullah dawowarsu kenan ita da sabuwa daga wannan Gidan dai na Jiya wanda yau ma sun daki Gurbi dan da suka je wai Matar Gidan ta fita bata nan haka sabuwa taita Mita daga nan Æ´an shige shigensu sukai Gidajen masu kuÉ—i wanda anan Amatullah ta samo Abinci wanda ta É—aure a leda ta tawo dashi Gida bayan sun rabu da sabuwa a bakin babban titi.

Sakin zanin Jikinta tayi bayan ta tsallako Tana mai dafe ledar abincin tana tafe kamar iska zata kwasheta dan tsananin Sauri Burinta taje ta amso Iman dan haƙurinta ya ƙare a wannan Lokaci.

Caraf taji an damƙi Tsintsiyar hannunta da ƙarfi Juyawar da zatai domin tai magana taga Ahmad Ne Riƙe da Hannun nata kafin ya soma janta har zuwa bakin Motar shi ya Buɗe Gidan gaba ya shigar da ita ciki kafin ya rufo ta ya koma mazaunin Driver ya zauna Fuskarnan tashi babu alamun Dariya........
*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*
*Ina masu kananan nono?*
*Ina masu yaye?*
*Ina yammata da ake shirin aure?*
*Ina matan gida masuson gyara?*
*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*
*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*
*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*

BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679
IG Bintus-spa-nd-more..
*BAƘON LAMARI...!*🌹
{ Eternal love }

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*14*

Cikin dakakkiyar Muryar shi mai cike da amo! ya furta.
"Daga Ina kike dan baki da Tunani shine zaki wani kwaye Cinya a waje kina tsallaka Titi bakya ko tunanin wani yaga Jikin ki a yadda kike?"
Ya faÉ—a yana mai zuba mata Girman Idanun sa ya kafe ta dasu yana jiran Amsarta.
Shuru tayi Bata iya bashi amsa ba Wanda hakan ya Kuma bawa cikin motar damar Yin tsit babu abin da ke tashi sai sautin wa'azin daya kunna acikin motar tashi sai Kuma ƙamshi da sanyin Ac.

Rintse idanunta tayi ta Kulle su gam tana sauke ƙaƙƙarfan Numfashi tana jin yadda idanunsa ke yawo a saman fuskarta.
Ba zata iya ba, bazata iya Jure wannan yanayin ba kallon sa gareta yana jefa zuciyarta Cikin wani yanayi wanda ya shuÉ—e ada!.
"Amatuhh!!"
Yaja sunan cikin wani yanayi mai wuyar a fasalta shi.
Hawaye ne mai zafi ya soma gangaro mata a saman fuskarta yana Jiƙa gaban rigarta.
Dama zata iya dama hakan ba haramun Bane data raɓu da jikin Yayah Ahmad a wannan Lokacin ko hakan zai zama garkuwa gareta Ko hakan zai saka taji salama acikin zuciyarta yaya zatai wadda tafi kowa kusanci gareta UWA! Ta juya mata baya ta mayar da ita abokiyar gabarta Akan Kuɗi!

Ta kama Ledar Abincin dake hannunta ta matse gam ta mayar da Jikinta waje ɗaya ta cure ta cigaba da zubar da hawaye mai zafi wanda zuwa wani Lokacin Kuka mai sauti ya soma fitowa daga gareta Kuka take mai ƙarfi wanda ya cika Ilahirin Motar.
Ahmad ya rintse idanunsa nan da nan Jijiyar dake kanshi ta Miƙe Ya fesar da zazzafan Huci Duk wasu makaman faɗan sa daya yi Niyyar Sauke mata akan Bar masa yarinyarta datai Jiya ta kwana yaji ya zubar dasu.

Yana da rauni matiƙa Ga Jin kukan Mace macen ma....
Ya kasa ƙarasa faɗin hakan a zuciyarsa.
A raunane ya juyo gareta rauni wanda ya jima baiji shi gare shiba.
"Meye na kukan Amatuh gaya min matsalolin ki Please kada ki Ɓoyen Komai Ki fitar da duk wani abu aranki Ni yayan kine Zan share dukkan hawayen Ki"
Ya faɗi hakan muryar shi can ƙasan maƙoshin sa yana danne zafi da raɗaɗin da yake Ji acikin zuciyar shi.
Chapter 14 · 0% Book details