Sashe 6
Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bazai tab'a mance fuskar Alhaji ba, mutumin da ya taimaka mishi ya tallafawa rayuwar shi har ya kai wannan matsayin zama soja.
Ba b'ata lokaci ya kira lambar wani aminin shi d'an sanda, ya shaida mishi abinda ke faruwa tare da yi mishi kwatancen inda yake.
Ba a d'auki lokaci me tsaho ba sai ga d'an sandan tare da jami'an tsaro masu yawa, tare da motar d'aukar mara lafiya, nan da nan suka kewaye gurin.
Basu tsaya b'ata lokaci ba suka d'auki su Alhaji aka saka su a mota sai asibiti.
Likitoci sun tabbatar musu da cewa Alhaji Allah yai mishi rasuwa, shi kuma drivern suma yayi, an cire mishi harsashin da yake jikin shi, nan bada dad'ewa ba zai farfad'o.
Sojan nan kuka yake yi ba k'ak'autawa, Abokin shi d.p.o yana rarrashin sa, tare da shawartar shi kan su d'auki gawar Alhajin sukai gidan mamcin domin suma su san halin da ake ciki.
Wajen fita da gawar Alhajin daga asibiti haka doctor's da Norse's suka firfito kowa sai kuka da kuka, da salallami domin d'ad'd'aiku ne cikin su Wanda ba Alhajin bane ya d'auki nauyin karatun su, suna kuka suna binshi da addu'a har aka fito dashi.
Nan aka shigar da gawar Alhaji cikin mota suka doshi gidan shi.
Ko da Isar su gidan su Mumy wad'anda suka kasa zaune, suka kasa tsaye, ko abinci sun kasa ci, suna jin k'arar mota dukkanin su suka tashi, suna rige -rigen fitowa domin su duba su gani ko Dadyn su ne ya dawo.
Suna fitowa farfajiyar gidan turus suka ja suka tsaya, ganin gawa kwance a tsakar gidan su, ga kuma soja da 'yan sanda sun kewaye gidan.
A dai-dai wannan lokacin Tukur ya tashi daga bacci, dama sallah ba yinta yake yi ba, yana fitowa shima yaja ya tsaya tare da zazzaro idanu harda k'arfin halin tambayar meke faruwa.
Mumy da Alaweeya da Yusuf fad'uwar gaban su ne ya tsananta, ita kuwa Mumy jikinta ya riga da ya bata Alhaji ne kwance a gaban su, ya rasu.
Ganin gabad'aya 'yan sandan sun kasa yi musu bayani, kuma duk wanda aka tambaya cikin su sai su duk'ar da kai suna hawaye.
Mumy ta durk'ushe a k'asa domin hakan da sukai ya tabbatar mata da hassashen zuciyarta, ta saki salati tare da fashewa da kuka me tsuma zuciya.
Alaweeya ce ta nufi gawar da sauri tare da yaye mayafin da aka lullub'e fuskar dashi, tana bud'ewa taga Dadyn su kwance cikin jini, sakin mayafin ta yi da sauri tare da girgiza kai tana ja da baya, sai luuuu ta fad'i k'asa sumammiya.
Tukur dake gefe zuciyar shi fara k'al kamar takarda, yace cikin zuciyar shi bari yai suman k'arya shima kar a gano shi.
K'wala k'ara ya yi sha yace "innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Yayana," shima se yai baya luuu ya sume.
Yaran Alhajin ne gaba d'aya suka k'araso kan gawar suna kuka suna jijjiga shi suna fad'in Dadyn mu ka tashi.
Mumyn su ce ta rarrafo inda suke, ta rirrik'e su, tace " kiyi hak'uri Dadyn mu bazai tashi ba, dadyn mu ya rasu, Dadyn mu ya tafi ya barmu, mun rasa shi rashi na har abada.
Fizge hannayen su suka yi daga gareta suna kuka suna girgiza kai suna fad'in " a'ah Dady be mutu ba," komawa kan gawar suka yi suka ci gaba da jijjiga shi suna fad'in " Dady ka tashi."
