← Book details Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 9

Sashe 2

Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shigowa cikin gidan ..kowa cikinshi yaduri ruwa banda alaweeya da ko tsoranshi bataji .

Cikin fara'a Alhaji ya rungumeshi don yana matukar son tukur sosai sannan yace"bakin turai har angama karatun kenan".

Cikin jan aji tukur ya saki alhaji ya zauna akan luntsumemen kujerar yace"eh ai karatunsa ba wuya".

Cikin karkarwar baki momy da yaranta suka fara gaishe da tukur ,a yangace yake amsawa idonsane ya sauka akan alaweeya dake zaune ba dankwali akanta gashinta yasha gyara sai latse latsen waya take.sanye take da riga gown tasha kyau .

Momy dataga tukur sai kallon Alaweeya yake cikin tsoro ta dan doki cinyar Alaweeya tace"ke bazaki gaishe da karamin dadynki ba".

Tsaki Alaweeya tayi tadago da idonta tana karewa tukur dake kallonta kallo sannan ta tashi tace"wannan dan iskan bai cancanci yazama ubana ba,Bazan gaisheshiba wallahi".*

Alhaji ya kalli alaweeya ya daka mata tsawa yana"ke kinsan dawa kike magana,be carefull with me,zaki gaisheshi kosaina saba miki".

Bude baki Alaweeya tayi tamkar zatayi kuka ta nuna tukur tana"Dad saboda wannan gayen zaka min tsawa,kasan a rayuwata yanda na tsani amin tsawa .shine zakamin tom wallahi ko za'a kasheni bazan gaisheshiba".
Daukar wayarta tayi ta harari tukur tahau sama tabar falo din,momy dai da yayanta ko motsi basu iyayiba.

Lumshe ido tukur yayi don gaskiya ya yaba da kyawun Alaweeya da surarta "haka alaweeya ta girma".

Alhajine yasa masu aiki suka gyarawa tukur part dinshi a upstair,suka bashi abinci kala kala.

Washegari an hallara anacin abinci a dinning harda tukur da yaketa satan kallon Alaweeya.

"Daddy dama a makarantane akace mu kawo kudin t.shirt na graduation din mu,kowa ya kawo nice ban kawoba". Alaweeya ce cikin shagwaba take fadin haka yayin da sukecin abinci a di.

Alhaji ya kalleta ya murmusa yace "ke meya hanaki fada iyeh?bana tura miki dubu dari a account dinkiba".tukur yanajin Alhaji ya turawa Alaweeya dubu dari a account dinta ,ya murtuke fuska ya buga teburin cin abincin wanda yasa su momy suka tsorata sannan ya aje spoon din dayake cin abinci yatashi yabar wajen cike da bacin rai .

Kowa dake dinning din suka bisa da kallo...yayinda alaweeya ta bi bayansa da harara sannan ta kalli abbanta cikin shagwaba tace "abba nifa dubu dari ba abinda zaimin...please ka daure ka karamin wani,nifa banason taba kudin Account dina don so nake ka cikamin insiya mota".

Dariya duka suka kaure dashi

Abba yayi murmushi yace "to mama zankara miki shikenan hankalinki ya kwanta,keda sadeek da siyama duk zakuji alert yau".

Dinning din yadauki murna suna ta "thanks you abba Allah ya bude hanya".

Momy dake sanye da farin medical gilashi tace "Alhaji kanafa sangarta yaran nan,nidai ka rage basu kudi kaji,saboda ran tukur yana baci duk lokacin da kabasu kudi".

Ko daya abba bai dauki maganar matarsa ba saima cewa da yayi"na taimakawa yan waje ma,nayiwa mutane hidima balle ya'yana farinciki.yayan nan guda hudu su Allah yabani don haka dole in musu abubuwan da sukeso...banda dangi daga TUKUR sai su.su kawai nake dasu aduniya,kuma inada arziki kar inmusu bazaiyuba,shima tukur din ai inamai sosai acikin yaran wana kai karatu kasar waje iyeh ki gayamin".

Tashi yayi yayinda suka rufamai baya,suka rakasa har bakin harabar gidan ,driver yabudemai bayan mota yashiga..sannan karamar cikinsu humaira tamikomai briefcase dinsa tamai sunba a kumatu...haka driver yaja motar sunamai daga mai hannu..

Haushine yakama TUKUR dake kallon duk abinda sukeyi ta taga.wani bakinciki ya mamaye mai zuciya,matsawa yayi daga bakin windonsa yazauna akan gadonsa yana neman mafita "dole in hargitsa gidannan,dole in kashe Alhaji in mallaki dukiyarsa sannan inyi facaka dashi".haka tukur ya ayyana aransa ...

