← Book details Arnan Daji 1 And Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 52

Sashe 48

Arnan Daji 1 And Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suhail ya nemi izinin tafiya gida Nan uncle yace shize Kai su Amma matarsa fafur tace a bar Mata su fadeela beso ba Amma ya roki alfarmar su tafi su gaida su daddy sai dawo ta yarda da hakan dakyar suka yarda suka fito Tsoron mutanen garin suke da tarin gine ginen dasuka gani ya daga musu hankali tayi saudat sunan matar uncle tayi alkawarin nuna musu yadda zasu dinga kula da jikinsu Dan gabansu har wari yake dukansu da wani yauki saboda rashin kula gashi ko kamar zaka kitsa kansuma abun kallone ga gashi Amma Duk kwarkwata inbame dauriya ba baze iya zaman minti biyar dasu ba

Tayi mamaki da suhail ya iya tahowa dasu duk da Taji labarinsu Amma tayaya suhail yazama Dan wannan garin zata so taji suka rankaya gidan su suhail sukai horn me gadi ya bude musu sukai parking sai rike hannayensu take haka suka shiga gidan hankali kwance ma aikatan gidan gudu suke gani suke suhail fatalwane suka shiga parlour din sukai sallama alhaji da hajiya na zaune inalillahi wainna ilaihirrji'un muryar wanake ji kamar ta suhail nine mom da sauri ta juyo

Da gudu ya karasa shigewa jikinta mom sai kuka dad ko mutuwar zaune yai Yana kallonsu ya sake ta ya rungume daddy hamdala kawai yake dad mom da Baki fa nake Uncle yai murmushi kugama murnar sa shigo saudat ku shigo Mana cikin murmushi ta sawo Kai yammatan suka biyo bayanta a firgice daa ya Mike Suma suka mike gaba dayansu kawai gani sukai ya yanke jiki ya Fadi yanata nuna wani guri hankalinsu ya gama tashi gaba dayansu tofa fans meke faruwane dad yayi hamo

_To fans bari indakata anan inajin dadin comment dinku fans Ina kaunarku har raina muna tare iya wuya I love you Lodi Lodi masoyana💋💋💋💋_

*FEEDYN BASH*
[10/23, 2:33 PM] 👯🏻Ummu Subai'a🎭: *🎭ARNAN DAJI🎭*

*NA*

*FAREEDA ABDULLAHI*

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Dr rahmatullah s nepa
Maman asmeey
Ummou shureim
Princess maisar
Nahdy
Ummu khalifa
Princess deejah
Maman Amma
Maman hamra
Mmn auwal
Maman humaira
Nerner Aysha
Humaira
K'sdq
Mrs aminullah
Zeenatu
Khadija
Ummy labo
Jamsam
Nahdy
Queen
_*Kai wallahi kunada yawa bazaku lissafu ba masoyana na feedyn bash fans Ina godiya Wanda beji sunansa ba Dan Allah karyai fushi koyaji Haushi Kuma Kuna Nan tafe masoyana wannan page din nakune kuyi yadda kikeso dashi ina Jin dadin comment dinku masu comment karkuyi fushi musamman masu comment Dan Banda marasa comment 😂😂😂nagode masoyana na Amana*_

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Book 2*

110-115

Da hanzari mom ta debo ruwa Duk sun rude sai kuka suke suko su ramatu sai buya suke suna tunanin ko tsoronsu sukeji Duk da a dogayen riguna suke Amma ganinsu suke wasu daban kuka kawai suke a gefe sai da ta zuba Masa ruwan yai wata ajiyar zuciya ya matso jikin ramatu ya kamota itako a tsorace take ta saki wani irin ihu wallahi Indo ce wannan sak ba mis iko sai Allah Indo Amma wannan nasan ba Indo na bace kamace kawai sai kuka Nan suhail ya zubawa daddy ido daddy meke faruwane wallahi kamarsu daya da kanwata danake baka labari kullum jikinsu yai sanyi tunda sunsan labarin su Amma shi betaba bashi wannan labarin ba yadai ce iyayensa sun mutu da kanwarsa hatsarin mota tofa wata sabuwa cewar suhail Nan aka zazzauna aka dinga gaishe gaishe Nan suhail ya basu labarin komai be boyeba harda yadda lamunde ta tubure dantane tofa gaba dayansu zufa suke ketawa mom ko hawaye take wallahi karya take meya hadaka da arnan daji muguwa kawai shiru dakin yayi

