← Book details Alwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 35

Sashe 22

Alwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*@Arewa books*
*Bintuumarabbale*
*Ga wad'anda ba su san jira akwai more peges a arewa na gode🙏*
*Free pege*
*14*
Hamusu ne ya yi duk abinda ya kamata akan rauninkan dake jikin Kamalu. Abdullahi mai chamis ya zo ya duba shi sosai, ya bashi maganin da ya dace. Sannan ya bi bayansa yana tambayarsa abinda za a ba shi.
Da k'yar na lallab'i Yusi ya shirya ya tafi makaranta. Babanmu ya leko yana fad'in." Ina Kamalun yake ne, ban ji motsinsa ba."
Na ce." Gashi nan, a kwance yana bacci, Abdullahi ne ya ba shi magani.
Ya shigo d'akin sosai yana duba kafartasa. Ya girgiza kansa babu kuzari a tare dashi ya furta." Allah Ya taikaita muku wahala."
Na amsa da "Amin Ya Allah."
Ya dube ni kafin ya ce." Maganarki da Alhaji Muntari tana nan ko?"
Kai na d'aga a hankali na ce." E, Baba." Sai ya kama hanyar fita yana fad'in." Allah Ya tabbatar miki da alheri."
Na amsa da "Amin." Cikin sanyin jiki.
Ummansu Hadiza ta le'ko ta duba jikin Kamalu, mun d'an jima da ita muna tattaunawa kafin ta fita daga d'akin. Na dinga zuba Ido ko zan ga Anti Sakina ta le'ko, ta duba shi, tunda dai ta san bashi da lafiya, amma shiru ba ta le'ko ba, kuma ina jin kayaniyarta da yaranta a tsakargida.
Na nemi wayar Sahura domin tunda na rakata neman aiki ba mu sake had'uwa ba, ko a waya.
Tana d'agawa take fad'in." Kina raina wallahi sis, kuma yau nake cewa zan kira ki kwana biyu network Yana yi mana wahala a unguwarmu."
Na ce." 'Kwarai kuwa, kuna da matsalar network a nan wuraran, ya gida, da yara?"
"Wallahi duk suna lafiya, ina su Kamalu fatan kowa lafiya."
Na ce." Alhamdullahi wallahi, kin ga har na je bikin Babandi na dawo, anti Yagana tana gaisheki da kyau."
"Ina amsawa wallahi, ina son zuwa garin nan k'awata."
Na ce." Sai ki bari idan auran Fadila ya tashi sai ki je."
Dariya ta yi tana fad'in." Ubangiji Allah Ya nuna mana, ai kaya ma zamu had'a ni da Yara mu je mu cashe da biki."
Dariya na yi, a hankali na ce." Sahura aure zan yi nan da sati biyu masu zuwa."
Da mad'aukakin mamaki a tare da ita ta furta "Aure sis!"
Na ce." E, wallahi Sahura."
"To ya aka yi ki ka canza shawara da gaggawa haka, wanene wannan da lokaci guda ya canza ki?"
"Ba wani ba ne Sahura Alhaji Muntari ne dai
wanda na baki labarinsa ranar da na zo gidanki...... Gabad'aya na kwashe duk abubuwann da suka faru na gaya mata, domin bahaushe yana cewa 'Abokin kuka shi ake fadawa mutuwa'
A sanyaye ta ce." Sis, kin yi bincike sosai a kansa ko? Ni fa ba na son irin wannan gaggawar a sha'anin aure Amina, ki nutsu don Allah, kada wata matsalar ta sanya ki jefa rayuwarki cikin garari, na tsorata da na ji kin ce matansa biyu yaransa takwas, ba ki hango matsala ba."

"Sahura ya zan yi? wallahi kaina ya kulle gabad'aya, gida sun takura mini, Kamalu Yana nema ya fi 'karfina, wannan ce kawai mafita a gare ni. Idan na ce ba zan yi aure ba, zan je na kama haya na zauna jama'a su canza mini manufa, ya zanyi ne Sahura, dole ko ba na so na amincewa mutumin nan domin na rufawa kaina asiri, yadda ya nuna alama kamar akwai nagarta a tare dashi, da bakinsa ya furta zai ri'ke mini yarana ba ni ce na nema ba, shiyasa na amince da auransa."

