← Book details Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 20

Sashe 13

Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kallo ya bita yana mamakin Ramewar da yarinyar tayi tome ke damunta?Ya girgiza kan shi yana mai juyawa Ya fita da Iman A hannunshi Wajan motar shi ya nufa ya BuÉ—e tare da aje Iman aciki ya zagaya ya buÉ—e Gate sannan ya koma ya fitar da Motar Sannan ya dawo ya rufe Gate ÆŠin ya Koma Cikin Mota yayi mata key yaja ya bar layin.
Kai tsaye wani ƙaramin Private Clinic ya kaita wanda Nurse suka karɓi Iman domin su duba Hannun ta kamar yadda yayi Musu Bayani Rintse Idanu yayi yana jin zafin yadda Ƴar ƙaramar yarinyar Keta tsala Kuka Lokacin da Nurse ke gyara mata Hannun nata wanda tace masa Buguwa ne tayi bayan an gyara aka shafa mata magani a wajan Ya biya Kuɗi sannan ya Shiga Mota sai da ya biya ta wani super market ya sayi madara ta Jarirai ya tambayi yadda ake haɗawa tare dasu pampers dasu Pida sannan ya ƙara Saya mata Riguna masu kyau sai yayo Gida.

Lokacin daya ƙaraso Gida tuni an soma ruwa da sauri ya shigar da Motar ya Kulle Gida sannan ya fito da Iman da kayan daya siya yayi ɗakinsa da Gudu gudu, Batare daya Bi takan Amatullah ba bare ya kai mata yarinyarta so yake yaga Gudun ruwan Haukanta........
Bayan ya shiga ɗakin ya rufo ƙofar shi ruwan zafi ya haɗa yay wanka ya Rage daga shi sai Guntun wando da singlet Itama Iman Tawul ya Jiƙa da ruwan Ɗumi ya goge mata Jikinta tas sannan ya sauya mata kaya wajan saka pampers ne yaci wahala dan har Gumi sai da ya haɗa yana gama shiryata ya Haɗa mata madara a pida da ruwan Ɗumi ya ɗaga kanta yana bata Cafkewa tai tana sha tana ajiyar Zuciya Har ƙwallar tausayin yarinyar ce ta tarar masa a idanunsa tas ta shanye Madarar dake ƙatuwar Pidar Ya kwantar da Ita saman Ƙirjinsa yana shafa kanta mai cike da suma Kafin wani Lokaci tayi gyatsa ba jimawa Bacci yay awon gaba da ita sai Fitar Numfashi mai ɗumi take.

Anan ƙasan Carpet yaja Pillow ya kwantar da kanshi Shima da yake Gajiya na Cin Jikinsa bai Minti Biyar ba bacci mai Daɗi ya kwashe Shi Batare daya yi Tunanin kaiwa Amatullah Yarinyarta ba.........

Amatullah.

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*
*Ina masu kananan nono?*
*Ina masu yaye?*
*Ina yammata da ake shirin aure?*
*Ina matan gida masuson gyara?*
*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*
*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*
*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*

BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679
IG Bintus-spa-nd-more..
*BAƘON LAMARI...!*🌹
{ Eternal love }

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*13*

Cikin mutuwar Jiki take sanya kaya ajikinta gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak, Yaushe ya dawo Gida Ina zai kai mata Iman ita bata son duk wata alaƙa da zata Haɗa ta dashi Dan haka Koma Ina ya nufa da Iman dole ya dawo mata da yarinyarta Tafaɗa tana Danno Bakinta gaba kamar Yana kallon ta.
Tana kammala shiri ta Fita tsakar Gida ta zauna Yayyafin ruwan sama na Dukan Jikinta Idanunta Lumshe Tana shaƙar Mayen Ƙamshin Turaren shi daya bari a tsakar Gidan Tun tana Zaune harta Gaji ta Miƙe ta fita harabar Gidan Ƙofar Gida a rufe Haka nan Gate Ɗin ma a rufe Jingina tayi da Bango Hawaye yana zubo mata Wa zata Tunkara da Batun Ahmad ya ɗaukar Mata Iman ya fita?

Haka ta koma cikin Gida gaba ɗaya Jikinta yayi mata sanyi ɗaki ta wuce a wannan dare Bacci Ɓarowa shine yayi awon Gaba da ita daman Ga jikinta Duk ta gaji.
Wajan Asubah zazzaɓi Duk ya rufe mata Jikinta ga Nononta ya samƙame Ya ciko sabida Rashin sha da Iman batai ba zuwa asubahi kanta ya soma yi mata azababban Ciwo a daddafe ta Fita tsakar Gida tayo alwala ta dawo ta zauna tana azkar Ta jingina kanta Jikin itace wajan shiddan safe ta Fita ɗakin Baba ta gyara shi sannan ta koma ɗaki ta kuma zama ji take Kamar tai tsuntsu ta ganta a gaban Iman bata san tana son yarinyar taba sai da ya nisanta ta da ita.

