← Book details Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 20

Sashe 12

Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kuma fuskantar sa taga yadda ya nutsu a gabanta yay ƙasa da kanshi sosai.
"Amatu tana gida fa Auren ta ya Mutu, wannan abu da shi na kwana na tashi dashi da Alhaji ya gayan Jiya duka yaushe akai auren nata amman yaron nan ya sake ta ga jaririya ina ga basu yi arba'in ba! sannan Ina son kaje kaga Jikin Babanka sha'aibu yakamata ai wani abu akan wannan Jiki nasa sannan Kuma ka ƙaro Kayan abinci Wa matan kawun ka da sauran matan gidan sai Kuma Kuɗin makarantar Yaran kawunka suma naji ance an koro su Jiya"
Dama a ƙa'ida idan sukai waya da mama tana gaya masa dukkan buƙatun Gidan da kuma abin da ya faru sabida shine Babba a kaf ƴaƴan gidan, Gudun kada a ce bata gaya masa Komai. To yau kuma ganin Allah ya kawo shi yasa take gaya masa waɗancan maganganu waɗan da dama tace zata bari In yazo ta gaya masa tun sanda yace mata zaizo.

"Sannan ina son Hafsa ta dawo gida ta haihu kaga haihuwar fari ce"
Ta kuma faɗin hakan duk da yayi shuru ya ƙi cewa komai.
"A,a mama ki barta a gidan ta kawai In yaso a É—auki mai aiki ta kula da ita"
Ya faÉ—a batare daya É—ago ya kalleta ba.
"To shike nan hakan za'ayi"

"Mama dama Amatu ta haihu aini ba wanda ya gaya Min, Shi Mijin nata É—an ina ne?"
Ya jefo mata tambayar.
"Kasan yadda auren yazo ai koshi Alhaji faÉ—an daya gama yi Jiya kenan ai Hadiza ta cuci Yarinyar nan Wallahi sam batawa haihuwa adalci ba"
Mama ta faÉ—a daga gani abun yay mata ciwo a matsayin ta na uwa.
Bai ce komai ba yaja Bakin sa yay shuru yana mamakin yau wace rana mama ta zage tana magana a gabansa wadda ko a waya bata jan doguwar magana dashi koda magana ce mai mahimmanci data gaya masa take kashe wayar.
Cikin haka Alhaji ya shigo wanda suka gaisa da Ahmad sosai kuma Suka tattauna akan aikin daya kawo shi wanda yace Nan da ranar Litinin Zai tafi can barrack Ɗin da aka Tura su wanda zasu haɗa team ɗinsu su shiga ƙauyukan sai dai zai na zuwa gida week end addu'a Alhaji yayi masa sannan ya Miƙe yana Musu sallama dan ya gaji bacci ne a idanun shi sallar isha'i kawai zai yi wadda tuni akayi babu shi sai ya kwanta...........*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*
*Ina masu kananan nono?*
*Ina masu yaye?*
*Ina yammata da ake shirin aure?*
*Ina matan gida masuson gyara?*
*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*
*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*
*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*

BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679
IG Bintus-spa-nd-more..
*BAƘON LAMARI...!*🌹
     { Eternal love }

           *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *12*

Lokacin daya fito daga Palon mama kusan ƙarfe taran Dare ne, sabida haka alwala yayi ya wuce masallacin dake kallon ƙofar Gidansu yayi sallar Isha'in daya rasa Yana fitowa daga Masallacin suka haɗu da Kamal wanda yake Buɗe Gate zai shigar da Motar Shi daya kai masa wanki Tun jiya sabida Haka dakata wa yayi Kamal har ya shigar da Motar Cikin Harabar Gidan sannan ya Miƙo masa Keyn Motar.
Amsar Keyn yayi sukai sallama da Kamal ya Nufi Cikin Gida shi kuma Kamal ya Juya da tashi Motar dan ya kaita gareji sabida Harabar Gidan bazai ci mota Biyu ba dan haka iya ta Ahmad ce kaÉ—ai ta sami wuri a harabar Gidan.

Hadari ne keta haɗowa a garin sabida yanayin na damuna ne iska mai ƙarfi tana Kaɗawa wanda ya bawa Ahmad damar Ƙara sauri wajan shiga Gida sabida baya son ruwa ya taɓa shi Gudun zazzaɓin daya ke haifar masa Kuma ya lura Hadarin dab yake da zubar da ruwan sama.

Kukan Jariri ke tashi cikin kunnen shi Lokacin daya kai ƙofar shiga sashin su A hankali yake ƙara matsar da Kunnen shi zuwa Inda yake Jin sautin fitar Kukan Jaririn Tabbas ba Gizo Kunnen shi ke yi masa ba Ƙofar Sashin Kawun sa Sha'aibu anan yake Jiyo Kukan jaririn wanda har takai ga jaririn ya sarƙe yana tari Kukan yaƙi Fita ta daɗi.

