Sashe 5
Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jira kawai yake yi dare ya tsala yaje ya aiwatar da manufar shi.
Sai da dare ya tsala wajen k'arfe biyu da rabi na dare sannan Tukur ya fito daga d'akin shi, tare da wani farin k'yalle wanda yake d'auke da maganin bacci a jiki.
'Dakin Alhaji ya nufa, kuma yai sa'a Allah ya taimakeshi be had'u da kowa ba duk sun dad'e da yin nisa a bacci.
Yana shiga d'akin ya tarar da Alhaji kwance yana ta bacci, cikin sand'a ya k'arasa kusa da fuskar Alhajin ya sa mishi wannan farin k'yallen, sannan ya saki murmushin jin dad'i, ya san cewa Alhaji kuma shi da tashi sai ya d'auki dogon lokaci, saima ya makara.
Bincike ya hau yi cikin d'akin ta ko ina, cikin sa'a kuwa ya harhad'a dukkanin wasu takardun kadarorin Alhajin gaba d'aya, ya tarkata su waje d'aya.
Bayan ya gama harhad'awa ne sannan cikin sauri ya cire k'yallen da ya saka a fuskar Alhajin, sannan ya d'auki lodin takardun dukkanin kadarorin Alhajin ya fice daga d'akin.
Da isar shi cikin d'akin ya baje a tsakiyar falon shi, bayan ya sakawa d'akin key.
'Dai-d'ai ya sake yiwa takardun yana sake dubawa wani farin ciki yana k'ara ziyartar zuciyar shi.
A ranar be yi bacci ba saboda duk ya k'osa gari ya waye a kawar da Alhaji duniya ta dawo mishi sabuwa, tun a daren ya fara tsare-tsaren yanda zai tafiyar da dukiyar, da abubuwan da zai gabatar da ita.
Littafi ya d'auko, sannan ya d'auko wata tsohuwar takarda wadda ya gani acikin takardun ta wani fili da Alhajin ya siya ne, a jiki akwai sa hannun Alhajin.
Ita yaita kallo yana so ya kwaikwayi sa hannun Alhajin, saida ya kusan cika littafin nan, sannan Allah ya taimake shi ya iya signing d'in Alhajin sak.
Sai da yabi takardun nan d'aya Bayan d'aya ya maida sunan shi, tare da saka hannun shi da Wanda ya saka iri d'aya sak da na Alhaji, sai kuma takardun yarjejeniya Wanda Tukur d'in ya rubuta da hannun shi a zuwan Alhajin ne ya rubuta na amincewa cewa komai ya zama na Tukur d'in, kuma nan ma ya kwafi sa hannun Alhajin ya rubuta.
Sai da ya kammala komai ne sannan hankalin shi ya d'an kwanta, yasan dai ko ba'a samu nasarar kashe Alhaji ba gobe, to dukiya dai ta zama tashi, dan babu wanda zaiga rubutun da sa hannun yace ba Alhajin ne da kanshi yasa ba.
K'ara kallon sa hannun Alhajin ya yi, da kuma Wanda ya sa, yaga sak iri d'aya, sai ya fad'a kan gado, tare da kecewa da wata irin dariya, sannan yace "wayyo duniya sabuwa," ya d'aga k'afa sama yana rawa da su.
*WASHE GARI*
Washe gari Mumy taga har wajen k'arfe takwas amma bata ga fitowar Alhaji ba, hakan yasa ta nufi d'akin shi domin dubawa ta gani ko lafiya.
Tana zuwa ta tarar har yanzu bacci kawai yake ta sharawa, k'arasawa wajen shi ta yi, tare da tayar da shi, sannan tace " Alhaji yau lafiya kake kuwa? naga baka tab'a kaiwa wannan lokacin kana bacci ba, kuma gashi naji ma kace yau kana da meeting. "
Alhaji nan da nan ya tashi, yana salati, agogo ya fara kalla, k'arfe takwas, kuma tara da rabi suke da meeting d'in, yace " subhanallah, yau wane irin bacci nayi haka har na rasa sallar Asuba," yana magana yana k'ok'arin saukowa daga kan gado.
