Sashe 8
Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Itama tana dariyar shakuwa takamata rike hannun momy tayi tana"momy....ki dingamin adu'a ..kalmar shahada tayi nan ta rufe idanuwanta tana murmushi .
Sanyi kalau momy taji gabantane yafadi ta aika yusif su kira likita aguje,likita yana shigowa yayi gwaje gwajenshi ,rufeta yayi da farin kyallen kan gadon cike da tausayawa ya kalli momy yace"Allah yayi wa Alaweeya rasuwa".
Kara momy tasa ta zube awajen sumammiya yayinda siyama tanufi inda gawar Alaweeya yake ta zufe akan gawan kuka take iyakacin karfinta tana"why sister?meyasa zaki mana haka,Alawweeya muna kaunarki.please karki tafi ki barmu a wannan rayuwar .wayyo Allah kulli nafsin za'ikatul maut tabbas haka yake.i cant believe my sister is gone,"sumbatu take tamkar ta tabu daga karshe ta kwanta akasa tana gwaggwara kanta har jini yana zuba.
Su yusif ma saikuka suke,mutane sai hakuri suke basu amma siyama tamkar ta haukace tashi ta kankame Alaweeya tana wallahi sai muntafi tare bazan iya rayuwa babu keba"😭😭😭😭😭
INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN
Allah yayiwa Alaweeya rasuwa
😭😭😭😭
🅱k da yarmama suna mika sakon ta'azziyarsu zuwa ga dangin Alaweeya harda yan uwanta.
_gaskiya anyi babban rashi,domin Alaweeya macece mai addini,kyautatawa da son jama'a gashi duk inda ta zauna akwaita da saurin sabo da jama'a_
*Alaweeya yarinyace yar shekara 21 yrs a duniya inda ta karanci lawyer ,ita burinta ta saka mutane cikin nishadi,gata da kokari da taimakon jama'a ita tafi dakko halin margayi Alhaji balarabe sak*
Kowa ya shaida mutuniyar kirkice
_wallahi ko mu da muke typing saida muka zubar da hawaye sosai,domin labarin yanada taba zuciya_
Ubangiji yaji kan Alaweeya yasa Aljannace makomarta
Muje zuwa
🅱k😭
Nd
Yarmama
😭😭😭(wallahi naji mutuwar Alaweeya wanda har zazzabi sai da nayi,nayi kuka sosai)
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤*
STORY & WRITING
BY
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
&
*MARYAM YARMAMA*
*👨🏻💻👩🏻💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*
*MASOYA*
_Muna godiya k'warai da addu'o'in ku ga wad'annan bayin Allahn da suka rigamu gidan gaskiya, Allah ya saka muku da alkhairi, kuma ya baku lada._👏
Page 71-75
Haka su mumy suka ci gaba da fuskantar k'alubale na rayuwa.
Tukur kuwa facaka kawai yake yi da dukiya, babu ruwan shi da su Mumy da 'ya'yanta.
Sai da yakai ya kawo garin kwaki shine abincin su, wata rana ma haka suke zama basu ci komai ba.
A haka yunwa ta kama auta shi yai sanadin mutuwarta
.
Karuwai kuwa abun ba'a magana kullum cikin shigo dasu yake yi cikin gidan.
Haka su mumy suka ci gaba da rayuwa, tare da rok'on Allah ya kawo musu k'arshen Tukur, da kuma k'arshen wannan mawuyaciyar rayuwar da suke ciki.
Bashi gidan club, bashi wurin shaye-shaye, bashi wajen karuwai ya zab'o wadda tai mishi ya kawo ta cikin gidan nagartaccen mutum Alhaji Bala Wanda har gobe ba'a daina yabon halin shi ba.
Tukur ne zaune gaban boka dan duk masihircin mutum me tsafi baza'a kira shi malami ba, yana kora mishi bayani, yace " So nake yaran matar yayan nawa a asirce su ta yanda zasu rik'a tozarta uwar, kuma ya zamana duk abinda na gindaya musu shi zasu yi.
Boka ya shek'e da wata mahaukaciyar dariya, sannan yace " in dan wannan ne karka damu kaje gida kasha mamaki."