Kuka take a wannan Lokacin domin ta kasa jure rashin Iman.
"Amatullah Lafiyar ki, kike kuka?"
Taji Muryar Ameerah a saman kanta wadda sam bata ji Sallamar da Ameerah ke mata a É—akin ba.
Ta É—ago jajayen idanunta ta zubawa Ameerah Tare da cewa.
"Ba komai Idona ke min Ciwo"

Da sauri Ameerah ta aje kwanon abincin data shigo mata da shi a gabanta tare da zubewa a kusa da Amatullah ÆŠin tace mata.
"Yaya naga Kina kuka da idanuna sannan Kice Idanun ki na maki ciwo Ina Iman ban ganta ba?"
Sai Amatullah ta kuma fashewa da kuka tana cewa.

"Tun jiya ya tafar Min da Ƴata ko ina ruwan shi dani Oho dan rashin Imani ya tafar Min da ƴata bai dawo Min da ita ba"
Da sauri Ameerah tace.
"Waye Imran? garin yaya?"
Tura baki Amatullah tayi tare da cewa.
"Yayah Ahmad Mana"
Jimm ameerah tayi Batai magana ba har tsayin wasu Lokuta Kafin tace.
"Meye Ya haÉ—a ki da shi da har ya ÆŠauki IMAN É—in?"
Cike da Mamaki Ameerah ta faÉ—i maganar.
"Oho mai"
Amatullah ta faÉ—a tana mai cigaba da kukanta.
Ameerah Danne abin da ke taso mata a zuciya tayi kafin ta shiga rarrashin Amatullah tana yi tana kawar da sharrin shaiÉ—an a zuciyarta.
Da Ƙyar ta Lallaɓa ta taci Indomie da ƙwan da ta da fo mata sannan Suka fita Ameerah na ce mata tazo suje wajan Mama ta gaya mata Ita kuma Amatullah taƙi tace yaje ya kwaɗanta Iman ɗin ya cinye.
Ranta Babu DaÉ—i ta fita daga Gidan tayi gidan sabuwa koda taje can ma sabuwa taita tambayarta meye ya kumbura mata idanu tace ba Komai Haka suka tattara don tafiya Gidan aikin nata.
***************
Da Gudu Ameerah ta shiga Cikin Gida tana yada kwanon tana kiran Anty wani azababban Kishin Ahmad na cin ranta.
Da sauri Anty dake haɗa ma Ƙanin Ameerah abinci ta fito tsakar Gida Tana cewa "Ke! Nifa nagaji da wannan ɗagamin Hankalin da kike jiya kin shigo min gida a firgice yau ma haka Uban me aka kuma yi Miki?"
Rungume Anty tayi tana cewa.
"Anty zuciyata raguwa ce na kasa lafawa duk wanda zai Raɓi Yaya Ahmad Anty zuciyata zata Buga Jina ke kamar zan Mutu in ban sami Yayah ba"
Anty ta shiga shafa kan Ameerah tana jin RaÉ—aÉ—i acikin zuciyarta na yadda da ranta da lafiyarta Æ´arta ke neman rasa Nutsuwarta akan É—a namiji.
"Ki shuru Ameerah kada Mutan gida suji me muke ciki wuce Muje ÆŠaki maza"
Jikin Anty har yana rawa tama mance da wani Abincin da take zubawa suka nufi É—aki suka zauna a saman Kujera Ameerah ta É—ago Fuskarta datai jage jage da hawaye tace.
"Anty jiya fa ƴar Amatullah a wajan sa ta kwana Fisabilillah meye haɗin sa da ita yanzu naje na tarar tana ta Kuka Da ƙyar na danne zuciyata na Dawo gida Anty Nifa bana son naga yana kula ko wace mace idan bani ba duk da nasan Amatullah ba zata ci Amanata ba domin tasan yadda nake son shi"
Anty ta zunduma wata irin ashar tana miƙewa tsaye.
"Dama kece Wawiya waya gaya Miki yanzu akwai amana ai wanda ka yarda dashi shiyake fara cin amanarka dama ni fa wannan tsinanniyar yarinyar bana ƙaunar ta bana son ta wato Har yanzu bai haƙura da ita ba kenan?"
Da sauri Ameerah ta Rufewa Anty Baki tana cewa.
"Nifa Anty bana zargin Amatullah kawai Kishin Abin naji acikin zuciyata amman wallahi kamar yadda yaya baya ranta itama haka bata na shi ran"
Anty Tayi juyi tana cewa
"Dama Yaya sai da tace min sai na tashi tsaye akan Ahmad sannan haƙar mu zata cimma ruwa sabida haka bana jin Ko ita waccan Ƴar mai kuɗin zan bari ya aura dan haka daga yau ki soma shiri Cikin ko wani yanayi zaki iya jin An ɗaura auren ki da Ahmad Ina shine Burin ki to kisa aranki wannan Buri naki cikakken Buri ne sai kin aure shi ita kanta uwarsa sai dai ta koma ƴar kallo"
Anty tana faÉ—in haka ta É—auki wayarta ta shiga kiran Yayarta a waya ta shige É—aki tabar Ameerah da nazarin maganar tata.
Mintuna kaÉ—an ta fito da mayafi tana cewa ameerah ta kula da gida zata Fita anguwa.
Chapter 13 · 0% Book details