Sashe 9
Alwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Cike da tsananin damuwa na ce." Shikkenan Baba zan yi bincike a kansa, idan ya kwanta mini a rai sai a yi."
Ya ce." Hurumin bincike ba a hannunki yake ba, mun riga mun gama bincike a kansa. Mutumin nan sananne ne, Ubangidan Babanki Sule ne, kuma yana da rufin asiri da dattako, sai ki godewa Allah wannan karon ba ki yi jinkiri ba. kuma ya ba ki miji mai wadata, idan Allah Ya yi ma don ya ri'ke miki yaran ba wani abu ba ne a wurinsa tunda yana da hali."
Shiru na yi ban ce komai ba. Ya kama hanyar fita yana fad'in." Ba za mu bari wannan damar ta wuce mu ba, ni kuma ba zan zuba Ido na dinga ganinki a gida kina yi mini shige da fice ba."
Shimfid'a na gyarawa yaran ina ta nazarin yadda rayuwar duniya take kwatantawa da ni. Babanmu da d'an'uwansa suna hango wadatar Alhaji Muntari. Suna ganin idan na aure shi zan huta suma za su huta, ni kuma akwai abinda nake hange.
Tara saura na dare yaro ya shigo yana fad'in." Wai ana sallama da Amina."
Ummansu Hadiza ta yi caraf ta ce." To gata nan zuwa."
Na juya na dubi Yusi da yake bacci a shimfid'arsu har lokacin Kamalu bai shigo ba yana can wurin Ummansu Hadiza.
Hijabina na zura ba tare da wata kwalliya ko fesa turare ba nasa takalmana na fita.
Yana jingine a jikin motarsa babban mutum ne don zai yi shekarun Baba Sulen. Yana da ki'ba daidai misali da duhun fata Amma ba can ba. Ga dai tumbi nan ya ajiye irin na alhazawa. Yana sanye da shadda riga tazarce da hula a saman kansa. Hannunsa kuwa manyan wayoyi ne guda biyu.
Cikin nutsuwa na iske inda yake tsaye. Ya saki fuskarsa Yana kallona tare da furta." Allah Ya sa ba daga bacci aka tashe ki ba."
Na dube shi cikin tsanaki na ce." Bacci kuma karfe tara fa yanzu mun yini lafiya ya iyali." Ya gyara tsayuwa yana amsawa ya dora da cewa ." To ai ban sani ba ko kina da saurin bacci."
Shiru na yi ban ce komai ba. Sai ya cigaba da cewa." Malama Amina na ji dadin ganinki a yadda nake hasashe. Sule ya jima yana ba ni labarinki. Na farko ha'kurinki da tarbiyarki, wannan ya kara kwad'aita mini jin sha'awar auranki a raina, ina fatan zuciyarki ta aminta da ni, domin ni ba da wasa na shigo ba."
Ba tare da na dube shi ba na ce." Na gode sosai da yabo da fatan alheri, amma don Allah ka yi hakuri da abinda zan fada maka, wallahi ba zan iya aure yanzu ba sai nan da wasu shekaru tukkuna, idan ma Allah Ya 'kaddara ba zan sake wani auran ba hakan daidai ne a wurinsa. amma dai yanzu babu shi a lissafina ."
Ya gyara tsayuwarsa a karo na biyu ya fuskance ni sosai Ya ce." Wace hujja ce dake da za ki furta wannan maganar. Amina guda nawa ki ke da za ki jingine maganar aure, ki ce ba za ki yi ba sai nan da wasu shekaru. lokacin kin tsufa kenan, babu namijin da zai yi marmarinki, ai aure rahama ne kuma ni'ima ne ba don komai ba sai don idan sha'awarki ta tashi ki samu wanda zai kawar miki da ita. Wallahi a shirye nake da na aureki, kuma na kula dake yadda ya kamata, idan matsalar yaranki ne, zan ri'ke miki su, ai d'a na kowa ne, ni ma ina dasu a gida sai mu had'a mu ri'ke gabad'aya."
Ganin yadda ya rikice yana karyar da kai, da kalamai tausasa, sai jikina ya mutu. Na rasa abinda zan gaya masa domin ya gama kashe mini jiki, matsalata yarana kuma ya ce zai ri'ke mini su. A dan nazarin da na yi masa na hangi sona a tattare dashi. Kuma bai nuna 'kyama akan yarana ba kamar yadda wasu mazan suke yi idan suna son mace, sai su dinga k'yamar yaranta, suna nuna kishi, amma shi tashin farko ya amince zai ri'ke mini da alkawarin kula dasu kamar yaransa..
Jiki a sanyaye na ce." To na gode da nuna damuwarka, ina so ka ba ni lokaci zan yi shawara akan hakan, in sha Allahu duk abinda na yanke zan sanar da kai."
Ya ce." Wannan ba matsala ba ce, amma ina rokonki don Allah ki yi shawara da mutanan arziki, domin kada ki yi da baragurbi su rud'a ki,wallahi da gaske nake auranki zan yi Amina, kuma zan kula da yaranki."
Murmushi na yi na ce." In sha Allah, ni ba ni da k'awaye marasa tarbiya duk wad'anda nake mu'amula da su, sun san abinda suke yi, don haka kada ka damu."
Ya ce." Ki ba ni lambarki zuwa gobe da safe idan Allah Ya kaimu, zan kira ki domin na ji Ina aka kwana."
A nutse na fad'a masa lambar ya yi serving. Ya ce." Kin ga goma saura yanzu zan wuce gida, don Allah zuciyarki ta sa'ka miki alhari a kaina."
Na ce." In sha Allahu, a gaishe da iyali." Na juya da zummar shiga gida ya dakatar da ni. Kudi ya d'auko a aljihunsa ya
miko mini.
Na girgiza kaina ina fad'in." Na gode amma ba zan kar'ba ba."
Ya rausayar da kansa. " Don Allah ki kar'ba babu kyau mayar da hannun kyauta baya Amina, ki yarda da ni da alheri na zo miki."
Hannu nasa na kar'ba tare da furta" To na gode sosai, A gaishe da iyalin." Ya amsa yana bud'e motar. Ni kuma da sassarfa na shige gida gaba na bugawa kad'an-kad'an.
*1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank ko 7084653262...Binta Umar Opey bank*
*07084653262*
*What's app kawai*
[11/16, 10:40 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A.*
*TALLAH!*
Albishirinku mata Yan gayu yan gwalisa kuyi maza kugar zayo shagon
(Aysha/Addah beauty saloon and spa).
Shin kintaba zuwa ingancaccen saloon din Aysha/Addah, idan baki taba zuwa ba kiyi maza kar a barki a baya domin sun qware a wajen aikinsu Wanda suke services dinsu cikin sauki tare da annasuwa
Suna wanke kai(wash and set)
suna wanke qafa(pedicure)
And sunayin steaming iri iri suna saida (supplements)suna kitso dama duk wani abu daku so Wanda akewa mace ta amsa sunanta mace yar qwalisa
Address dinsu nanan a Federal low-cost opposite open University gombe state
Ko kuma ku tuntune mu a wannan number kamar haka,
08037925676
Or
08167764242
Whatsapp ko kuma Call we’r available 24/7..