Cikin 'yan sandan nan kaf babu Wanda bai yi kuka ba.
Nan da nan yara da manya suka cika k'ofar gidan, yara da manyan unguwar kuka suke kamar zasu shid'e.
Saboda Alhaji mutum ne me barkwanci da wasa da dariya, ga taimako, unguwar nan kaf ba Wanda be shak'u da shi ba musamman ma yara shi mutum ne me son yara, kuma yana tallafawa rayuwar su, shiyasa kowanne daga cikin su a yau yake kukan rasa shi.
D'aya daga cikin yaran unguwar ma Wanda yafi shak'uwa da Alhajin shima zuwa ya yi wajen gawar cikin yaran Alhaji yana kuka yana jijjigashi.
Nan da nan aka d'ebo ruwa aka yayyafawa Alaweeya amma ina ko motsi bata yi, hakan yasa soja cikin muryarshi wadda ta disashe saboda tsabar kuka yai umurni da a kaita asibiti.
Shi kuwa Tukur ana yayyafa mishi ruwan ya mik'e kamar gaske, tare da sakin wani sabon kukan, ya shiga cikin yaran ya duk'a wajen Alhajin shima yana kuka yana fad'in "Yayana meyasa zaka tafi ka barni, kai kad'ai ne Wanda ya rage min," sai ya sake fashewa da kuka.
Muje zuwa
Mune naku
*YARMAMA*
&
*(🅱K CE)*😘💋
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU 🖤🖤*
*TRUE LIFE STORY*
STORY & WRITING
BY
*MARYAM 'YARMAMA*
*👨🏻💻👩🏻💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*
&
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
_wannan shafin kacokam Sadaukarwa ne ga *🅱K FANS GROUP* tukuicin soyayyar da suke nuna mana da kuma novels d'in mu, muna k'aunar Ku sosai, kamar mu Baku ranmu kyauta, mungode sosai da k'auna🙏_
*MASOYAN MU*
_Masoyan mu na nesa da na kusa muna rok'on ku dan Allah ku saka 'yar uwar mu *Aisha mumys frnd* addu'a Allah ya bata lafiya da dukkanin musulmi baki d'aya._
Page 51-55
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!!!" Kalmar da keta fitowa daga bakin Mumy kenan, yayin da hawaye ke wanke fuskarta.
Sai Allah ya sa mata dakiya da juriya, d'an sandan nan ne ya karb'i wayar Mumy ya kira 'yan uwa da abokan Arzik'i, shima Tukur ya kikkira wasu yana kuka yana sanar da su nan da nan aka cika gidan.
Ba gidan ba kad'ai titin unguwar kaf cike yake da mutane wad'anda suka zo domin su sallaci gawar Alhaji.
Kuma kowanne ka gani daga cikin su kuka sosai yake yi na rashi, duk inda ka gifta zaka ji suna kuka suna fad'in munyi babban rashin Mutum na gari me taimako da tausayi da son na k'asa dashi, gaskiya mutuwar nan ta gigita mutane da dama, wasu fad'i kawai suke d'azu fa da zai fita sun ganshi har suka gaisa dashi.
Allahu Akbar! Alhaji kam ya dace, tun kafin ya tafi makwancin shi wato cikin k'abari kyawawan shaidu yake ta samu ta ko'ina daga bakunan mutane, tabbas shi kam ya dace manya da yara suna kokawa kan rashin sa, se dai mu mu yi fatan Allah kasa namu k'arshen yai kyau.
Haka aka yi wa Alhaji wanka aka suturta shi, sannan aka ce iyalan shi duk su fito su yi mishi addu'a za'a tafi dashi makwancin shi.
Dukkanin su suna duk'e a gaban gawar banda Alaweeya wadda take kwance a asibiti.