Tun daga wannan ranar ne Tukur yaiwa yaran Mumy asiri, nan da nan suka tsani mahaifiyar su wadda tasha wahalar haihuwar su.
Ya zamana duk duniya su Sadeek basu da masoyi sai Tukur, sun k'i Mumy kwata kwata, suka rik'a da mayya.
Akwai ranar da Tukur da yaran suke zaune, a falo Mumy tazo wucewa sai jiri ya debeta ta fad'i k'asa, ta d'an bige k'afar Sadeek, ya tashi zai daketa sai Tukur ya hana shi, sannan ya kalleta ya bushe da dariya, ya kalli Sadeek, yace " yanzu kai sai ka daketa uwarka ce fa," Sadeek yace " Allah ya sauwak'e ta zama uwata, mayya ce fa," Tukur ya sake shek'ewa da dariya, sannan yace musu su tashi suje d'akin shi yazo musu da kwalaben giya masu kyau.
Bayan sun tafi sai ya kalli Mumy yace " kad'an kika gani, ya tashi ya wuce d'akin shi yana tafiyar 'yan iska yana girgije girgije, yana zuba fito.
Tukur ya koya musu shaye-shaye, ta sanadin haka yasa Sadeek ya zama gawurtaccen d'an fashi. Koda aka kama shi aka yanke mishi hukuncin kisa.
Ranar Asabar suna zaune a falo Mumy ta shigo cikin falon, kwalbar giya ce a hannun su Sadeek suna kwankwad'a, mumy ta saki salati, Suna had,'a ido da sadeek ya tashi ya gaura mata mari, tare da rufeta da duka, sannan cikin maganar mashaya yace " ba nace ki dena kallona ba, to duk maitar ki kurwata tafi k'arfin ki, mayya kawai."
A ranar Mumy tayi kuka kamar ranta zai fita, sai ta mik'a dukkanin lamuranta ga Allah, tare da kai kukanta gare shi tasan yana sane da halin da suke ciki.
Haka ya wulak'anta rayuwar yaranta ta hanyar asirin da yai musu, gashi ta sanadin haka ta rasa d'anta an yanke mishi hukuncin kisa.
A ranar da labari ya iske su sunyi kuka kamar ransu zai fita.
Rasuwar Dadyn su sai ta dawo musu sabuwa.
Kuma har yanzu babu alamar nadama a ran Tukur, saima cin duniyar shi yake da tsinke.
Ganin burin shi ya cika, komai ya tafi yanda yake so yasa yaje yaiwa boka godiya tare da yi mishi kyauta me tsoka.
Ya dawo ya ci gaba da cin Karen shi ba babbaka.
Ku biyo mu muje
Mune naku
*YARMAMA*
&
*🅱K😘💋*
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤*
*TRUE LIFE STORY*
*END*🔚🔚🔚🔚🔚
STORY & WRITING
BY
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
&
*MARYAM YARMAMA*
*👨🏻💻👩🏻💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*
*wannan shafin nakune ZAMANI WRITTERS ASSOCIATION TARE DA ZAMAN AMANA WRITTERS.mungode sosai bisa kaunarku we love u all*
*Muna yiwa dukkanin masoya godiya, da masu yi mana fatan Alkhairi ta whatsapp, da wad'anda suka kira mu a waya muna godiya Allah saka da alkhairi.*
*Kar a manta wannan labarin ya faru da gaske duk abinda ke ciki ba k'age ko k'irk'ira, muna yi wa mamatan Addu'a Allah yai musu rahma, Allah ya k'ara musu hak'urin jure rashi.*
Last Page 76-80
...................................
_page d'in jiya munsa Auta ta mutu, to bata mutu ba, muna fatan za'ai mana afuwan kuskuren nan da muka yi_
...................................
Haka Tukur ya ci gaba da cin Karen shi ba babbaka.
Mumy da Siyama ne suka dage da Addu'a kullum cikin dare, su yi ta kuka, suna kiran sunayen Allah kyawawa, suna kai k'ara wajen Allah ya saka musu, ya kawo musu k'arshen Tukur.