Baigama fadin hakaba ,Alaweeya tashigo dakin .tsayawa tayi abakin kofa tana mai aikamai sakon harara domin duk duniya ba wanda ta tsana kamar uncle dinta.

Shiko tukur ko damuwa baiyi da kallon da takemaiba,shidai burinsa yacika burinsa na lalata mata rayuwa,don bazai jureba domin ya kwadaitu da kyakyawar surarta . Ahankali tukur yakalli alaweeya cikin mayaudarin murya wanda yake amfani da ita wajen sace zuciyar mace yace "ala....weeya lafiya kika shigomin daki ina matsayin uncle dinki ko gaisuwa babu".

Wani yarrr alaweeya taji amma tadake ta murguda baki tana" nazone dama in gaya maka karka kara shiga harkata.in abbana yanamin magana ba ruwanka ehe kaji dai".

A hankali tukur ya taso daga kan gadon abinka da farin mutum dogo hansome guy mai faffadan kirji ga kuma dogan hanci da sexy eye gashi yamata kwarjini...kafa mata sexy eye dinshi yayi yana mai karasowa,itama Alaweeya takasa dauke idonta daga na uncle amma ta dake ta murgudamai baki tace"lafiya kake kallona kamar wani maye,ko acan turan ka koyo maita"....shiru tayi sakamakon ganin tukur ya nufo inda take.

Mune naku
_yarmama 👊_
&
*🅱k😍💋*
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤*

*TRUE LIFE STORY*

STORY & WRITTING
by

*MARYAM YARMAMA*
*👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*

&
*BILKISU Z.Ya'U(🅱k)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*

Page 16-20

Yana nufowa wajen,Alaweeya tana ja da baya har tazo bango,shima matsowa yayi har suna iyajin numfashin juna yayi murmushi cikin murya mai sace zuciyar mace yace "Ala..weeya an girma shine na dawo ko sanda zuwa babu iyeh haka akeyi".

Rau rau Alaweeya tayi da ido don duk rashin kunyanta sai yau tsoran Uncle ya shigeta sannan ta kallesa cikin sanyin murya tace"uncle am sorry is mistake".

Tukur yayi wani shu'umin murmushi yasa hannu a Aljihunshi ya dakko wata yar tagarda ya bude daka gani kasan hodan ibilis ce,daidai fuskar Alaweeya ya fasa,nan Alaweeya ta lumshe ido tayi luuuuu tamkar zata fadi .tarota tukur yayi ya kaita kan gadonsa,cire rigarsa yayi ya haye kan gadon da niyyar keta mata haddi....haka tukur cikin kankanin lokaci ya lalatawa Alaweeya rayuwa (subhanallah😭).

Wanka yashiga yana murmushin samun nassara..yafito ya shirya cikin wasu arnayan kaya ,kananun kaya harda sarka ya fesa turare ya dauki daya daga cikin motocin gidan yafice zuwa club dinsu na mashaya.

Bayan wasu dakika Alaweeya ta tashi kanta ya mata nauyi ga wani radadi datakeji,da kyar ta tashi kanta taji ya juyawa duba gadon tayi taga duk bedsheet din kaca-kaca da jini ,kuka msi tsuma zuciya tasa tana tuna abinda yafaru sannan tafara tuna nasihar momy:

_"Alaweeya kece babba,karki kuskura wani abu yashiga tsakaninki da wani namiji,karkiga kinada degree kiyi tunanin akwai namijin dazai aureki bayan kin siyar da mutuncinki,no ko bai ganeba sai Allah yasakamai"_

Kuka Alaweeya ta kara fashewa dashi tashiga toilet d'in uncle ta bude shayan ruwan zafi tahada da ruwan sanyi ta gasa jikinta fitowa tayi ta gyara jikinta,Tana nadamar shigowa d'akin tukur, bata gama rufe bakiba tukur yashigo d'akin ya kalli inda Alaweeya ke zaune akan gado tanata ruzgar kuka yafara waka yana wakar _"my body my money na yo own woo baby"_.

Aguje Alaweeya ta taso ta rik'emai kwalar riga tana "wallahi uncle tunda kai ka lalatamin rayuwa, wallahi saika aureni".