Mummy tace " lallai Dadyn mu bacci yai dad'i yau, nima gani nayi baka tab'a dad'ewa haka ba tare da ka sauko ba shiyasa nace bari inzo in duba," koda take wannan maganar tuni Alhaji ya shige toilet.
Alwala ya fara d'aurowa, sannan ya fito Mummy ta shimfid'a mishi dadduma ya tayar da sallah.
Mumy na zaune har ya Idar, ya d'auki kusan minti sha biyar yana istigfari da rok'on Allah Afuwa, sallar asuba da ta wuce shi yau.
Bayan ya kammala Addu'a suka fita tare da Mumy sai wajen cin abinci, suka tarar da kowa ya hallara su kawai ake jira, banda Tukur da suka zo suka tarar har yama kusa gama cinye nashi abincin, yana gama ci kuma ya tashi ya bar wajen.
Bayan an zuzzubawa kowa abincin nan da nan kowa ya fara cin nashi, banda Alhaji da yaketa faman jujjuya cokalin yanda kasan yaro.
Mumy ce ta lura da yanayin shi, ta kalle shi tace " Alhaji wai yau lafiya kake kuwa, naga tun d'azu kake juya cokali ka kasa kai koda 1 spoon bakinka?"
Haba su Alaweeya suna jin haka gaba d'ayansu hankalin su ya dawo kanshi, nan da nan kuma kowanne daga cikin yaran ya ajiye cokalin shi harda Mumy, suka yo kan Dadyn da tambayoyi.
Haka suke yi, duk lokacin da suka ga canji daga wajen iyayen su haka suke yi, basa k'ara yin walwala har sai iyayen nasu sun dawo normal, da iyayen nasu suka tambayesu meyasa suke haka, sai yaran suka ce suma suna shiga damuwa ai a Kansu akan koma menene ya same su, damuwarsu ce kesa nan da nan iyayen su sauko, su saki ransu koda abinci suke ci sukaga Mumy ko Dadyn su cikin damuwa to suma ajiye nasu abincin suke yi har sai ya dawo normal.
Dady ya kalle su yai murmushi sannan yace " ina alfahari daku, kuna nuna damuwarku a kaina sosai, to ranar da kuma kuka rasani ya kenan, Ku kwantar da hankalinku, babu abinda yake damuna, yau dai haka nan na tashi wani iri, da kuma matsanancin fad'uwar gaba."
Yaran suna jin Dadyn su ya ambaci mutuwa sai suka hau kuka musamman Alaweeya kuka take kamar zata shid'e, tun jiya suka ga yanayin Dadyn su ya canja, yanayin maganganun shi kamar na me barin wasiyya.
Mumy ne da Dady suka samu dak'yar suka lallashi yaran, abinci kuwa saida suka ga Dadyn su ya saki ranshi har yaci kad'an sannan hankalin su ya kwanta.
Yaran suka yiwa Iyayen nasu sallama suka fita domin tafiya makaranta, Alhaji ya k'ure su da idanu har suka fita daga d'akin, duk Mumy na kallon shi.
Mumy ta kalle shi tace " kodai zaka hak'ura da zuwa meeting d'in nan ne kai musu waya ka sanar dasu sai wani lokacin?"
Dady yace " a'a sun fad'amun yana da matuk'ar muhimmanci, kawai kiyi mun addu'a, "
Mumy tace "to Allah ya tsare mana kai a duk inda kake, ya dawo dakai gida lafiya."
Dad ya amsa, sannan ya nufi motar da zasu fita da ita, driver ya bud'e mishi, bayan ya shiga ya sauke glass k'asa ya d'agawa Mumy hannu alamar yana yi mata bye-bye, itama tana d'aga mishi hannu, har motar ta fita daga gidan.
