← Book details Alwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 35

Sashe 28

Alwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba ka fahimta ba, zan samu wadda za ta taya ni aiki ne ranar girkina, tunda kun ce yara suna makara a makaranta, kai ma baka samun kulawa daga wurina, shiyasa na yi wannan shawarar."
"Ban yadda ba."
Ya fada hankalinsa yana kan wayarsa. Shiru wurin ya yi gabad'aya raina ya gama baci da abinda yake yi mini. Ya ce." Sai dai ki dauko wata daga cikin yaran dangi, zan yi miki wannan alfarmar. Amma ban yadda da d'auko mai aiki ba, bayan kuna da ita, na gaya miki babu wani tsari da za ki zo dashi da zumar rusa mini zaman lafiyar gida."

Ya tashi ya kama hanyar fita ba tare da saurari abinda zan ce ba. Yadda na fahimce shi ya fi tsoron Jamila fiye da anti Maimuna, ko meye dalilin haka oho! ko da yake 'yar kauye ce ai, Allah kadai ya san irin surkullen da take yi a gidan.
Gabad'aya sai ya jefa ni a cikin tunani. Ba yarinyar da zan je na nemi alfarmar iyayenta su ba ni kai tsaye sai Yusura yarinyar Sahura. To kuma idan na yi hakan ban yi wa kawata adalci ba, itama tana zuwa aiki, kuma yarinyar itace take d'awainiya da 'kananta tunda ta yi wayo.
Na yini ina nazarin yadda zan yi, domin fa zahiri idan ba mai'aikin nan na samu ba abubuwan ba za su gyaru ba, ni kuma ba zan fasa neman kudina ba, gashi daga farawa ta zuwa yanzu na samu kudi sun kai dubu dari biyu da hamsin, babu yadda za a yi na yi watsi da wannan damar da Allah Ya kawo mini, dole na yi wa marayun yarana digin da zasu amfana a gaba, ubansu bai bar musu komai ba.
Da yamma bayan la'asar yara duk suna makaranta, ina kan keke Sahura ta yi sallama. Cike da farinciki na tare ta. Ina fad'in." Wallahi yau yini na yi da tunaninki."
Ta zauna kan kujera tana cewa." Sai gashi Allah Ya kawo ni, daga aiki nake sai kawai na ce bari na karaso mu gaisa, kin san babu wata nisa fa tsakanin nan da wurin aikin na mu."
Na ce." Aikuwa kin kyauta mini wallahi bari na kawo miki ruwa.

Na kawo mata ruwa da d'an snacks da lemo na zauna ina fad'in." Me zan girka miki, na san kina tattare da yunwa daga ganinki."

"Wallahi a koshe nake, ai ba daga wurin aikin nake kai tsaye ba, mun je can gidan ogan mun duba mahaifiyarsa bata da lafiya, yau kwana biyu kenan da dawowarta daga egypt ganin likita, shine fa muke tattara mukaje dubata, mun ci mun sha ba na tare da yunwa."
Na ce." Ayya, to ko ruwa ai kya sha Sahura." Ta d'auki d'aya ta kai bakinta tana fad'in."To shikkenan."
Bayan ta ajiye ragowar ruwan na dubeta a nutse na ce." Sahura ya aikin fatan komai lafiya, na ga fa kin yi kumatu, ko ya yi muku karin albashi ne ."

Sai ta fashe da dariya tana cewa." Muna sa rai dai 'kawata, kin san ma na nemi alfarma a wurinsa za a mayar da ni daya daga cikin kamfanoninsa dake kusa da mu, saboda kafin na je Ina makara gaskiya, to da ya tambayi dalili sai na gaya masa, na kuma nemi alfarma."

Na ce." Hakan zai fi miki gaskiya, to Ina yi miki fatan alheri kawata, Allah Ya hadamu da rabonmu na alheri ."

Ta amsa da Amin tana bin falon da kallo. Ta ce." Su Kamalu suna makaranta kenan?"
"Suna makaranta wallahi, kin san wani abu kuwa?"
Ta girgiza kanta tare da mayar da hankalinta gare ni.

"Alfarma nake nema a wurinki, ban sani ba ko Idiris zai amince buk'atar tawa dai ta wucin gadi ce, idan ma zan samu a ba ni duka har aure zan fi son hakan."

"Wace alfarma ce wannan ki fad'a kai tsaye muddin Ina da iko, zan yi miki ai mun zama daya."
Yadda ta fadi maganar da karsashi, shine ya bani kwarin guiwar fayyace mata halin da nake ciki. Na d'ora da cewa." Sai kuma na yi tunanin yarinyar tana taimaka miki kema, sannan tana kula da 'yan'uwanta a duk lokacin da ki ka tafi aiki, shine dalilin da ya sanya na janye maganar a zuciyata."
Murmushi ta yi tare da dafa kafad'ata ta ce." Ki daina fad'in haka, idan ta ni ce yau ma Yusura ta dawo hannunki, ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, na san za ki kula mini da ita, maganar kula da gida da yara kuma, ba ki ji Ina gaya miki cewa wurin aiki za su dawo da ni kusa da gida ba, ai kin yi maganar akan ga'ba in sha Allahu kuma Abbansu ba zai k'i amincewa ba."
Ajiyar zuciya na sauke mai sanyi na ce." Na gode kwarai da wannan karamcin kawata, in sha Allahu duk sabgar makarantarta zan yi mata kokari sai ta dora daga inda ta tsaya tunda akwai makarantu anan din."
Ta nisa tana kallona." Kina ganin dai babu matsala a wurin abokanan zamanki ko?"