Tukur ne cikin Club d'in su na mashaya tare da wata sabuwar karuwar kuma domin kullum cikin canjin mace yake baya kula mace d'aya kamar wani bunsuru.
bayan sun yi raye-rayen su sun shawu, suka fito basu zame ko ina da ita karuwar tashi ba sai gida.
Ko da shigar su suka tarar da su momy suna shan garin kwaki.
Karuwar shi ta kalle shi, tace " Baby wad'annan kuma su wanene?" Da yake karuwar bata jin hausa, sai Tukur ya canja harshe zuwa turanci yace " wallahi wasu Almajirai ne suke neman taimako nace su jirani in dawo, ya juyo inda su Mumy suke, ya kalli su Mumy sannan cikin harshen hausa yace ba na hanaku zama Ku shantake a cikin falon nan ba? Salon a inzo da bak'i a ganku Ku zubar min da mutunci koh.
Ba Wanda ya kula su duk da cewa sun ji abinda ya fad'a wa karuwar tashi cikin harshen turancin.
Bayan ya gama bambamin shi ba Wanda ya kula shi yaja karuwar shi suka haye d'akin shi
Tun daga ranar su Mumy basu sake zama a falon ba, saboda gudun kar yai musu tijarar da tafi haka, sedai Addu'a basu fasa yi ba kullum cikin yin Addu'a suke yi ba dare ba rana.
*BAYAN SATI 'DAYA*
Yau laraba, Tukur ne kwance cikin d'akin shi, yana zuba fito ya d'auko giyar ya zauna ya zuba a Kofi ya fara kwankwad'a kenan sai yaga inuwar mutum a gaban shi acikin d'akin.
Yana d'aga kai kawai sai yaga Alhaji a gaban shi, ya sake mutsuke idanun shi, sannan ya k'ara dubawa yaga bega kowa ba, se yai dariya, sannan yace " daga fara shahuwata har na fara buguwa.
Ya ci gaba da sha, yana d'agowa ya k'ara ganin Alhaji, ya mutsuke ido amma yana nan dai inda ya ganshi, zaro idanu Tukur ya yi, ya fara ja da baya yana ihu, da gudu ya fad'a d'akin bacci ya hau kan gado ya rufe idanu da matashi jikin shi ba inda baya rawa saboda tsabar tsoro.
Can bayan wasu lokuta sai ya d'ago kanshi be ga kowa ba, sai ya baje tsakiyar gadon ya fara bacci.
Washe gari, sai abinda ya faru jiya yaita dawo mishi, duk da dai ya yi tunanin abinda ya faru jiyan saboda ya yi shaye-shaye ya bugu ne, amma duk da haka haka ya wuni a ranar sukuku kamar ba shi ba.
Bayan kwana biyu, Tukur yasha gayu ya had'u saboda wani casu da suka shirya a ranar.
Bayan ya gama shiri ba tare da wani b'ata lokaci ba sai ya d'auki hanya, ko da Isar shi gurin 'yan uwansa 'yan iska suka hau ihu suna fad'in " ga babban yaro," suna zuba mishi kirari.
An fara casu kenan yana d'aga kai yaga Alhaji tsaye kusa dashi, wani mahaukacin ihu ya saki, ya fita daga wurin taron a guje, suma abokanan shi suka biyo shi da gudu suna tambayar shi lafiya.
Yaje zai shiga mota yaga Alhaji zaune cikin motar, haba da gudu ya d'auki hanya duk nisan wajen amma be tsaya ba saida ya isa gida.
Haka abokanan shi suka tsaya bakin ti-ti suna mamaki da tambayar anya lafiyar Tukur k'alau kuwa.
Haka ya ci gaba da kasancewa duk inda yaje sai yaga Alhaji a gaban shi.
Washe gari Tukur ya buga sammako sai gurin boka ya fad'a mishi abinda ke faruwa, fatalwar Alhaji da ta Alaweeya suna ta zuwar mishi.
Boka ya bashi wasu layu guda hud'u, sannan ya kalle shi yace " d'aya ka saka a k'abarin Alhaji bazai k'ara zuwa maka ba, d'aya a k'abarin Alaweeya, d'aya ka ajiye a k'asan filon d'akin ka, d'aya kuma wannan me igiyar ka sakata a wuyanka, Ina tabbatar maka daga yau bazaka sake ganin su ba.