Sashe 23
Alwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Na gode sosai Alhaji Allah Ya 'kara arziki."
"Amin Ya Allah, zan shigo yau da daddare sai mu sake tattaunawa ko?"
"To shikkenan, Allah Ya kawo ka lafiya."
Muna yin sallama da minti biyar message ya shigo a waya. Ina dubawa naga kudi ne ya turo mini har dubu dari da hamsin. Ban yi mamaki ba, tunda tun farkon haduwarmu ya nuna yana da kyauta da sakin hannu.
Wani abin haushi da takaici, Ummansu Hadiza kuma sai ta tsiri jin haushina. Da farko duk abinda zan zartar sai na nemi shawararta amma ganin yadda ta fara nuna halin ko'in kula da lamarin auran ya sanya na janye jikina. Nake gabatar da abubuwana kai tsaye tunda ni ba yarinya ba ce. Abinda dai yake ba ni mamaki shine; Yadda take nuna mini hassada a duk abin alherin da zai tunkaro ni. Da farko ta nuna sha'awarta da lamarin, amma ganin yadda komai yake tafiya gwanin sha'awa sai bakinciki ya shigo ciki. Hadiza ta zo gidan tana fad'in "Dukda dai ba sanya mu a sha'anin ba, muna da abinda fad'a, mutumin nan dai bashi da wani kuzari a gidansa, matansa sun fi karfinsa, sannan kuma Yana neman mata, kowa ya san haka don har ciki ya yi wa wata yarinya, don dai yana da kudi ne maganar ta mutu."
Ban girgiza ba, ban kuma tanka mata ba. Na cigaba da shirye-shirye na, ina kara mi'ka wa Allah lamarin, gefe guda Gwaggo tana kara kwantar mini da hankali da fatan alheri. Duk wani gyara na yi, na ciki da waje. Na sayi abubuwan da ba ni dasu. Domin da kansa ya dinga gaya mini idan kudin ba su isheni ba na yi masa magana zai kara mini. A iya tunanina dubu dari da hamsin da ya turo mini harda lefe, abin mamaki sai gashi saura kwana biyar d'aurin aure danginsa sun kawo mini akwatina uku cike da kaya manya da takalma da mayafai, wallahi ko wata budurwar albarka.
Takaici ya kara cunkushe zuciyoyin massadana. Ita Ummansu Hadiza bakincikinta a kaina baya b:oyuwa, amma anti Sakina watsar da makamanta ta yi ta zo har dakina tana gaya mini idan na tashi fitar da kayan da zan bayar tana buk'ata. Na ce mata in sha Allahu zan zabar mata masu kyau.
Ana jibi d'aurin aure, anti Yagana da Ya Falmata suka dira. Kaya sosai suka had'o mini na gyara
dana sanyawa. Na yi farincikin zuwansu ba kad'an ba, domin dama kad'aici ya isheni. Sune suka je suka ga d'akin da zan zauna a unguwar Kawo Jirga. Su ka dawo suna 'kwarzanta gidan, da kuma sakin fuskar da suka samu daga matan gidan..
Hakan ya kara kwantar mini da hankali, na ajiye a raina in sha Allah zan yi iya iyawata wurin ganin na zauna dasu lafiya, zan kuma toshe kunnena daga barin jin gutsiri tsoma na jama'a..
Aka daura aure ranar juma'a, shedu suka shaida, kuma a ranar na tare a gidan. Inda na samu rakiyarsu Anti Yagana da Ya Falmata Sahura da kuma Anti Sakina.
Ummansu Hadiza ita da yaranta babu wanda ya raka ni. Ita a ranar ma kwanciya ta yi a d'aki ta ce zazzabi take yi.
Hadiza kuwa dama sai Yamma ta zo, Fati kuma tsohon cikine da ita ba ta fita, Hassana da Usaina kuma sam ba su zo ba, na fi zargin ba ta gaya musu ba, amma da ko Hassana ba ta zo ba, na tabbata Usaina zata zo, tunda muna shiri da ita.
A ranar da na tare na d'auka zai tattaramu wuri d'aya ya yi mana nasiha, sai na ga akasin haka. Bai yi wannan ba, gabad'aya ya d'okantu sai barin jiki yake yi. Ya manta da sunnar da annabi ya koyarwa sabbin ma'aurata. Na gaza yin shiru na tunasar dashi akwai sallar nafila fa, mu yi da kyakykyawar niyyar domin wanzuwar farinciki a cikin auranmu.