"Babu wata matsala Sahura, ai tunda maigidan ya amince magana ta kare, Jamila ce matsalar gidan itama na san inda zan yi da ita.

Ta sauke ajiyar zuciya a nutse ta ce.'" in sha Allahu rabbi ina komawa gida zan sanar da Abbansu duk yadda muka yi za ki ji ni a waya."
Na ce." To shikkenan, ina godiya k'warai, Allah Ya bar mana zumunci."

To cikin ikon Allah ba a sha wata wahala ba a wurin Idiris ba ya amince. Sahura ta kira ni a waya tana gaya mini na tura a d'auko yarinyar domin babanta ya amince tare da tabbatar mini da cewa ya yi farincikin hakan saboda shedar da ya yi mini yana da tabbacin yarinyarsa za ta samu ingantaciyar rayuwa."

Na ji dadin dawowar Yusura hannuna. Dama tun fil'azal yarinyar ta horu da aiki, shekararta goma sha hudu ta iya komai, sai dai ba duka nake sakar mata aikin ba, ina sanya mata hannu saboda yawan aikin ba irin wanda take yi ba ne a gidansu, na nan da yawansa. Ranakun da ba ni da girki kuwa, idan na fita na gaisa da matan gidan na koma wurina ba na sake fitowa, za mu dukufa aiki ni da yaran gabad'aya, lokacin makaranta da sallah ne yake tashinmu.
Kafin ki ce kwabo al'amurana sun 'bunkusa, duk sati sai na hada bacco na kaya sama da set talatin an kai Maiduguri. Tun ina lissafin dubu dari biyu uku hudu a cikin acct dina, sai na dawo lissafin miliyan. Al'amarin ya dinga ba ni tsoro da mamaki. Sai kawai na ajiye a raina cewa 'Allah ba yadda ba ya shirya lamarinsa'

Ranar da muka wayi gari da Azimi na farko. Baba Sule ya dira a gidan. Dama ya kan zo sa'i da lokaci da matsalarsa na d'auki kudi na bashi. Wannan karan kuma da buk'atar na saya masa kayan abinci ya zo, saboda wai Usaini ya gaya masa harkokina sun bud'e yanzu, gashi babu abinda na nema a gidan aurena, tunda dai kowa ya sheda gidan Alhaji Muntari da kulawa ta fanni abinci da suttura babu yunwa. A cewarsa neman da nake yi sai na wahalta musu tunda suna raye sai na samu lada."
Na riga na san son zuciyarsa sarai, idan ba haka ba mai zai sanya ya dinga zuwa yana cewa na bashi kudi, har binciken halin da nake ciki yake yi. Na dube shi a tsanake na ce." Baba ka koma gida in sha Allahu zan aiko muku da kayan abinci kai da Babanmu dama na yi niyyar hakan, amma don Allah ka dan rage zuwa, tunda ka ga ba ni kadai ba ce a gidan ina da kishiyoyi kada hakan ya janyo mini matsala."
Ya ce." To, zan rage zuwa idan kin san abinda ya dace, ni dana had'a auranki da Alhaji Muntari ai kamata ya yi ace ina da kaso a wurinki, amma sai na ro'ka k'i, ki dinga tunani"

Na ce." Ni fa ba wani abin nake samu da mutumin nan ba Baba, don Allah ka daina wannan maganar, duk alherin da nake yi muku daga aljihuna yake fitowa, saboda haka don Allah ka d'auke 'kafarka ba na so wani ya ta'ba muku mutumcinku."

Da kyar na rarrashe ya kama hanya ya tafi bayan na d'auki dubu biyar na bashi a matsayin kudin mota. Kwana biyar da zuwansa na gama had'a komai. Sai na fara tunanin yadda za a yi a fita da kayan domin kuwa matan gidan za su iya zargin na mijinsu ne na d'iba tunda yana ajiyesu da yawa. Da daddare aka shigo mini dasu lokacin kowacce tana wurinta, sai na yanke shawarar kawai a fitar dasu da daddare. Na kira Usaini a waya na gaya masa ya zo da adaidaita sahu ya d'auka kowa ya kai masa, na dora musu dubu talatin talatin akai.

Cikin rashin sa'a, lokacin da Usaini ya zo d'aukar kayan maigidan yana nan, tare da abokanansa a waje dama suna zaman shan ruwa idan sun yi asham sai su watse, abinda na cewa Usaini kenan bayan sallar asham zai zo. Minti goma da fitar Usaini ya shigo d'akin Muna zaune da yara gabad'aya a falo, ina yanka wasu riguna su kuma suna kallon tibi. Ya zauna kan kujera, suka dinga jera masa sannu da shan ruwa, ya amsa a takaice. Na daga kaina na dube shi. Babu fara'a, a fuskarsa, zaman da ya yi ya nuna yana buk'atar magana da ni, ga kuma yara.
Na dubi Yusura a nutse na ce." Ku je d'aki ku yi kallon a can tunda da tibi. Suka tashi da saurin na ajiye almakashin hannuna. Na ce."Barka da shan ruwa."
Ya dube ni. "Barka dai, wanene yanzu ya fita da buhunhunan shinkafa da su taliya?"
"Usaini ne k'anina su Baba na sayawa."
Ya zuba mini ido na minti daya kafin ya ce." A ina ki ka ga kudin sayan wad'annan kayan abincin Amina, rankatakaf fa komai akwai kayan sun tassama dubu dari uku a yadda rayuwar nan take tsada."
Chapter 28 · 0% Book details