← Book details Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 20

Sashe 19

Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Parking yayi a parking space na gidan yana ciro wayar shi ya shiga kiran Zainab wadda duk ranta ya gama ɓaci da yadda Ahmad ya shanyata kowa yana wajan Event ɗin ita kaɗai da ango ake jira sai waya ake mata har ta gaji da ɗaga wayar mutane.
"Ina parking space Ki fito"
Daga haka ya katse wayar yana mai jingina da Jikin kujerar.
Zainab sai da taja lokaci mai tsayi kafin ta fito ita kaɗai jal sabida tana Gudun wata taga angon nata a ƙawayenta yasa tace Musu suyi gaba zasu zo ita dashi.
Da yake akwai haske a wajan wannan ya bawa Amatullah damar ƙarewa zainab kallo wadda take tafe kamar wata ɗawisu taci gayu bana wasa ba wanda nan da nan Amatullah taji ta raina kanta.
A hankali ta ɗora hannunta saman Iman dake Cinyar shi ta ɗauke ta tana ƙoƙarin fita daga Cikin Motar.
"Ina kuma zaki?"
Taji tambayar tashi akan ta tun kafin takai ga fita.
"Zan koma gidan baya ne Yayah Naga Antyn tawa zata shiga nan"
Ta faÉ—a Muryarta na rawa.
"Koma ki zauna malama"
Bata bi ta kan maganar shiba ta ja ƙofar ta Fita ta koma gidan baya ta zauna tana faman zaro idanu waje.

Ƙamshin turaren Zainab ya cika Motar wadda take ta faman masa ƙorafi akan ya jima bai zo ɗaukarta ba.
Sai wani langwaɓe masa take tana faman zuba masa shagwaɓa bai kulata ba yaja Motar a sukwane suka bar Gidan.

Amatullah ta saki bakin mamakin muskilancin sa au matar daze aura ma haka take fama dashi tunda ta shigo take magana yayi mata banza.

Kukan Iman ne ya sanya zainab ta farga akwai Mutum a motar da sauri ta juyo ta dubi Amatullah wadda suka haÉ—a idanu da ita.
"Dee wannan wace a bayan motar ka?"
Jin tambayar yayi kamar rainin wayo idan ya bata amsa ya zama Bin Umarni dan haka yayi mata banza.
Itama Kuma Amatullah haka kawai taji ta kasa gaida zainab Sannan ta kasa rarrashin Iman dake ta kuka harda ƙwarewa.

Wani Burki yaja.
ƙeeeeeee.
Kana ya juyo rai a ɓace ya dube ta.
"Idan ba zaki bata Nonon ba fitar Min daga mota shasha sha kawai wadda bata san ina ke mata ciwo ba"

Tsintar kanta tayi da sakin Kuka kuma taƙi bawa Iman Nonon sai ma ƙoƙarin Buɗe Motar da take yi zata fitan kamar yadda yace haka kawai taji zuciyar na mata Ƙunci ji take tana jin haushin kowa.

"Indan kika buÉ—e saina karya Miki hannun ki"
Ya faɗa yana ƙoƙarin tada Motar Zainab wadda suka Kulle mata kai da mamaki tabi wannan da kallo tabi wannan da kallo haka ta koma.

Ai ina ko sauraran shi batai ba Ta ɓalle Motar ta fice a zuciye tayi hanyar Titi zata tsallaka.
Da wani irin sauri ya Ɓalle nashi ɓarin yabi ta.
Kafin yaje har tai Nisa a ɗaya ɓarin.
"Amatu ke Amatu ina zaki da daren nan baki da hankali ne?"
Ya faÉ—a yana binta da sauri.

