← Book details Arnan Daji 1 And Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 52

Sashe 45

Arnan Daji 1 And Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jeddah Bata zame ko Ina ba sai gidan wata dillaliya a Yan lemo Tai Mata bayanin komai ta amince akan kudi dubu dari biyu sunyanke maza za'a nema su karbi lefe su daura aure Baki alaikum haka ko akai ansamu wasu dattijan biri zauna gari banza aka tsadance su uku ta Kira alhaji labaran ta Gaya Masa komai dariya kawai yai ba matsala gobe karfe goma na safe zasuzo su kawo Haka ko akai washe gari ta Kama asabar aka kawo kayan lefe akwati Sha biyu sai kace wata budurwa budurwar ma ta yayan gata da sadaki dubu dari biyu da kudin gaisuwar iyaye dubu dari uku gaba daya dari biyar suka kawo murna kamar jeddah ta zuba ruwa a kasa Tasha daya tambayeta meyasa aka kawo Nan bayan da tace a dangwauro take sai ta waske kawai

Ai chan din babanta dama ya mutu mamanta Kuma Bata garin sunyi waya tace azo Nan gidan kanwarta Haka suka bar maganar bayan sati daya akai bikin afra aka kaita me Dile batai party ko daya ba sai dinner da ango yai bayan daurin aure an kaita gidanta suka Sha dinner dinsu tadai yi walima agidansu anyi biki lafiya angama lafiya duk wata kawa datasan ta barikice Bata gayyaceta ba iya Yan unguwar sune da Yan uwanta matar babanta bataso Tai wannan auren ba bakin ciki kamar tayime gashi ta samu mijin marainiya akwati takwas yai Mata komai Masha Allah sai muce amarya Allah ya bada zaman lafiya

Haka jeddah tadinga shirye shiryen ta tsaf dangane da nata bikin tasha gyaran jiki tayi kyau dama jikinta me kyau ne sai ta dawo tamkar wata fure Dan kyau tayi fes abunta gwanin Sha'awa biki ya rage saura kwana uku duk wasu fitinannun kawayenta ta gayyacesu Dan party suka shirya har kala biyar zasu watsu su lalace ya bude Mata bakin aljihu sai bindim bindim take a ciki gashi komai ya sauke mata na daki tasan ita me sa'a ce a rayuwarta bazata taba auren wahala ba wata kawarta ta hadata da wani hatsabihin boka megani har hanji yagama shiryata yadda zata tunkari gidan alhaji labaran Tofa maji magani jeddah koza a Kara dacewa

_*To fans sai naji comment dinku gaskiya na yanke shawarar Dena posting kowane book nawa a wasu groups din sai nawa Dan bakwa mun comment wahar dakaina kawai nake iya fans Dina kemun comment wallahi indai Banga sanji ba daga yau nadena posting din book Dina a kowane group nice taku a kullum a Koda yaushe*_

*Feedyn bash*
[10/23, 2:33 PM] 👯🏻Ummu Subai'a🎭: *🎭ARNAN DAJI🎭*

*NA*

*FAREEDA ABDULLAHI*

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Assalamu alaikum my fans inafatan Kuna lafiya Dan Allah kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu hakan ya farune sakamakon rashin lafiyar danake fama da ita kuyi hakuri kumin uziri ba kullum zan dinga muku typing ba Dan Allah kudinga kokari Kuna posting zuwa wasu groups din wallahi bazan iyaba abun dayawa nagode my fans nagode da kaunarku a gareni da tarin addu'oi in da kuke mun suke Kara bani karfin gwiywar faran ta muku kamar yadda bakwa gajiya dayimun addua akara hakuri dai dani👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻*

95-100

Jeddah duk wani shirye shirye ta Gama tayi gyara na tashin hankali ko budurwa albarka har wani yalo yalo take wankan inji akai Mata jikin ta yayi smooth ga alhaji labaran ya sakar Mata bakin aljihu facaka kawai take da kudi ta tattaro ta dawo gidan hafsa dillaliya hankalinsu kwance suke shirye shiryen biki wadda hafsa ta Zama uwar amarya ga wayanda aka debo haya a matsayin iyayen ta maza tunda dama mahaifinta ya mutu a matsayin abokans da Dan uwansa suke Tayo gayya ta manyan Mata matan dasuka amsa sunansu Mata wasu zawarawa ne wasu matan aure wayanda suka gagari mazajensu wayanda suke haduwa a shargallensu yammata ma ba'a barsu a baya ba bikine ta shirya shi nakece raini anshirya karya a bikin ko dayake da abun ai

Kawarta ce ta rakata gun boka sangamu ya Bata lakanunnuka da magungunan dazata mallake mijin ita kadai ta juyashi San ranta sannan ya Bata Wanda zata haukata haleema saboda bala'in haushin dukan datai Mata ya Bata Amma sai yai wata wata daya yake Fara aiki sannnan ya Bata Wanda zata kashe yayan Amma da sharadin indai aka kuskure wani ya ganta sanda take aikin ita zata haukace Kuma a haukan zata mutu ba magani ta yarda da hakan gears yaran su mutu nata su tsira ai ko tana tafiya Bata zame ko Ina ba sai gidansu ita da haleema ta Gama shirya duk wani plan ita da kwayenta ta ajiye su a hanya ta danna horn megadi ya bude Mata direct part din haleema tayi

