← Book details Arnan Daji 1 And Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 52

Sashe 7

Arnan Daji 1 And Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A razane suka juya wazasu gani baban rama ne da mado saurayin aduke Wanda za ay musu aure bana sunasan junansu so me tsanani anan mado ya durkushe yafara sharar kwalla duk dauriya irinta mazan ARNAN DAJI hakan besa ya daureba abun yay masa ciwo baban rama ya duka garin Yaya haka tafaru rama tafara kuka tafara magana muna zaune nida aduke mungacin farfesun kwadin datay mana mun ajiyewa tenkwai nata saita rigani wanko hannu bayan ta dawo saina fita Nima saina zaga bayan gida ina fitowa nadinga jin magana sama sama sai nadanyo sanda na labe sainaji yana cewa ina rama bazaki gayan inda takeba saina kasheki badu ya temakeka bansan inda rama tayiba Ni Bata gidannan Sam bazaki fada ba toko zanmiki abunda zanmata amadadinta nayarda kayimun komeye Raina fansane ga Yan uwana meye amfanin rayuwata inaganin Yan uwana cikin wani hali tana kuka take furta masa haka Nan ina labe ina kallo yafara cire kayansa ya juya baya saina fito Ashe aduke taga tahowata tace na koma naki na tsaya saida tahada hannayenta biyu tana rokona sannan na koma dakinka na buya saidayasha yay mankas sannan ya farwa aduke tana ihu yana zabga mata mari ahaka ya farkata farkawa ta rashin mutunci ya yagalgalata bakaramin ta adi yay mataba banjin akwai maganin dazewa aduke aiki harta gyaru takarasa cikin kuka idon mado jage jage da hawaye way waye waye sukai shiru saida baban rama ya daka musu wata mahaukaciyar tsawa ba magana ake mukuba waye da wannan danyen aiki me kikai masa ke rama daya biyoki har gida cikin rishin kuka ban masa komaiba yadade yana neman mu kadaice nakiya saboda shize auri kawata aminiyata bazan iya cin amanartaba yasha tareni a jeji ina guduwa shine ya biyoni har gida a yau besamanba sai yasamu aduke shiru na minti biyar ya gifta adakin inbanda tashin kukan tenkwai da rama da aduke bakajin komai baban rama yay gyaran murya tabbas hayaki baze hakaba tayayama bayan shine da ze aureku rama bayanan yana daure a kurkuku saboda shine cikon mutum na biyar daza a yanka nasan kowaye ya aikata wannan lefin kurufamin asiri kurike alkawarin dakuka daukarmun karku gayawa kowa abunda yasameni karku bari kowa yaji cewar aduke wadda dakyar maganar tata take fita munmuki alkawari bameji fitar maganarma zata iya sawa a hallakamu cewar baban rama way waye kugaymun nifa banganeba cewar mado zan gayama kowaye Amma saikayi alkawarin bawanda zeji wannan batu mubarshi anan iya mu biyar dinnan Ni Kuma zanje dawa na nemowa aduke magani yanzu Inasan aduke har Raina bazan taba Bari wani yajiba Amma aransa ya kudurce sai ya dau fansa ja e ne dan gidan sarki kaho Yay mata wannan aikin kasan aikinsane a razane ya dago abokina ja e yaci Amanata na rantse da gemun kakana saina dau fansa yasa Kai ya fice sunata kwala masa Kira be juyoba sai suka kara rushewa da kuka.

Tofa muje zuwa nice taku maikaunarku akoda yaushe.

*FEEDYN BASH*
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: *?ARNAN DAJI?*

*NA*

*FAREEDA ABDULLAHI*

*_?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION_*??
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

45-50

_*GODIYA DA JINJINA AGAREKI ANTY FAUXY YAR AMANA, AMANA TAKAIMIKI GASKIYA SAMUN MACE KAMARKI AKWAI WUYA MACE BA HASSADA BA KYASHI ALLAH YA KARA DAUKAKI DA DUKKAN YAN KAINUWA WRITERS*_

*JINJINA AGAREKI MARYAM DANDAWAKI SANNU DA KOKARI ALLAH YAKARA DAUKAKI YAKAWO KASUWA ME ALBARKA NAGODE MAKU*????????????

A fusace suka juyo suga wacece wannan? cike da farin ciki ja'e yace "itace ku cimmata ku kamon ita yanzun nan".
Tariga ta fita hayyacinta kawai gani tai sun yiyo kanta gadan-gadan nan tafara gudu, gudu takeyi suna binta abaya haka suka dingayi har suka fara shigowa gari, nan suka dakata ita Kuma ta bazama cikin gari da gudu tamkar zararriya, bata zame ko inaba sai gida, tana shiga taga haryanzu tenkwai na nan da gudu ta fad'a kanta jiki na rawa bakinta sai karkarwa yake ta rirri'keta taboye abayanta "lafiyanki aduke menene? "
Sai kallo ba magana nanfa tafara girgizata amma ina bata hayyacinta bata magana, ganin haka yasa takamata suka fice daga gidan suka tafi nasu gidan suna shiga lamunde tace
"To sarakan yawo daga ina kuke? kunsan munada mara lafiya gashi harya fara motsawa Amma ya kasa tashi saboda ciwon kansa ya dai bud'e ido yai yun'kurin tashi ya koma"
cike da farin ciki take gaya musu taga duk sun mata shiru ba wanda ya kulata, tenkwai taja hannun aduke takaita dakinsu tazaunar ta fita ta d'ebo mata ruwa a tulu me sanyi tabata takarba tasha ba tace komai ba sai had'iyar zuciya take kamar zata had'iye zuciyarta, daukanta tenkwai tayi ta kwantar da ita batace komai ba sai binta da idol kawai take tamkar zararriya ganin komai take tamkar a mafarki, "wai ankashe babanta ancinyeshi anwa aduke fyade tana chan batasan halin datake cikiba" gaba d'aya kwakwalwarta ta dena aiki ta tsaya chak ta sandare kawai akwance, ganin haka tenkwai ta koma waje taleka d'akin majinyacinta da tunda tasa Kai Bata 'kara waiwayarsaba sai yanzu taganshi yana baccinsa hankali kwance ta tsura masa ido tana hango tsantsar kyansa da nagartarsa sabanin wancen Dan iskan ja'en daba wata nagarta atare dashi sai zallar iskanci ace shizata aura tazauna har karshen rayuwarta gwara ta mutu data aure shi tana fatan wannan bawa ya kawo wani haske a wannan garin nasu.