Ina kafin yaje harta sha wata kwana wadda sai da ya haÉ—a da Gudu kafin ya cimmata.
Yana zuwa Gabanta ya saka hannu ya wanke ta da wani irin Mari wanda sai da taga wuta  a gigice ta saki Ƴar a ƙasa tana mai zubewa Itama a ƙasan tai zaman Bori tana Zunduma Ihu!
"Mai nayi maka zaka mare ni Ina ruwanka dani"
Ta faÉ—i maganar kamar bata hayyacin ta.
Tashin hankali cewar Ahmad Cikin zuciyar shi kafin ya É—aga Iman yana cewa.
"Dan baki da tunani ina zaki je anan wajan ina kika sani danna gaya Miki magana shine zaki fushi saboda Kinga ina shiga Hurumin ki"
A zafafe itama ta É—ago tana cewa.
"To ka dena shiga hurumina mana kaga idan zan Mutu zan rayu tunda uwata ma ta juyan baya na rayu waye zai Juyan baya na Mutu ka tafi ka barni na rayu da Æ´ata Wallahi duniya zan shiga na gaji nagaji da wannan bala"in kowa baya sona na rasa gatana"
Ta faɗi tana kwanciya a ƙasan wajan.

Ya haÉ—a Gumi ya share to duka mai ya kawo wannan abu?
A hankali ya É—agota ya Sanyata ajikinsa ya Rungumeta wanda ya bawa Kukan nata damar tsayawa.

"Ya isa muje Gida mutattauna Ni ban tsane kiba Amatu Kiyi haƙuri In marin danai Miki ne Ga fuskata nan ki rama"
Ya faÉ—a Muryar shi tana sauyawa.

Tsintar kanta tai dajin wata Irin faÉ—uwar gaba.
Zuciyarta tana ce mata Amatullah Hakan fa haramun ne yakamata ki sanar dashi da auren Ki ya daina raɓarki.
A hankali ta zare Jikinta anasa tai gaba tabar shi a baya haka ya bita kamar raƙumi da akala Har suka je Motar sai dai abin mamaki babu zainab babu dalilinta acikin Motar wadda tuni zakara ya bata sa'a ta bar motar.

Haka ya lallaɓata ta shiga Ciki ta zauna yaja Motar ya nufi Gida sai dai zuciyarta babu daɗi na yadda Tai masa rashin Kunya a ɗazu.

Koda suka je Gidan ma tana amsar Iman tai cikin É—aki har washe gari ranar juma'a wunin É—aki tai haka kawai take Jin faÉ—uwar Gaba na ziyartar Kirjinta.

Daga Gidansu zainab Kuwa haka akai shagali ba amarya ba ango Sai dai koda Hajiya mahaifiyar zainab ta koma gida tai mamakin yadda taga zainab ta hargitsa Komai na É—akinta tana ta kuka duk ta birkice.
Nan da nan hankalin mahaifanta ya tashi sunyi tambayar Duniya ta gaya musu meke damunta taƙi sai da Ƙyar ta iya furtawa mahaifinta cewa.

"Dady na fasa auren Ahmad koda shi kaÉ—ai ne yay saura a mazan Duniya saboda ina zargin sa dayi wa wata yarinya ciki dan Jiya abin da nagani ya É—agan hankali da ita fa yazo har nan ya tafi dani wajan Event sai dai a hanya data Turje haka ya barni a mota ya bita agaskiya Dady ni na fasa auren shi kawai"
Ta faÉ—a tana kuka sosai.
"A,a Ƴar Dady ya kamata ki soma Bincike kafin ki zartar da Hukunci akan shi Gudun Yin dana sani"
Cewar mahaifiyarta.
Ta É—ago da idanunta da sukai jajir sabida Kuka tace wa Hajiya.
"Dama nina kawo maku shi nace Ina son shi to yanzu na fasa in kuma Kuka yarda kuka auren shi to zaku rasani, Yarinya ƙarama ya samu ƴar talakawa ya ɗirka mata Ciki Ƙila ma dadiro ya mayar da ita gashi nan Jaririyar kamar su ɗaya"
Duk yadda Iyayen zainab suka so ta basu damar Bincike taƙi haka dady ya fita da ɓacin ran yadda tasa zai abun Kunya wato magana Biyu.
Da tsananin nauyin abin da zai cewa Iyayen Ahmad ya kwana har ranar ɗaurin aure ya kasa Tunkarar wani dan ya gaya musu cewar Ƴarsu tace ta haƙura.