Da sauri ya ƙarasa Cikin sashin Abin mamaki harya tura Ƙofar da aka karo ya shiga tsakar Gidan amman babu wanda ya fito daga ɗaki bare yasa ran sallamar daya ke yi za'a amsa masa.
A hankali yake Bin sahun Inda yake Jin kukan jaririn Bai sha mamaki ba sai da ya tsinci kansa a ÆŠakin daya haÉ—u da tarkacen Itace Duhu DumÉ—un acikin É—akin babu alamar Haske Hannunsa har rawa yake wajan ÆŠauko wayar shi dake aljihun jallabiyar shi.

Yana mai kunnata ya Haska É—akin da fitilar wayar tashi

Wanda idanunshi yakai masa Duba wajan Jaririyar Yarinya ɗanyar haihuwa yashe a ƙasan wani ƙaramin zani sai Kuka take Duk ta ɓata Jikinta da Dattin Sumuntin Ɗakin.
Cikin zafin nama ya ɗauke Jaririyar yana jijjigata ajikinsa har Lokacin bata daina Kuka ba sai cilla ƙafafu take.
A hankali ya saka mata harshen sa Cikin bakinta wanda ta kama tana mamula kamar ta sami Nono sai Kukan ya tsaya ta kama ajiyar Zuciya.
Haska yarinyar yayi sosai yana ƙare mata kallo tausayi da Soyayyarta a take suka Kama masa Zuciyarsa.

Hannunta ya kama wanda aka saka mata ƙaramar azurfa a ɗan ƙaramin yatsarta Da sauri ta saki harshen nasa ta canyara Kuka Har tana ƙwarewa.

Ya Kuma ÆŠorata a kafaÉ—arsa Kallo É—aya yayiwa hannun yaga Ya kumbura har yaja Ruwa.
Ya zaro idanunsa waje yana mamakin Rashin Imanin uwar yarinyar da bata san ya rayuwa take Ciki ba amman an barta cikin tsananin azabar Ciwo a hannu ba tare da an kula ba.

Amatullah.
Tunda suka fita da Sabuwa bata dawo gida ba sai da akai Sallar isha'i Lokacin da suka je Gidan Alhaji Idris mai kwano masu gadi suka hanasu shiga sabuwa taita Kiran Number Hajiya Zahra bata same taba sabida Haka sai kawai suka Juya Koda suka juya ÆŠin a hanya Amatullah ta sanya wa Sabuwa Kuka akan cewar bata da Daidai da KuÉ—in Maganin sauro bare abin da zata ci Ruwan Nono ya kawo Yarinyar ta tasamu Tsananin tausayin ta ya kama sabuwa sabida haka sai kawai tai Rijiyar Zaki cikin tasha Da Ita wajan Wata Hajiya Balki mai Abinci akan ta É—an yi mata aiki ko naira ÆŠari biyar ta bata Cikin Ikon Allah suna zuwa tashar ma Hajiya Zahran ta Kira sabuwa Sai dai ganin Magariba ta kawo kai yasa sabuwa tace mata Gobe
Zasu dawo Basu ma sami Hajiya Balki ba sai yaranta dan haka sai suka Juya Gida to sai sabuwan tace wa Amatullah ta Bita Gidanta taci abincin dare sai ta koma Gida Sabida Sabuwa tana jin tausayin Amatullah sosai.
Hakan akai Suka Nufi Gidan sabuwa Anan taci Abinci har akai isha'i sannan tayo Gida Bayan sunyi sallama da sabuwa.
Koda ta Koma gidan Bata sami tarbar arziƙi a wajan Ummah ba bare ta sami Darajar tace mata daga ina take sai ma ɓacin rai data riska dan Nana ta ɗaukar mata kayanta Kala ɗaya takai gidan Ɗinki an rage mata ta sanya su ajikinta Koda tai magana Nana tahau Gaya mata baƙar magana Hussaini Ƙaninta shine mai cewa sai ya ɓallata ya ɓalla banza sai da ƙyar Hassan ya riƙe Hussaini Amatullah tasha Kuka a ɗaki Sannan ta aje Iman a saman zaninta ta Ɗebi ruwan sanyi a rijiya ta shiga Banɗaki domin tai wanka Duk da ba Omo bare sabulu amman tasan Ruwan sanyi zai mata Maganin zafin daya Isheta.

Tajima tana kallon Gefen cikinta wanda tsargiyar É—inkin da akai mata na C's Ta cire tsaf wajan yayi Kyau babu alamun wata matsala Jan ajiyar zuciya tai aranta tana Godiya ga Allah daya sa wajan bai sami wata matsala ba ya warke ras.

Duk Budirin Kukan da Iman take sam bata jiba sabida Bayin yaÉ—an shiga Loko Haka ta gama wankan ta É—auro zani ta Fito kanta Ko É—an kwali babu.

Sai dai koda da fito Ɗin Ta tsinci kanta da tsananin faɗuwar Gaba sakamakon wanda ta gani a tsaye Riƙe da Iman A hannun shi yana jijjigata Tsananin tsoro da faɗuwar gaba ne suka Kuma ƙaruwa acikin zuciyarta Ko shekaru nawa zatai bata gan shiba bazata mance Kamannin saba YAYA AHMAD.
Ta faɗa aranta da sauri Kuma ta raɓe shi tai ɗaki har tana Bugewa da bango.
Chapter 12 · 0% Book details