← Book details Alwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 35

Sashe 5

Alwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hannu nasa na goge hawayen da yake zuba. Na ce." Na san Allah Ya yi mini Sahura, ba zan butulce masa ba, yana taimakona ta fannoni da yawa. Amma sis ina da damuwa sosai, ba zan iya aure yanzu ba sai yarana sun yi 'kwari, sis Baba Sule kwana biyu ya sani a gaba, ga Kamalu Yana nema ya fi 'karfina."

"Wace irin magana ce wannan Amina, ki haifi 'dan a cikinki sannan ki ce yana nema ya fi karfinki, me yake yi? kuma me Baba Sule yake yi miki, na ga dai ke kike hidima da kanki da yaranki, na d'auka ai ba ki da wani kalubale da mutanan gidanku."

Naja majina cikin jin ciwon abubuwan da suke faruwa na fara bata labarin abinda ya wanzu kwanaki biyu da suka wuce.
Ta ce." Ki yi hakuri, kada damuwar hakan ta janyo miki ciwo, aure dai a yanzu sai kin yi ra'ayi za ki yi tunda dai ke ba yarinya ba ce, bazawara ce muddin za ki ri'ke mutumcinki ki cigaba da sana'arki domin ki kula da yaranki, Ubangiji zai shige miki gaba, ki yi ta addu'a dai, sannan maganar Kamalu kada ki dinga yi masa kuka domin hakan zai sake jefa shi a garari, ki yi ta yi masa addu'a. In sha Allahu lamarin zai tsaya iyakacin 'kuruciya, kuma wallahi irinsu idan sun girma ba su iya hankali ba. Suna da biyayyar iyaye. Kowane yaro da irin 'kuruciyarsa.

Zuciyata ta sassauto sakamakon irin rarrashi da tausasan kalamanta. Sahura k'awata ce tun ta k'uruciya tare muka dinga fa'di tashi muna 'yan mata. Daga gidansu na samu taimako sosai a harkar karatuna. Sai dai ta riga ni aure har sai da ta yi haihuwa ta biyu tukkuna Abbansu Yusi ya yi fito da zummar aurena.

Ta ce." Tunda kin zo na samu abokiyar tafiya dama ba na son zuwa ni kad'ai wallahi, duk da hakan ba wani abu ba ne, amma dai bibiyu tafi dadi.
Na kalleta cikin nazari sai a lokacin ma na hangi ramar da ta yi, yanayinta ya nuna tana cikin damuwa.
Na ce." Da Ina za ki je ne?" Ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce." Hotoro zan je sabon kamfanin Alhaji Tajo na leda suna buk'atar ma'aikata. Maman Anisa makociyar nan tawa ta kar'bar mini form a wurin mijinta kin san shi ma yana aiki a 'karkashinsa amma dai Yana da matsayi ba 'karamin ma'aikaci ba ne, to shine suke neman ma'aikata da na gayawa Abbansu Yasir ya amince, yanzu na cike form din zan je na kai wata'kila ma a yi mini interview."

Idona a kanta har ta ajiye maganar. Na ce." Sahura ba wai zan dakile ki ba, don Allah kada ki yi aiki a kamfanin nan, ki cigaba da neman aiki na gomnati, ni ma zan cigaba da nema miki har Allah Ya sa a dace, amma hankalina bai kwanta ba wallahi tunda Abbansu Yusi ya yi aiki a kamfanin mutumin nan aka zalince shi nake jin tsoro. Kin san suna amfani da lafiya da kuzarin mutum ne, duk wahalar da za ka yi musu da lafiyarka daga ranar da Allah Ya jarrabeka da ciwo ka kwanta sai suce ba su san wannan ba, 'karshe a rubuto maka takardar sallama kuma babu ko sisi."

"Amina ni kaina akan dole zan yi wallahi, na fad'a miki tun farko Abbansu Yasir ne ya cuce ni, farkon auranmu na samu aikin rabon magani 'kauye-k'auye ya ce ba zan yi ba saboda mugunta. Gashi kuma yanzu muna nema Ido rufe dalilin hidimar gida da ta Yara tunda shi ba k'arfi ne dashi ba, wallahi idan lokacin biyan kudin makaranta ya yi hankalina yana tashi Amina, wasu lukutan Ina ji ina gani za'a koro mini Yara daga makaranta. Kin ga kuwa idan Ina aikin zan samu hanyar da zan dinga biya musu da yin wasu hidindimun babu fargaba."