Tukur da yaji kukanta ko ajikinsa ya kalleta ya tab'e baki yace"Tab' saidai fa kiyi hak'uri nawuce wajen domin ni bana maimaitawa, kuma bazan aurekiba, ai bama aure a tsakaninmu tunda ke d'iyatace".

A hankali Alaweeya tasaki tukur taja da baya tana kuka maicin rai tana"uncle kasan ni d'iyarkace kuma ka ketamin haddi, macuci azzalumi sai Allah ya sakamin, ka cuceni ka cuci rayuwata".

Tukur ya daka mata tsawa yace "get out of my room nonsense banza karuwa".

Arazane Alaweeya ta tashi tana tafiya da k'yar tafice daga d'akin tukur, lek'awa falon gida tayi taga ba kowa tayi sad'af sad'af ta haye upstair d'inta tawuce d'akinta, danno sakata tayi ta shiga band'aki ta d'ora alwala tayi sallah tana mik'a kukanta wajen Allah yasaka mata.

Washegari duk An hallara a dinning banda Alaweeya.

Alhaji ya kalli siyama yace "jeki kiramin auntynki kice tazo muci abinci."

Siyama tanufi d'akin Alaweeya, a kwance ta sameta sai kuka take tana rik'e da kanta..

Ihu siyama tayi tanufi dinning d'in tana "dady Alaweeya zata mutu ku taimaka" duka su Alhaji suka haura upstair d'in har gware suke suka nufi d'akin Alaweeya banda tukur daya tashi yayi gaba abinsa.

Cikin gaggawa Alhaji yakira likitoci biyu, nan da nan sukazo suna bincikar Alaweeya sannan suka gano matsalar dayake damunta.

'Dayan likitan ya kalli Alhaji dayayi tagumi cike da damuwa yace "Alhaji bala, gaskiya rashin lafiyanta yayi tsanani anytime zuciyarta zai buga, kuma munga b.p d'inta yakai 99 _(hawan jini)_ gaskiya abin yaban mamaki, meya damu Alaweeya haka har bugun zuciya harda hawan jini".

Alhaji yashare gumin daya zubomai ya kalli gadon da Alaweeya take kwance ansa mata drip, yace "Nidai ko k'asar turai zan iya fitar da ita indai 'yata zata samu lafiya, Amma ya za'ayi ace yarinya 'yar 21 ta kamu da ciwon hawan jini,me Alaweeya ta nema ta rasa iyeh?"

Likitan yacire glass d'insa yace "Alhaji karka damu in Allah ya yarda zata samu lafiya, amma aguji b'ata mata rai.

Haka likitan suka harhada musu magunguna, suka musu Allah yak'ara sauki suka fice.

Kowa zama yayi yana tunanin meyasa Alaweeya b'acin rai..yarinyar da kullum happy girl ce ga zolaya acikinta.

___________♡♡♡____________
"Dama na kira kane domin in baka wani aiki, dafatan ka iya kisa ko?" Tukur yai tambayar.

Wani basamude ne bak'i k'irin dashi ya kalli tukur dake zaune akan kujerar plastic a wajen shakatawa yace"ai ni Na k'ware awajen iya fashi da kissa shiyasa mutane suke kirana da *sharp bullet*,wa kakeso a kashe maka?"

Murmushin mugunta tukur yayi, ya cire bakin glass d'in dake idonsa kyansa ya k'ara fitowa yace "kasan dai Alhaji balarabe ko?"

Bullet yace "waye baisan Alhaji balarabe ba, kodan taimakon jama'ar da yakeyi dole yayi suna".

Tukur ya gyada kai yace"good to shi nakeso ka kashemin acikin wannan weeks d'in".

Zaro ido bullet yayi yana "haba yallab'ai mutumin dake yawo da bodyguard tayaya zan iya kasheshi".

Tukur yace "indai wannan ne karka damu, nasan yanda zanyi ya rabu da bodyguard d'insa, indai ka kashemin shi kanada million biyar".

Xaro ido bullet yayi yana "million biyar, ai kawai kasa a ranka Alhaji yazama shekakke."

Dariya sukayi suka tafa, sannan suka d'auki kwalbar barasa sukaci gaba dasha.

Mune naku
Yarmama
&

🅱k😘💋
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤*

*TRUE LIFE STORY*

STORY & WRITTING
by

*MARYAM YARMAMA*
*👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*

&
*BILKISU Z.Ya'U(🅱k)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*

Page 21-25

_wannan shafin sadaukar wane ga ANA TARE GROUP_
Mungode sosai muna alfahari daku❤❤
Chapter 2 · 0% Book details