Sashe 33
Alwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Anti Maimuna ta ce." Da alama an samu maslaha sai dai yadda na ganka a sa'bule kamar akwai matsala."
Ya ce." Matsala babba ma kuwa." Sai ruwan hawaye ya ciko kwarmin idonsa.
Na ce." An gano wanda ya aikata kenan?"
Kai tsaye Ya ce." Turmuzi ne!"
Gabad'aya muka shiga gigita! hawayen da ya ciko kwarmin idonsa ya zuba a kumatunsa. Ya nisa kafin ya yakice kuttun takaicin da yake sasakarsa ya ce." Yaron nan Yusi bashi alhaki kuma dukan da jami'an nan suka yi masa sai Allah Ya saka masa, abinda ya faru shine; Wato rud'u da firgice da kuma tsoratarwa ya sanya yarinyar nan fad'in Yusi ne yake cire mata wando. Amma a zahiri Turmuzi ne, tun farkon fara shigowarta wasa gidan nan yake janta bayan korodo yana cire mata wando ya bata alawa. Mahaifin yarinyar shi ya yi mata wayo da daburu ya lallabata kan ta gaya masa wanene tana kuka tace Turmuzi ne ya ce duk wanda ta gayawa sai ya kasheta. Ya kunna mata wani film yana nuna mata irin kisan da zai yi mata da wuka.
A ranar da ya cire mata wandon ya danneta." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! sai kawai ya fashe da kuka yana girgiza kansa, tabbacin abin yana susar zuciyarsa.
"Yaushe Turmuzi ya lalace haka, yaushe ya balaga da zai iya haikewa yarinyar mutane. Shekara sha hudu me ya sani, a cikin gidana, ni ban kasance mazinaci ba, Allah kada ka jarrabe ni."
Babban mutum Yana kuka tukuru!"
Gabad'aya jikinmu ya yi sanyi. Kudirin da yi na d'aukar fansa akan haka na janye ganin irin gigitar da ya shiga.
Anti Maimuna ta ce." Yanzu a wace matsayar aka tsaya?"
Yasa hankice ya share fuskarsa." Maganar ta mutu, mahaifin yarinyar ya janye karar da ya yi. Yanzu sun kaita asibiti an duba wurin raunin kad'an ne, yarinyar ta yi bayani bayan gabansa da yake sa mata har hannu yana sa mata a wurin."
Na sunkuyar da kaina k'asa kawai sai wasu hawaye masu rad'adi suka goce mini suka dinga fafara gudu a kumatuna. Yaushe rabon da na yi kuka irin wannan har na manta. Ba komai ne yake daga mini hankali ba yadda tarbiyar yaran k'ananu take nema ta gurbace. Wai kamar Turmuzi shekara sha hudu shine da aikata wannan lamari.
Sai na ji anti Maimuna tana fad'in." Ban yi mamaki ba, dalili wayar da take hannun yaron babu abinda ba zata janyo ba. Tuntuni na gayawa Jamila cewa ta kwace wayar bata da amfani tunda ba aikin karatu yake yi da ita kallace kallace yake yi da, ya yaudareta ne kawai ya ce ta siya masa zata dinga taimaka masa bangaran karatunsa. A gabana akayi hakan, kuma ta saya masa. Na tabbata idan ka bincike wayar ba za a rasa fina finan banza ba, domin wasu lokotun idan ya shigo wurina Yana kallo baya barin kowa ya zo wurin da yake. Ya kan rage murya ko ya sanya airpix a kunnansa."
Fad'a sosai ya shiga yi, domin shi duk abinda ake yi bai san yaron yana da waya ba, uwar bata gaya masa ba a lokacin da zata saya masa sai lefin ma yake ko'karin shafar anti Maimuna. Ana haka Jamila ta shigo. Ganinmu a hargitse ya sanya ta dan yi sanyi tana fad'in." Yanzu nan na ga yaron nan Yusi nace ashe an samu maslaha sun ba dashi kenan."
Lokacin da take maganar hankalinta yana kan maigidan. Aikuwa tana rufe baki ya fara bata amsa, ya warwarewa mata zare da a bawa, har da barazanar saki muddin ta cigaba da yin abu ba tare da saninsa ba, domin ya tabbata wayar ta taka muhimiyar rawa wurin lalacewar yaron.
Bata yarda ba don kuka ta fashe dashi tana fad'in an yi wa yaronta 'kage, wallahi ba zata yarda ba sai ta d'auki mataki. Ya kuwace sai dai ta d'auka a gidan ubanta domin idan tace zata yi wani yun'kuri na fitar da maganar sai ya sake ta.