Kamar dai wanda na tilasta haka ya bi ra'ayina da yadda nake so, muka yi nafilar. Ina ta nazartarsa a tsanake na fara hangar wasu halayensa. Wato kowa dai ka ganshi kawai. Dama ana fad'in yawanci maza suna auran sha'awa ne, masu yi don Allah kad'an ne, na fara gazgata haka a dare daya da Alhaji Muntari, amma ba zan yanke hukunci kai tsaye a kansa ba tukkuna sai tafiya ta mi'ka. Yadda dai ya nuna zulamarsa a kaina shine abinda ya fi daure mini Kai, tamkar wanda bai da iyali haka ya kasance da ni a daran, ya gudanar da sha'aninsa, cikin nishadi da sambatu kala-kala.
Muka wayi gari cikin aminci. Amma har yanzu ban daina mamaki a kansa ba. Da Ya tambaye ni Yara na ce "
Suna can gidan kakarsu sai na yi sati tukkuna za a kawo su."
Sai Ya ce ." To Hakan ba lefi, kema kin yi kyawun kai, na gama morewa ko?"
Na yi murmushi ban ce masa komai ba. Ya ce." Za ki shiga ku gaisa da matan gidan hakan ya yi ko?"
Na dube shi a tsanaki na ce." Ai na d'auka kai za ka yi mini iso a wurinsu mu gaisa sosai, idan da wani karin bayani a kaina da kansu sai ka yi mana."
Ya girgiza kansa yana furta." A'a, ki je dai ku gaisa, ai kina fita kowacce ga kofarta nan. Ku dai zauna lafiya don Allah, ki ba su girmansu, tunda su ki ka samu a gidan, ki bi tsarinsu, muddin babu cutarwa. Suma na yi musu bayani akanki, ba ki da matsala, abinda dai na sani kansu a had'e yake, haka zalika ma yaransu, idan kin bi su a yadda suke so, za ku zauna lafiya da juna."
Na jima Ina kallonsa da kuma nazartar maganarsa. Ai idan da wanda zan bi sau da k'afa shine, tunda shi ya ajiye ni, banga dalilin da zai sanya ace mini na bi wata ba, zaman aure ai ba wasa ba ne.
Amma ban nuna masa damuwata akan maganarsa ba na ce." Babu matsala zan shiga mu gaisa da su zuwa an jima, amma wani hanzari ba gudu ba, wallahi abubuwa sun sha mini kai, tun farkon had'uwarmu nake so mu yi maganar da kai, Allah Bai nufa, amma wata'kila Baba Sule ya gaya maka Ina aiki ko? Ina koyarwa gwale firamare skull, sannan ina dinki sosai, ina so na cigaba daga inda na tsaya, ba don komai ba sai don kula da yarana, ba zai yiwu duk wahalarsu na sakar maka ba, ni ma zan taimaka da wani abun."
Fuskarsa ta canza da wani yanayi da ban ta'ba ganinsa a ciki ba. Ya gyara zama Yana fuskatantata sosai Ya ce, "A gaskiya bai gaya mini ba, kuma kema kin yi ragwan azancin da ba ki sanar da ni ba tun farko ai da na fada miki ra'ayina, ba zan iya bari iyalina na fita aiki ba, bayan Allah ya yi mini komai, ba ni da wannan tsarin."
Gabana na wani irin fad'uwa na zuba masa ido, Ina tunanin yadda zan yi don wallahi ban ta'ba tsammanin zan samu matsala a wurinsa ba.
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Ki ajiye maganar zuwa aiki Amina, babu ita a tsarina, sai dai ba zan katseki ba, adalci daya zan yi miki, ki cigaba da dinkinki, a cikin gida, ai aure ba wasa ba ne, da zan fita matata itama ta fita tana cud'anya da maza a waje, ba mu ta so da wannan akid'ar a gidanmu ba. Matayenmu suna gida a lullube mu ne muke fita mu nemo musu abinda za su ci, maganar yaranki kuma, ni na ce zan ri'ke su ai, kada ki damu zan miki kokari a kansu, a marayu ne, wata'kila sai na samu aljanna ta dalilinsu, in sha Allahu zan kula miki da su.......✍️
*1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank*
*07084653262*
[11/24, 9:34 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*
*TALLAH!*
🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨
🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi
https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t