Yau ta kama Asabar Ranar ɗaurin auren Ahmad da Zainab Tun safe Yake kwance a ɗaki ya kasa wanka abokan shi na ta masa waya akan ya shirya ya kasa kataɓus Babu abin da yake So ya gani kamar Amatu kwana ɗayan dayayi bai ganta ba ji yake kamar ya shekara Gashi kuma ya fahimci kamar haushin sa take Ji ta kulle kanta Ko falon mama bata fitowa tana ɗaki ita da ƴarta Haka dai ya Miƙe yana Jin duk babu daɗi ajikinsa wanka yayi tare da sanya Farar shadda ƙal sabuwa wadda tai masa Matiƙar kyau ya fesa turare ya ɗauki wayar shi ya fita.

Adaidai wannan Lokaci itama Amatullah tai wankanta ita da Iman Mama ce ta aiketa sashin su kawu dan ta amso robobin rabon abinci kamar ance ta ɗaga kanta ta hangi Imran Tsaye shida Ummah a bakin ƙofar sashin su sai dai daga gani magana suke mai mahimmanci gabanta yay wani Irin faɗuwa tana Ƙoƙarin juyawa domin ta Koma  Sashin mama
Ummah ta nuno ta wa Imran wanda yay wani Irin tsalle ya damƙo hannunta yana lashe bakin sa.

"Yau zaki zama nama na yau Ishirwar dana jima ina Ji zan kawar tabbas ayau duk Nacin ki sai nai yadda naga dama dake wuce Mota mu tafi Gida kwaÉ—ayayyar Uwarki ta sallamamin Ke"
Ya faÉ—a lokacin da yake jan hannunta tana Doke shi.
Yana ƙarasawa gaban Ummah yay raurau da idanunsa tare da cewa Ummah.
"Kinga ni dai yadda take Doken hannu ko? ummah ke kina kallon kamar bana son mai da ita ne a,a wannan abubuwan da take Min  shine yake fusatani"
Ya faÉ—a cikin kirsa da iya haÉ—a sharri Umma ta sanya Hannu ta doke Amatullah tare da ce mata.
"Shegiya mai ƙashin tsiya Kinsan Allah yau sai kin bishi ba zaki kuma kwanar Min agida ba daman zuba Muku idanu nai"
Amatullah Kuka take tana tirjewa tana cewa.
"Ummah ki bari na gaya Miki waye Imran dan Allah kada ki turani inda zaki nadamar Kukan da ba hawaye"
Sai dai Ina ummah idanunta ya rufe sai ma ƙara Danƙara mata baƙar maganar da take tare da aibata ta.

Ganin tana ɓata masa Lokaci ne yasa ya Soma janta ta ƙarfin tsiya.

Ahmad dake amsa wayar Alhaji wanda yace ya same su a babban masallacin layin wanda zasu haɗu ashiga Mota a tafi wajan ɗaurin aure da sauri ya mayar da wayar Idanunshi har wani hazo yake ɗauka Lokacin daya ga Wani ƙato najan Amatuh tana kuka.
Da sauri ya ƙaraso wajan Imran wanda har ya kusan Kai Amatu Bakin gate.
Wani mari ya Zuba wa Imran kafin ya juyo ya kuma bashi Wani.
"Uban wa ya baka damar Taɓata har zaka shigo gidan mutane kana janta dan kai ɗan akuya ne"
"Nice nan na bashi wannan dama nida na kawo ta Duniya"
Cewar Ummah data ƙaraso wajan cikin masifa
A fusace Ahmad ya Juyo wajan ummah yana cewa.
"Ke kam ba uwa bace wallahi Na rasa wace Irin mace ce......."
"Yaya Ummah fa mahaifiyata ce dan Allah kada kai faÉ—a da ita"
Amatu ta faÉ—a tana kuka.
Chapter 19 · 0% Book details