Sashe 9
Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Bayan Tukur ya gama aiwatar da duk abinda boka yace mishi ya sami me gadin mak'abartar da aka birne su ya bashi mak'udan kud'i, ya tayashi suka hak'a k'aburburan suka binne, bayan ya gama duk abinda boka ya sa shi.
a ranar da aka bashi wannan layun ikon Allah kamar ma an k'ara rok'on Allah ne akan ya ci gaba da bayyana mishi su, Dan a wannan ranar sam be runtsa ba.
Yanzu a duk inda yake, kuma ko menene yake yi su yake gani, duk ya sukurkuce ya lalace, yanzu Sam beda natsuwa balls wani abu wai shi kwanciyar hankali.
Yau Asabar a yau d'in ne kuma cikin dare yai mafarki Alaweeya tazo gaban shi ta tsaya tana kallon shi tace mishi insha Allah nan bada dad'ewa ba shima zai biyo su ya girbi duk abinda ya shuka, tun da ya farka be koma ba har gari ya waye.
yana gida yana zaune cikin d'aki yana tunanin mafita, saboda mafarkin da yayi da fatalwar su Alhaji da yake gani sun d'aga mishi hankali, musamman ma mafarkin da yayi jiya ya tsorata shi sosai.
Yanzu ya rage fita ma, saboda duk abokanan shi yanzu kallon mahaukaci suke yi mishi, shiyasa duk suka guje mishi.
Sai yanzu nadama ta fara zuwa mishi, gadai dukiyar amma sam babu kwanciyar hankalin cin dukiyar.
Tunani ya fara akan ya kamata yaje ya rok'i gafarar su Mumy watak'ila idan yai haka su dena fito mishi.
Yana cikin wannan tunanin sai ga Alhaji zaune kusa dashi, a guje ya fito daga d'akin nashi, yana fitowa d'akin ya danno falo a guje.
Kawai ganin shi su Mumy suka yi cikin falo a guje cikin firgici, ya zube a gaban su, yace " Hajiya dan Allah, ku dubi Allah Ku yafe min, " nan ya kwashe dukkanin irin makircin da ya dad'e yana shuka musu sai da ya fad'a musu komai, da yanda ya sa aka kashe Alhaji da asirin da yaiwa yaranta, babu abinda ya b'oye.
Su Mumy babu abinda suke yi banda kuka mumy ta dubesa tana"tukur mun yafe maka,yanzu tsakaninka da ubangijiinka ne .
Yusif wanda hawaye yacika a idonsa yace"oh duniya ,yanzu meye ribarka yanzu mu uku muka ragewa mahaifiyarmu ka cucemu tukur".
Alhaji da Alaweeya Tukur ya sake gani cikin falon, haba a guje ya tashi ya fita daga gidan gaba d'aya.
Yana fita kai tsaye office d'in yan sanda ya wuce a guje.
Kawai police ganin Tukur suka yi ya fad'o cikin station d'in a guje, da sauri suka mik'e suka rik'e shi ganin a rud'e yake baya cikin hayyacin shi, suka hau tambayar shi lafiya meke faruwa.
Yace musu ya kawo k'arar kanshi ne, nan ya bayyana musu duk irin abubuwan da yayi, yana cikin fad'a musu sai ya sake ganin fatalwar Alhaji kusa da 'yan sandan, nan da nan ya zabura ya fita daga cikin office d'in, yana fitowa yazo dai-dai bakin ti-ti a dai-dai wata tifa ta taho a guje ta kad'e shi, k'afar shi ta cire, idanun shi suka tsiyaye, ko kafin a kaishi asibiti Allah ya d'auki ran shi.
su Mumy sun sami labari, sun yi farin ciki sosai, suna godiya ga Allah da ya kawo musu k'arshen Tukur.
Jama'ar unguwa kaf sun k'i yi mishi sallah, dole tasa 'yan sanda suka bar shi a asibiti a mutuware.
Bayan rasuwar Tukur da wata d'aya aka dawo wa da su Mumy dukiyar su, rayuwar gidan ta dawo normal.
Sedai har yanzu kullum sabuwa suke jin mutuwar Alhaji da Alaweeya da Sadeek, kuma a koda yaushe suna yi masu Addu'a.
ALHAMDULILLAH
*To jama'a wallahi k'arshen zamani yazo, abinda muke jin labari, abinda muke tunanin bazai tab'a faruwa ba wallahi yanzu shi ke faruwa a zahiri, uba ya nemi 'yar cikinsa, d'an uwa yaci amanar d'an uwansa, mun ji yanda zuciyar mugu ta kasance, ya biyewa zuciyar shi ya shirya sharri kala kala, daga k'arshe ya mutu a wulak'ance, zaije can kuma ya fara had'uwa da sakamakon muguntar da ya yi, ina fatan masu mummunan hali ko niyyar shuka sharri irin wannan to wannan labarin zai zama darasi a garesu, Allah ya tsarkake mana zuciyar mu.*
*TSOKACI*
_I want use this opportunity to thanks my mummy,lokacin da akaa bani labarin nan,wallahi nasha kuka har nakasa barci_
_wai wani irin duniya muke cikine?_
*ku duba irin hallacin da son da Alhaji balarabe ya nuna wa dan uwansa tukur.amma jibi abinda ya sakamai dashi*
Oh duniya ina zaki damu gashi shima baa ribar daya ci a duniya,duniya takisa lahirama ta kisa...Allah yasa muguji sharrin zuciya sannan ya sa muyi kyakyawar karshe.
sannan Allah ubangiji yaji kan Alaweeya da Alhaji Ameen summa ameen.
*SAI KUN JI MU A SABON WANI LABARIN NA DABAN.*
Mune naku
*YARMAMA*
&
*🅱K😘💋*