Alhaji yai gyaran murya hajiya bansan rashin gaskiya Mana kinsan dai cewa maganar gaskiya bamu muka haifi suhail ba wani ihu suhail yai yai kan daddy Amma kafin ya karasa ya sume akadinga zuba Masa ruwa ko gezau hajiya kuka take wallahi idan ka kashe mun shi bazan yarda bazan yarda ba Dana ne nono na yasha wallahi sai nai shari'a dakai suhail ya mutu sai lallashin ta saudat takeyi Banda kuka ba abunda take suko mamaki suke yadda har maganar lamunde ta tabbata tunaninsu wannan mutumin shine yayan lamunde chab chakwakiya aka Debi suhail sai asibiti nan aka Kira haleema aka sanar mata ko takalmi Babu akafarta Tama rasa meke Mata Dadi hankalinta yagama tashi daga wayannan sambala sambalan yammatan Kuma tare suke Duk da akwai kauyanci a tare dasu da kazanta da rashin wayewa faduwa tazo daidai da Zama anan aka kwantar da subai'a akayi Mata dinki agabanta aka Bata gado na sati biyu saboda tetenus yaso shiga wajen saboda kazanta da rashin kulawa su fadeela sun koma gidan anty saudat asibitin dama ba'a zaman jiyya haka suke zuwa suna dubasu

Suhail sai da ruwa leda yasha biyar Dan akwai karancin ruwa ajikinsa gaba daya shikansa beda lafiya saboda sauyin rayuwar daya samu kusan shekara guda satin sa daya sannan aka sallamosu Duk ya rame hankalinsa Duk a tashe yake wannan wane irin mutane ne masu yakanah haka Dame ze saka musu wannan alkahirin dasukai Masa beda bakin godiya agaresu gaba daya yanzu kunyarsu yakeji Sam ya kasa sakin jiki dasu mom ko gaba daya itama ta rame tare suke jiyyar

Haleema ko Ina aljanna ta shiga Amma abunda ke damunta dayane motsi kadan yace y jikin subai'a wacece itane gaba daya ta tsare gida ta kankane tana tare da shi har aka sallamo shi gaba daya sun hallara kwansu da kwarkwatarsu Banda subai'a dake gadon asibiti kowa ka kalla fuskarsa ba walwala Dan sun San wannan zaman bana lafiya bane alhaji ne yai gyaran murya suhail ka fahimceni zan fayyace maka wani boyayyen sirri Duk da mahaifiyar ka ta rokeni akan boye wannan Sirrin Amma bazan bi San zuciyarmu mu cutar da mahaifiyar ka tunda Allah ya nuna Mata Dan ta Duk da bamu da yakinin haka Amma idan har ba mahaifiyar ka bace ba abunda zesa harta furta haka tsakanin d`a da mahaifi sai Allah jini ba karya ba ya gyara Zama

Bayan na rasa ahalina gaba daya Wanda wannan wani sirrina ne Wanda ko matata Duk tsawon shekarun mu batasan takamai mai labarin ahalina ba Amma ta Soni a haka ta kaunaceni Banda abunda zan saka Mata anan gidan duniya bayan mun rabu da ahalina na fito titi a wannan lokacin ne narasa yadda zanyi Ina hawaye Ina komai ga tarin shanu da kudade dankar a tare Dani gashi hanyar Nan akwai yan fashi musamman dajin falgore gaba daya a tsorace nake cikin ikon Allah sai ga wata mota ta fyallo da gudu Nan na hau titi na dinga daga Masa hannu dakyar ya tsaya dayaga ze kadeni cike da tsoro ya dakan tsawa Kai Dan fashi ne ko ya zaro bindiga ya saita Ni na durkusa nasamasa kuka Ina cewa yatemaka min Banda kowa a garinnan hanya tabiyo damu an kashe iyayena da kanwata a cikin Daji ya tausaya min to Kai gaka da shanu yazanyi dakai da wayannan shanun Allah Kuma ya temakeka muna gab da gari Nan da Nan Naga yayi waya cikin minti talatin saiga wasu mutane da kakin sojoji yace maza su kada shanun zuwa garin falgore gidan Mai gari