Tana shiga ta tayi nocking aka bude Mata sannan ta zauna haleema ta hade fuska tan jiran Taji taima ta wani haukan na daban ko zancen banza Amma sai taga ta durkusa kasa tana hawaye kiyi hkr Yar uwata da duk abunda nai Miki ki ya femun nazo neman gafararki dama bikina za ai na kawo Miki iv nazo na Gaya Miki na nemi gafararki gaban haleema yai wani irin faduwa ta ringa addu'oi a ranta tana rokon Allah ya kareta daga sharrin Jeddah idan da wani mugun abun tazo Allah ya maida Mata da kayanta kanta ba komai na yafe Miki jeddah cike da farin ciki sai washe Baki take nagode sosai Yar uwata Nan suka dinga kwasar Hira Amma Jeddah Anya ko Baki garajan daura aure ba baku da tabbacin mutuwar suhail fa dariya tayi haba sadiya inbanda abinki suhail ai ya Dade da mutuwa shekara kusan daya ba amo ba labari ai Dole mu fidda Rai Kuma anga takalmansa a wajen da hularsa to shi Yana Ina har zaman makoki anyi Masa fa Kuma ai nayi takaba ko haleema dai kallonta take cike da mamaki ai kema kawai ki auranki Dan Kinga gaskiya da kyanki gwara ki Mori lokacin ki ki auren ki kema

Shiru kawai Tai Mata tana ta nazari chan Jeddah tace haleema Baki da abinci ne Tai murmushi Yana cooler a flask naci nawa saura na Yara debo kici to tace ta nufi kitchen din maryama ta koma bangaren haleema dama tunda Jeddah tabar gidan Al ameen yai Mata korar Kare tunda ta shigo tana jinta tana bayan kitchen tana wanke wanke ta Gama Kuma Tai zamanta bataso su hadu Sam Dan tanajin tsanarta fiye da yadda haleema ke tsanarta ta shiga kitchen din harda cire mayafi haleema Bata kawo komai ba ta debo hadaddiyar jelop din shinkafa taji kayan lambu da nusashshen kifi ta zuba a plate maryama na hangota tana ta mamaki kodai da gaske ta sauta

Ta bude freezer ta dakko drinks me sanyi ta duba ba kowa dake hangota ta warware zaninta ta kwanto maganin yaran ta barbada musu a ciki tana karkade hannunta maryama ta Kara lekowa Bata ga komai ba Amma jikinta ya Bata wani abun ta zuba ta dakko abincin ta dawo parlour tanata zurawa sunata hirarsu kamar gaske sai da taci Tai Kat Tai Mata sallama ta fito zata rakota ta hanata itako Maryama Sam hankalinta be kwanta da zuwan Jeddah gidan ba bataga dai me ta zuba ba Amma tabbas tayi wani abun tana Nan tana jiran ta tafi bacci me nauyi ya dauketa a wajen dama wajene me kyau

Tana fita ta fito da maganin da akace idan dai halima ta shaki kamshin sa zata haukace ta fef fesa shi yadda ze shiga wajenta abun tsautsayi me wanki yazo kawo kayan wanki ya ganta tuni ya kunshe bakinsa ya juya Dan shi tsoronta yake ba ruwansa Haka ta ja motar ta Tai gaba cike da murna tana fita direba na sako hancin motar yaran suka fito ansar ya taho da gudu ya fada kan haleema momy abinci to Dan gidan momy autan momy bara na zubo ma ta mike taje ta zubo masa Nan ya Fara cin abincin magriba tayi Jin Ana kwalla Kiran sallah firgigit maryama ta tashi ta shigo gidan da gudu taga yaran duk suna parlour ansar na cin abinci da sauri ta karbe ya saka ihu Yana Kiran momy

Lafiya waya taban autana cewar haleema ranki ya Dade nice banyarda da abincin bane Allah yasa ba Wanda yaci no ba Wanda yaci menene wato hajiya Ina taga Naga kamar maman asra tasa wani Abu a abincin to Kuma bacci ya daukeni kafin nazo na dauke na zubar ikon Allah wallahi dama sam banyar da da itaba maza jeki zubar shi Kuma insha Allah ba abunda ze same shi nasan dama Dan Ni da yayana tayi ba yayanta ba Dan ba yarda za ai taima yayanta Haka ko akai ta zubar ta Dora musu indomie suna ta Kiran abinci cikin 10 minutes ta kawo musu suka ci hankali kwance sunata hirarsu hankali kwance suna Al ajabin Hali irin na jeddah tunda duk cikinsu ba Wanda take bakon sa

Jeddah ta cika da farinciki aikin ta yayi batasan yayanta suna hannun haleema batasan Dana nata yayan ba ta dauka suna gurin hajiya shiyasa idan zaka Gina Ramin mugunta Gina shi gajere Dan karya fada dakai Haka ta koma gidan hajiya hafsa tayi yadda boka yace Mata na zubawa a abinci duk ta ajiye na cushe cushe duk ta tusa tayi kyau kyan Dan miciji idan Kika ga Jeddah tamkar fure angama komai an na biki anfara biki anyi shagali iya shagli anyi lunch anyi party ya ake dinner a Bristol palace guri yayi guri Mata masu ji da kansu sun hadu maza sugar Daddy masu ji da kudi sun hallara matane manyan Mata matan aure wayanda suka gagari mazajensu da zawarawa wayanda suka gagari gidansu da yammata wayanda suka gagari iyayensu matan bariki manyan alhazawa ne ke ta faka manyan motocinsu Nan aka Fara dinner anci an Sha
Chapter 45 · 0% Book details