"To, shikkenan sis, amma don Allah ki tsananta da addu'a akan lamarin, Ubangiji Allah Ya tabbatar miki da alheri, Allah Ya sa abinda muke hasashe a kan mutumin ya tabbata."
Na ce." Amin Ya Allah Sahura na gode sosai, in sha Allahu ai kafin d'aurin auran zan zo mu tattauna."
"To Allah Ya nufe ki, sai ki zo ranar da ba aiki, mu yini muna hira."
Na yi dariya tare da ce wa." Sahura Ya aikin kuwa? Ina fatan babu wata matsala."
"Wallahi babu matsala, ai na gaya miki na fara a sa'a, sati daya da fara zuwana ma'aikatar ya yi mana rabon kayan abinci. Harda kudin cefane.
Na ce." A lallai, ma sha Allah, na taya ki murna, Allah Ya sa a d'ore."
Na fad'a cikin barkwanci.
Tana dariya ta ce." Za a dore in sha Allahu rabbi, ai kamar yadda ya gaya mana idan mun bi dokokinsa, zai kyautata mana, wallahi akwai alamun tausayi a tare dashi, shiyasa nake ko'karin ganin ban sa'ba dokokin aikinsa ba."
"Ai kam Sahura ba girin-girin ba, Inji hausawa ta yi mai, Alhaji Tajo ne fa, ni dai ba na yinsa, tunda ya yi sanadin uban 'ya'yana."
Ta dinga kyalkyala dariya tana fad'in." Ho 'kawata, idan ki ka tsani abu, duk inda makusa take sai kin nemo, wallahi mutumin arziki ne, ga kyauta da sakin fuska ga ma'aikatansa."
Na ce." To a ba ni hakkin mijina kawai a zauna lafiya, shekara kusan goma yana yi masa bauta, ai ya ci ya bashi fansho."

Ta ce." A rigimarki ba, ai ko gomnati ce sai mutum ya zartar shekara goma suke biyan fansho da garatuti, balle kamfani da babu wannan yarjejrniyar. Amina nifa na fi zargin akwai wad'anda suke cin amanar mutumin nan a bayan fage shiyasa ki ke ganin kamar bashi da Imani."
Na ce." Ai duk wanda yake aiki a k'arkashinsa ba zai ga aibunsa, mussaman idan Ya na amfanuwa dashi, shiyasa idan na fadi abinda ya yi mana sai jama'a su karyata ni, ke dai kin sani, ba sharri ba ne ko?"
Ta ce." Na sani, shiyasa ma ai ki ka ji na ce miki akwai masu ha'intarsa a bayan fage, wallahi na san da saninsa ba zai wulakanta wanda yake moruwa dashi ba."
Na ce." Lallai Sahura harda rantsewa akan mutumin da ba ki jima da saninsa ba, to shikkenan mu bar maganar kawai, ba za ki fahimta ba ai."

"Ai dole mu barta sis, tunda ba kya so, amma dai Ina kara tabbatar miki da nagartar mutumin, idan mu'amula ta had'aku, za ki gazgata cance na."
"Uhm" Kawai na ce' "Kin ga gyaran jiki, nake so na fara tun yanzu, bahaushe ya ce' Idan kana da kyau ka kara da wanka, dukda breast dina ba sa samu wata babbar matsala ba, amma dai Yana da kyau na kara gyarasu, a cike suke sai dai sun dan rankwafa, nan ba sosai ba, Ina so ki bincika mini maganin gyaran nono mai kyau, dana sanyi, da na'ima, ina buk'atar na matsi sadidan, amma harbel nake so, ba na buk'atar na bature."