Yadauke idonsa daga kanta cike da takaicin yadda tazama tamkar gunki gaban wanda bemasan tanayiba shigashi yana tsananin kaunarta Amma Bata saniba gata kyakykyawa me diri mtsww yaja tsaki sai da jeddah takare masa kallo ta tabbatar da yay mata ? Nan takada kai takama hanyar fita daga hall din taja hankalin maza dayawa saboda kyanta Amma batasu takeba tafuce waje tanemi waje tazauna tana jiran taga fitowarsa ayko kafin atashi taga ya fito da sauri shida wani abokinsa sun durfafo inda take Nan takara suma azaune saida sukazo gab da ita taga yabude motarsa da hanzari ta tashi ta isa gabansa Tace "sannufa" yay mata banza kamar badashi takeba, abokinsane yayi karfin halin cemata "sannu y'anmata ya kike? Ta washe baki tare da qara yauqi ta amsa da "lafiya lau" Nan suka hau zuba dama shine Wanda ya ganta tun a ciki ta tafi dashi shiko be auraba tunda yaga kamar Yar hannunce yad'ana Amma zefi san ya aureta, dataga wankin hula na shirin kaita dare saitace "abokinka baya maganane" yadan kalleshi a sace yaga yadda ya had'a rai ransa inyayi dubu ya baci sun barshi a cikin mota kamar bawansu, bayasan wargi Sam besan wanna shegen kwashe kwashen na faruk ya jiyo ya kalleta have "haka yake bikiga ya bude mota ya shigeba" "gsky yay mun" ya kalleta "Ni Kuma kinmun yaza ayi? " tai far da ido "naima kamar Yaya? " wani murmushi ya sakar mata irin nasu na 'yan duniya sannan yace "kinmun a matsayin matar aure"
Dariyar ita ma Tayi sannan tace "kaban dariya wallahi ni gaskiya abokinka nake so shi yai mun shizan aura" ya'ke yayi don maganarta ta sosa masa rai amma ya dake yace "to ni a wane matsayin zaa ajiyeni?" "Abokina" ta fada da sauri sannan ta qara da "matsayinka kenan Kuma abokin mijina" Ya kalleta rai bace yace "To wannan da kike gani ansa masa rana Kuma bayasan babbar mace sannan baya kula mata".

Ta dago ta kalleshi tace "wanne temako zakay mun yasoni ya kulani?"
"Gaskiya babu" Ya bata amsa kai tsaye "zan dai baki card dinsa da number din wayarsa, Amma Ni mezaki ban?" Ya qarashe zancen da kashe ido irin na yan bariki,
"hmmm me kake so ajikina kafada da kanka zan baka shi? " cike da murna yace "kinyi alkawari? " bata amsaba ya dora da "kawai so nake ki mallakamun kanki"
Murmushi ta sakar masa na manyan bariki tace "dan dai wannan karka damu ka kwantar da hankalinka.
"zanbaki complementary card dinshi, yadda zaki same shi a office da Kuma number din wayanshi shikenan ko? "
cike da farinciki tace "shikenan ngde gaskiya"
"to muje murage muki hanya".

Tana tsaye taga kamar ya motsa da hanzari ta karasa kusa dashi tace "sannu kafarka? " saitaga ya bude idonsa Nan tacika da farinciki da gudu tafito waje cikin zumudi take kiran lamunde tana "Ya farka ya bude idonshi" lamunde ma cikin farin cikin tabiyota suka koma suka kamashi suka zaunar dashi sai binsu yake da ido ba umm ba ummun yakasa cewa komai kansa yakeji yay masa nauyi ya daure tam ya Kai hannu ya taba sai yaji a kulle yake ashe, yay shiru ya kasa magana Nan lamunde ta dakko masa maganinsa tabashi yasha shidai bece komaiba kawai binsu yake da ido, bai sansuba betaba ganin halitta irinsuba to Amma wayema shi meyake anan? beda amsar tambayarshi sannu suke ta doka masa yanata kallonsu kamar gumaka chan lamunde tace "begama hutawa be dawo hayyacinsaba mu kyaleshi ya sarara zuwa jimawa muje" suna fita Dan naci ta fakaici idon lamunde ta koma tasashi agaba tanata kallonsa tana murmushi.

Tunaninta daya yaza ay tayi rayuwa dashi dama haka yake idanuwansama kawai abun kallone shine zetafi da ita inda yake ya aureta ko kuwa waye shima batasaniba tambayar dataketaywa kanta kenan tabbas inasan shi zan rayu dashi bazan taba gajiya da kallonsaba.
Chapter 7 · 0% Book details