Sun yi nisa cikin tafiyar yaga driver d'inshi ya d'auke hanya ya nausa cikin daji, Alhaji ya kalle shi yace " ya naga ka canza hanya ka shiga damu cikin daji, ina zaka kaimu?"
Driver yana kuka yace " Alhaji kayi hak'uri, na bi son zuciyata na karb'i kud'i domin in kawo ka a kashe ka."
Kafin Alhaji yai wata magana sai ga su Bullet sun kewaye su, nan da nan Bullet ya harbi Alhaji a k'irji, sannan ya harbi driver d'in Alhajin a k'afa, basu bar wajen ba saida suka tabbatar Alhaji baya numfashi ya mutu sannan suka bar wajen.
Ku biyo mu muje
Mune naku
*YARMAMA*
&
*(🅱K😘💋)*
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU 🖤🖤*
*TRUE LIFE STORY*
STORY & WRITING
BY
*MARYAM 'YARMAMA*
*👨🏻💻👩🏻💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*
&
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
Page 46-50
Bullet suna b'acewa daga gurin suka kira Tukur suka shaida mishi sun cika aiki, Alhaji ya tafi garin da ba'a dawowa, farin ciki ne ya lullub'e Tukur, nan take yai musu transfer kud'i masu yawa yace gashi nan su k'ara.
Tunda Alhaji ya fita ita ma Mumy gabanta yake ta fad'uwa, ta rasa dalili, Alhaji kafin ya fita ya sanar da ita cewa bazai wuce k'arfe sha d'aya zuwa sha biyu ba sun gama meeting d'in ya dawo gida, amma yanzu wajen k'arfe Uku saura shiru ba shi ba alamun shi.
Shi kuwa Driver tun lokacin da aka harbe shi a k'afa ya suma.
Yara duk sun dawo daga makaranta suma dai kamar jikin su ya basu zasu yi rashi haka suka zauna jugum.
Suna dawowa daga makaranta Dadyn su suka fara tambaya domin sun riga da sun saba duk in suka dawo daga makaranta sai ya kira sun gaisa da kowa, daga nan idan da me wata buk'ata ya fad'a mishi ya taho musu dashi, hakan yasa yaran suka yo caaa kan mumy da tambayar ina Dadyn su ya tafi ganin lokacin da ya saba kira ya gota bai kira ba.
Hakan ne ya k'ara tayar da hankalin Mumy ta shiga neman wayar shi a kashe, Alaweeya ma haka sun kira yafi a k'irga ana ce musu wayar na kashe, har yamma ta yi amma shiru ba Alhaji.
Duk wainar nan da ake toyawa Tukur yana d'akin shi yana sharar baccin da be samu ya yi ba jiya, hankalin shi kwance.
Nan da nan mumy ta baza masu tsaron shi domin a dubo shi, har gurin aikin shi anje duk baya nan, gashi ranar kamar Allah ya rufe bakinta ta kasa tambayar shi inda zasui meeting d'in.
Wani soja ne ya kutso kan titin da zai sadaka da cikin wannan dajin, yana zuwa dai-dai nan kashi ya matse shi, ya faka motar shi, sannan ya kashe ta ya rufe ya saka makullin a aljihu, sai ya shiga daga cikin dajin domin ya samu ya biya buk'atar shi, ya tsugunna kenan ya fara sai ya d'aga kanshi sama yana fito yana zuba wak'ar su ta sojoji abun shi yanda kasan a gida yake.
Bayan ya gama yai tsarki ya mik'e tsaye, yana d'aga kai gaban shi ya hango mota can nesa dashi.
Daga inda yake zuwa gurin da motar take akwai tazara sosai a tsakani.
Har ya juya zai tafi ya sake kallon inda motar take, yace kai gaskiya sai yaje ya duba ba mamaki ma 'yan fashi ne.
Yana k'arasowa wajen ya yi matuk'ar razana da gigicewa ganin sanannen mutumin dake kwance cikin jini a cikin mota, gefe kuwa driver ne Wanda aka harba a k'asa, nan da nan ya hau salati.