"Aikuwa gyaran Yana da kyau kawata, don ma Allah ya yi mini kyawun suffa, wallahi da yawa wasu ba za su yarda kece ki ka haifi su Kamalu ba, kamar wata budurwa fa."
Dariya na yi na ce. Lallai Sahura, ke ma abinda za ki fad'a kenan, to na gode sosai, dukda haka dai zan gyara jikina, kin ga ina da kishiyoyi, Yana da kyau na je gidan zam-zam."
Ta ce." Kaya ya tsinke a gindin kaba, shekaran jiya na ji Maman Anisa tana waya da wata mai magani GARKUWAR MATA sunanta. Maman Anisa za ta cire yarinyar da take goyo daga nono shine tace ta had'a mata magani. Gaskiya duk abinda na ga Maman Anisa ta saya nagartacce ne, har take tabbatar mini da ingancinsa domin yawanci 'yan gidansu a wurin matar suke sayayyan kayan gyara, in sha Allahu zan karbo miki lambarta sai ki kira ta kuyi magana ko ta whasap ne, tana garin Kano tana kuma tura kayatanta kowane gari. Duk wani na'unin maganin matantaka idan kina bu'kata akwai wurinta cikin farashi mai sau'ki da rahusa, don har sari suke bayarwa.....08089965175 a yi magana kai tsaye ta wannan lambar..

"To yawwa, don Allah Sahura ki yi kokarin karbo mini lambarta yau din nan, sai ki turo mini, ina so mu yi magana da ita da wuri ta Aiko mini na fara amfani dashi." Ta ce." In sha Allahu rabbi yanzu zan shiga gidan da kaina na kar'bi lambar.
Sallama muka yi, na ajiye wayar na tashi domin gyara d'akin, da tunanin lamarin da yake fuskanto ni, ina ro'kon Allah Ya wanzar mini da alheri.

Ina tsaka da aiki Ya kira ni. Dama na yi hasashen hakan, wata'kila Yana ta kira lokacin muna waya da Sahura.
Na zauna a nutse na daga wayar da sallama a bakina.
Bai amsa sallamarba ya fara cewa." Na jima ina trying lambarki sai ace busy Amina ke da wa kuke wa da sanyin safiyar nan."
Yanayin yadda ya furta maganar a cunkushe shi ya sanya jikina ya dan yi sanyi. 'Wato shi kuma mai titsiye ne'
Na ce."Sahura ce kawata, muke tattauna yadda sha'anin bikin zai kasance."
Sai ya sauke ajiyar zuciya. Ya sassauta sosai ba kamar farko ba. Ya ce." Ai na d'auka wani ne yake hure miki kunne da sanyin safiyar nan."
Na ce." Wani kuma Alhaji, ai babu shi sai kai, domin zuciyata ta gazgataka akan abokin rufin asirina."

Murmushi Ya yi wanda sautinsa ya fito har sai da na ji a kunnena, cikin jin dadi Ya ce." Kin gama faranta mini rai my love, ashe na samu wannan matsayin ba a gaya mini ba sai da aka gama ja mini aji ko?"

Dariyar da babu nishadi na yi na ce." Ka kai makura a zuciyata, Kuma ina kyautata zato na alheri a kanka, ba zan yi kaico ba."
Ya saki dariyar nishadi ya ce." Na yi godiya sosai da wannan yabo da na samu daga wurinki, Allah Ya ba ni ikon kula daku bakidaya."
Na amsa da "Amin Ya Allah."
Ya ce." Yanzu wace rana ki ka tsayar ta d'aurin aure?"
"Juma'a ta sama ai hakan ya yi ko?".

"Ya yi sosai, dama ke nake jira, don ni ko yau a daura ba ni da matsala a shirye nake."
Murmushi kawai na yi. Ban ce komai ba. Ya ce." Zan tura miki kudin gyaran jiki, da hidimar da za ki yi, sannan na sanya miki kayan d'aki da labulaye, abinda dai da
za ki zo dashi kad'an ne. Don gabad'aya na canza musu furniture din gidan.
Chapter 22 · 0% Book details