Na ce." To yanzu kina da tabbacin idan mun je za a d'auke ki, wulakanci nake gudu Sahura, shiyasa ki ka ji ina wannan maganar wallahi."
"A a ai ina da hanya kai tsaye muna zuwa zan kira wayar mijin Maman Anisa d'in tunda shi ya kawo mini form din, in sha Allahu ba za a samu matsala ba."
Na gyad'a kai tare da cewa." Daga nan ja'in zuwa hotoro nawa za ki kashe Sahura, kuma nawa ne kud'in albashinki komai fa d'an lissafi ne?"
Ta ce." Gaskiya ba zai haura dubu saba'in ba, bayan haka kuma an ce sa'i da lokaci yana yi wa ma'aikatasa alheri, har da su kayan abinci Yana bayarwa."
Na ce." To ni dai tsayin shekara biyu da Abbansu Yusi ya yi aiki a k'arkashinsa bai ta'ba gaya mini ya samu wani abu ba bayan albashinsa. Kin ga fa koda aka sallame shi ma fa ba'a bashi ko kwabo ba."

A sanyaye ta ce." Zan dai jarraba na gani Amina, idan na ga babu ci sai na ajiye, don Allah ki taya ni da addu'a, ki kuma cigaba da nema mini wani aikin ko koyarwa ne irin naki."
Cikin kulawa na ce." In sha Allahu rabbi, zan taya ki da addu'a kawata, zan kuma cigaba da yi miki fafutuka, Ubangiji Allah Ya sa mu dace gabad'aya."
✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*07084653262*
[11/13, 9:30 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*

*Marubuciyar*
*Yar bangar siyasa*
*Ba'aboren namiji*
*Madadi*
*Ga irinta nan*
*Goje*
*Babban yaro*
*Sadauki Omar*
*Nida Yaya sadam*
*Da sauransu..!*

*Tallah!*
Albishirinku mata 'yan gayu yan gwalisa ku yi maza kugar zayo shagon
(Aysha/Addah beauty saloon and spa).
Shin kin taba zuwa ingancaccen saloon din Aysha/Addah, idan baki taba zuwa ba ki yi maza kar a barki a baya domin sun qware a wajen aikinsu wanda suke services dinsu cikin sauki tare da annasuwa
Suna wanke kai(wash and set)
suna wanke qafa(pedicure)
And sunayin steaming iri iri suna saida (supplements)suna kitso dama duk wani abu daku so Wanda akewa mace ta amsa sunanta mace yar qwalisa
Address dinsu nanan a Federal low-cost opposite open University *GOMBE STATE*
Ko kuma ku tuntune mu a wannan number kamar haka,
08037925676
Or
08167764242
Whatsapp ko kuma Call we’r available 24/7..
Tabbas ni ma na shaida ingancin ayyuka da kayayyakin shagon anti adda mutuniyar kirki. Babu tsada komai ana samunsa cikin sau'kin farashi mutanan gombe kada ku bari wannan sau'kin ya wuce ku.🥰

*@Arewa books*
*Bintaumarabbale.*
*Free pege4*
Ba mu fita ba sai da yaran suka dawo daga cefane tukkuna. To abin dai gashinan a hannu a hannu. Na ce." Yanzu Sahura shinkafa gwangwani biyu ce zata ishe su har su uku?" Tana gyara zaman hijabin wuyanta ta furta." To ya zan yi Amina, babansu da wuri ya fice don ma kada na tambaye shi kudi, ko sallama bai yi mini ba. Jiya dai da daddare na gaya masa zan fita. Wallahi dubu dayan kenan ta rage mini na ba su suka yo cefanan nan. Kudin mota kuwa dama cewa na yi zan kar'ba a a wurin Maman Anisa, idan na samu daga baya sai na bata.
Na dubi Yusra dake juye shinkafar a faranti domin tsincewa. Na ce." Tashi ki je ki auno kwana daya sai ki dafa muku yadda za ta ishe ku. Ki karo man'kuli da maggi da wake." Na zuge jakata na d'auko dubu biyar na mi'ka mata." Duk abinda babu ki saya a ciki." Sahura ta yi sakato tana kallona. Na tashi ina fad'in." Wannan rayuwar Allah Ya magance mana. Ta ce." Sis, anya kuwa ina lefin ki bata kudin rabin kwano."
Na ce." Don Allah kada ki bata mini rai Sahura." Yadda na fadi maganar cikin fushi shi ya sanya tayi shiru da bakinta ta juya kan yaran tana cewa.'' Yusra ki rufe gidan idan mun fita, duk wanda zai k'wankwasa kofa kada ki bude, ki ce bana nan."
Ta ce." To Ummi sai kun dawo."

Ba mu wani jima a bakin titi ba muka samu abin hawa. Ya ce sai dai mu bashi dubu daya da d'ari shida duk mutum daya d'ari takwas kenan. Na ce." Sahura shiga mu tafi a hakan ya yi mana adalci, tunda gaskiya tsakanin hotoro da ja'in akwai tazara mai tsayi.
Wajan d'aya saura muka isa. Ya ajiye mu daidai bakin kamfanin duk da sabo ne hakan bai hana masu sana'ar adadaita sahu saninsa ba idan an yi duba da shuhurar mamallakinsa.
Chapter 5 · 0% Book details