Mumy ta kalli fuskar mijinta wadda take cike da annuri, idan ka kalle shi sai kaga kamar murmushi yake yi, tace "Dadyn mu a zamana da kai babu abinda ka tab'a yi min na cutar wa, ina rok'on Allah ya saka maka da kyakkyawa, Allah ya amince mu k'ara kasancewa da juna acikin Aljanna, wanda yai silar raba mu da kai kuwa Allah ya saka mishi da sakamako dai-dai da abinda ya aikata gaba d'aya d'akin suka d'auka da ameen"
Tukur ma ya yi addu'a amma ba'a jin me yake cewa, sai kuka da yake ta k'ak'alowa.
Bayan sun gama addu'ar ne anzo za'a d'aga shi a tafi dashi zance yasha bam-ban.
Ana d'aga shi Mumy ta rirrik'e gawar karakam tak'i saki tare da fashewa da kuka tana kiran sunan Alhajin, suma yaran duk sun rirrik'e shi suna kiran sunan shi suna kuka, dak'yar mutane suka b'anb'are su daga jikin Alhajin.
A lokacin ne kuma zuciyar Mumy tai mugun karaya da taga dagaske fa sun rasa shi kenan, tana ganin an nufi hanyar fita dashi ta fashe da kuka me k'ara tare da k'wala wa Alhajin kira, daga nan sai kuma itama tai baya luuuuu ta fad'i k'asa sumammiya.
Itama saida aka kaita asibiti, bayan kwana biyu jikin su yai kyau se dai dukkanin su suna da hawan jini da ciwon zuciya, dama ita Alaweeya tana da shi, sanadin lalata mata rayuwa da Tukur ya yi, mutuwar mahaifin ta ya tayar da ciwon.
Ita kuwa Mumy sanadin mutuwar mijinta ne ta kamu da ciwon zuciyan.
Haka dai aka sallame su suka dawo gida suka ci gaba da karb'ar gaisuwa.
Mutane kuwa koda yaushe cikin b'arkowa suke, maza da mata kuma kowanne yazo sai ya yabi Alhaji tare da tunowa da alkhairan da yai musu.
Shi kuwa Tukur a duk lokacin da aka yabi Alhaji wani irin haushi yake ji, gashi babu Wanda zai zo gaisuwar nan har ya tashi ba tare da ya yabe shi da fad'in alkhairin shi ba.
Sojan nan tun da aka yi rasuwar ko da yaushe yana nan ana zaman makoki dashi, dama a ranar da sukai rashin Alhajin tafiya zai yi, wata tafiya ce ta kama shi, Ashe ba rabon ya yi ta, domin ya sawa ranshi sai an gama zaman makoki an watse zai bar wajen, kuma ya k'udurta a ranshi zai saka Alhajin da iyalen shi cikin dukkanin Addu'ar shi, domin d'an halak be tab'a manta alkhairi.
To dama haka rayuwa take, komai yai farko zai yi k'arshe, duk abinda ka saba dashi dole wata rana zaka rasa shi, se dai fatan yin kyakkyawar k'arshe da cikawa da imani.
*_muna bawa masoyan mu hak'uri na jinmu shiru shekaran jiya da jiya, insha Allah ba zamu k'ara tsayawa ba har sai mun kammala gaba d'aya, mun gode da k'aunar Ku sosai._*
_masoya ku dinga yiwa Alhaji balarabe adu'a domin gaskiya anyi babbar rashi😭😭_
INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN
Muje zuwa
Mune naku
*YARMAMA*
&
*(🅱K CE)*😘💋
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤*
*TRUE LIFE STORY*
STORY & WRITTING
by
*MARYAM YARMAMA*
*👨🏻💻👩🏻💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*
&
*BILKISU Z.Ya'U(🅱k)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
Page 56-60
*Wannan shafin nakune ZAMANI WRITTERS ASSOCIATION*
_Mungode bisa kaunar da kuke nunawa littafin nan musamman Aunty nasmat,Allah ya biyaku_ AMEEN SUMMA AMEEN🙏
_ubangiji Allah yaji kan Alhaji bala,yasa aljannatul firdaus ce makomarsa😭_