Ni kuma yadaukeni mukaje falgoren gidan me garin yai Masa bayani aka saukeni haka kawai naji hankali na yafi kwanciya da wannan mutumin Ashe sojane babba me mukamin general Nan nace Inasan magana dashi muka kebe na nuna Masa tarin kudina shikansa ya tsorata dayaga wayannan kudaden yadauka kayana ne a buhun Ashe kudine tabbas kayi hankali meye sunan kane yace Ibrahim zan tafi daki zuwa garin Jos inda iyalina suke suna shagari quarters Dan haka zansan yadda za'ai da kudin kayi karatune eh nayi secondary a kauyenmu to Masha Allah zaka koma makaranta daga Nan sai asan yadda za'ai nai Masa godiya yace Dame gari ze tafi Dani ga amanar shanun Nan tunda sunfi dari ya kula dasu adinga kiwo dasu kudin nonon da Mai adinga sallamar masu kula dasu yai megari yaji dadin haka muka wuce barrack dinsu ta falgore daga da sassafe mukaiwa Jos tsinke Nan ya bude account yasa kudin akayimun takaddun sakandire kunsan yanayin kasar nan

Agurguje a hannunsa nasa mu komai na rayuwa harda matata yarsa ce shekarata ta farko a makaranta ya auran ita na samu buk a Kano Nan muka dawo tare yasiya mun gida da kudina ya siyamun company guda biyu ya bude mun manyan super market da manyan shaguna inda na zabi sunan mu na gado alhaji Ibrahim gadon kudi a kowane Abu Dana mallaka shekarar mu biyar da aure shiru ba batun haihuwa nagama karatuna lafiya ba Kama kasa na waye baza kuce wannan iro na kauyen burji bane wata ran munje duba baban hajiya ba lafiya mundawo dai dai wani daji motar mu ta tsaya ruwa ya Kare gashi ba gari kusa hakan yasa na tafi neman ruwa cikin dajin dake safiya ce Haka na kutsa daji sai Naga ruwa me mugun girma cikin farinciki na karasa nasa jarka na debo ruwan sainaji kukan jariri abun ya ban tsoro na saki robar zan zura da gudu sainaji kukan yai yawa dana matsa chan saina hango wani Abu kamar Dan karamin kwale kwale

Amma na ice nayi addu'oi na karasa sainaga jariri fari Sol dashi a cikin wanna abun ga ganyaye sun rufe shi da hanzari nasa kafata cikin ruwan na janyo shi ba komai a jikinsa ga ruwan ya Fara tabashi ko cibi be Fadi daga gani sabuwar haihuwane da hanzari na cire rigata nasashi na dakko abin dayake ciki na maida shi ciki na debo ruwana na ajiye shi a gefe na juya zan tafi ya Kara tsandarewa da kuka tausayinsa yasa banyi shawara ba na dakko shi hajiya harta gaji tafara biyi hanya muka hadu na Mika Mata jaririn Tai mamaki nai Mata bayanin komai tai hamdala a ranta Dane daga sama Allah ya bani muka daukeshi bako tsoro mun tsinci da a daji cikin ruwa muka dawo Kano lafiya muka kaishi asibi lafiyarsa kalau sai nemonea data kamashi Haka muka dinga rainonsa har ya girma mun sanarwa da iyayen ta sun amince Amma munce a gidan marayu muka dakko shi
Chapter 48 · 0% Book details