Jin haka yasa ta fita tana kuka. Ya tashi ya bi bayanta. Can muka dinga jin hayaniya a wurinta da kururuwar Turmuzi
Gabad'aya muka nufi wurin. Ya samu narkeken itace yana dukansa dashi. Duk ya fasa masa hanci. Wahala ta sanya yaron fad'in shine ya aikata amma ba zai kara ba. Da kyar na kwace itacen hannunsa ita kuma anti Maimuna ta rirri'ke shi. Lokacin ne Jamilar ta dadi a wurin tana wani irin abu wanda ya tabbatar mana da cewa aljanune suka buge ta. Maigidan bai tsaya ba ya kama hanya ya fice da wayar da ya kar'ba a hannun yaron. Ni da anti Maimuna muka tsaya a kanta da tofi da addu'a har suka saketa bacci ya d'auketa.
Lokacin da muka fito na kalli Anti Maimuna cikin sanyin jiki na ce." Dama anti Jamila tana da aljan u?
Ta ce." Tana dasu amma ba koyaushe suke tashi ba, sun fi zuwa yayin murna ko bakinciki idan ta haihu ma haka suke tashi akai akai har sai an yi suna."
Na girgiza kai ina mamaki, tabbas hakan zata iya faruwa idan aka yi duba da yanayin halayyarta. A hargitse take koyaushe kuma bata da yarda gata da mugun izza da girman kan tsiya.
Sai bayan sallar isha'i tukkuna hankalina ya daidaita.
Yusi ya shigo ya zauna kusa dani jikinsa duk a sa'bule. Na dube shi a tsanake na ce." Ka je massalacin ko?"
Ya daga kansa alamun "E, sai ya ce." Mama ina Yayana yake? yanzu ina fitowa daga massalaci na ji wasu suna cewa 'yansanda sun kama shi saboda ya zage su."
Na ce." Yana can gidan Gwaggwo k'arya suke yi yanzu nan zan kira Hamusu a waya ya kawo shi gida.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin jikinsa. Na dau'ki wayata da sauri number Hamusu na nema.
Ya daga muka gaisa Yana tambayata ya ake ciki.
Na ce." Hamusu komai ya zo da sau'ki ga Yusi a gabana tun d'azu suka ba dashi saboda gaskiya ta bayyana kanta."
Ajiyar zuciya ya sauke yana godewa Allah kafin ya cigaba da cewa." Yanzu dai an kama wanda ya aikata ko?" Na ce." E, ana kan binkice dai."
Ba na so na fad'a masa yaron gidan nan ne, yin hakan kamar tozarta maigidan ne, kuma na ji dadi sosai da tsayuwar da ya yi akan sha'anin har gaskiya ta bayyana.
Na ce." Don Allah tunda kana da abin hawa ka kawo mini Kamalu akan babur d'inka kada ka bari ya taho da kansa, dama akwai maganar da nake so mu tattauna dangane da bud'e shagunan da zan yi."
Ya ce." A a, Kamalu ai baya nan, tun lokacin da ya zo ya gaya mini abinda yake faruwa ban sake ganinsa ba, bai dawo gidan ba ne?"
Cikin faduwar gaba na ce." Bai dawo ba wallahi, amma don Allah yi maza ka duba gidanmu ko yana can."
Da sauri ya kashe wayar.
Yusi ya dube ni." Mama ya akayi, ina yayan nawa?"
Cike da fargaba na ce." Yana can gidanmu, yanzu Kawunku zai je ya d'auko shi."
Ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na biyu. Ina nan zaune ina sakawa da kwancewa. Hamusu ya kira ni yana tabbatar mini da cewa Kamalu baya can gidanmu.
Na ce." Ka ga Saminu a gidan kuma?"
Ya ce." Kwarai kuwa shine ma ya tabbatar mini da cewa baya nan, don koda sallah bai je musu ziyara ba.
Jikina ya shika, sai fargaba ta yi mini sallama, da ban kawo komai ba a zuciyata, amma yanzu babu irin tunanin da ba na yi. Na ce." Hamusu bari na yi magana da maigidana yanzu zan kira ka zuwa an jima.
Na kashe wayar da sauri na tashi na fita zuwa d'akin maigidan tunda ba girkina ba ne, Yusi ya biyo bayana da sauri yana kuka....✍️
*Gudun aure 1k on talgram via 0542382124....Binta Umar gtbank mutanan nijar dala dari katin Airtel a kankare a tura mini shaida ta wannan lambar*
*07084653262*