← Book details Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 9

Sashe 7

Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wata daya tukur ya kwace duk wani arziki na wajensu momy hatta kaddarorinta ya kwace..makarantar sadeek da nasu siyama duk ya tsaya gidan yazama wani iri ba hadin kai duk ya tarwatse tamkar ba gidan Alhaji bala ba,kullum kowa na dakinsa ko abinci sun dainaci a dinning saidai kowa yaci nasa
Bari Alaweeya da mutuwar Alhaji ya tabata sosai ko abinci bata iyaci kowa ya gujesu(dama a zamanin nan sai kana dashi)...kuka da tashin hankali bawanda basuyi shiba.
Haka momy tasiyar da gwala gwalanta ta siyo musu kayan abinci karshema duk yan aiki suka gudu saboda ba abinci ishashshe agidan.
Alaweeya tsananin son tukur sai kara tsira yake a zuciyarta...yanzu kwata kwata ya shareta ko ganinsa batayi ,rana daya ta yanke shawarar zuwa ta samesa,dakin ta nufa tana shiga ta gansa akan gado yana zukar taba ,toshe hanci tayi tana karasowa ta durkusa har kasa tana kuka mai tsuma zuciya tace "uncle abinda kamin ka kyautamin ,kwata kwata ka shareni ka manta da wacece alaweeya,bayan kaine namiji daka sanni arayuwa".

A fusace tukur yatashi ya wanke alaweeya da mari yana"ke ai dama tunda basanki nakeba,tunda nasamu abinda nasamu aishikenan,ni wawane duk uban karatun danayi in auri dis-virgin Allah ya kiyaye,tashi ki ficemin daga dakina kafin in saba miki ".nuna mata hanyar waje yayi sannan yaci gaba da zukar tabansa,Alaweeya dake dafe da kunci hawaye masu dumi na zuba a idanuwanta don tunda take a rayuwarta ba'a taba marinta a rayuwaba..amma yau uncle ya mareta tashi tayi tana kuka mai tsuma zuciya....ficewa tayi daga dakin tana zuwa falo su momy suna zaune duk sunyi tagumi...autace kawai take bacci...amaine ya tahowa alaweeya tafadi kasa tadinga kwarara amai falon tamkar hanjinta zaifito.

Siyamace ta tashi ta taimaka mata ,momy takalli alaweeya cike da tashin hankali tace "alaweeya watanki nawa bakiga period dinkiba".

Alaweeya duk ta galabaita dakyar ta budi baki tace" na wata biyu ne kenan".

Arazane momy tamike tana kuka "alaweeya kin cuceni,ciki?innalilahi wayamiki ciki?ki gayamin".

Rudewa siyama tayi tana kallon aunty alaweeya tace "dagaske ne sister,please momy karkice haka sister fa bahaka takeba".

Yaya Yusif ya fusata yayo kan alaweeya yana jibga yana "zaki fada mana ko saikinci ubanki iyeh haba Alaweeya dame zamujine".

Cikin kuka alaweeya tace "wallahi uncle ne uncle tukur ne,shine".

Dafe kirji momy tayi tana kiram sunan Allah "Alaweeya ki rasa wanda zakiyi tarayya dashi sai uncle,wallahi nayi nadamar haifuwarki..momy tasa kuka tana "oh Alhaji kadawo duniya mana kaga bakincikin da yarka ta kunsamin yanzu";

Sadeek zubewa yayi akan kujera shima cike da tashin hankali yake bin alaweeya da kallo .cikin kuka alaweeya tace "momy kiyi hakuri ba laifina bane,wallahi yaudarata yayi.inason uncle,shine nabashi hadin kai dayamin alkawarin zai aureni".

Kara siyama tayi ta rushe da kuka mai tsuma rai wanda ya fargar da auta daga barci....duka falon suka rushe da kuka,kowa kuka yake mai tsuma rai....sai yau alaweeya tayi nadamar abinda ta aikata,taji ta tsani duniyar ma gabaki daya".

Tukur ne ya sakko daga bene yasha kananun kaya...sai fesa kamshi yakeyi..sanye yake da glass dark spackle ,yana isowa falon yaga kowa sai durzar kuka sukeyi tamkar ransu zai fita ,tsawa yadaka musu "ku mahaukatai ,meye kuka cikamin gida da kuka .au dan namuku alfarma kuna zama acikin gidan shine zaku dameni da kuka".

Bawanda ya saurareshi sai yusif dayatashi cike da zuciya yayi gaba da gaba dashi yace"wallahi baka cancanci zama ubanmu ba kaci amanar dady kasaka mu acikin bakin ciki ,kai azzalumine.kuma fasiki,kuma dole ka anshi cikin da kawa kanwata ko kanaso ko bakaso ko kuma duniya tajimu".

Kyalkyalewa da dariya uncle yayi yana "yaro yaro ne,kai yaro ka iyewa bakinka ni nafi karfin inkula yayarka kazama kuchaka da ita"taje can ta nemi uban danta...kuma daga karshe zance muku congratulation issa goal⚽".

Kukan kura yusif yayi "heeeeeey .munkai kararka kotun Allah ..Allah shi zai saka mana ".

Ko kallonsu tukur baiyiba yayi ficewarsa daga falon yana dariyar mugunta..

Haka sukaci kuka suka gaji,ga tunanin mutuwar alhaji komai ya cabe musu .

Tamkar yau Alhaji ya mutu suka dinga kuka daga karshe momy ta rungumi kaddara ta hada kan yayanta suka dinga kuka mai tsuma rai.

Allah sarki rayuwa

Mune naku

🅱k
&
Yarmama💋💋
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤*

*TRUE LIFE STORY*

STORY & WRITTING
by

*MARYAM YARMAMA*
*👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*

&
*BILKISU Z.Ya'U(🅱k)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*

Page 61-65

_wannan page din mun sadaukarwa da duk masoyanmu .muna ta ganin sako da adu'o in da kukeyiwa Alhaji .komin rashin imaninka dole ,ka tausayawa rayuwarsu Alaweeya 😭😭dan Allah kudinga yiwa Alhaji bala adu'a_

*ZAMANI WRITTERS ASSOCIATION*

________________________________

Haka suka share satukan ba walwala balle farinciki ...momy ce ta tuka musu tuwo miyar kuka.dama tunda alhaji ya rasu basu karacin abinci a dinning ba saidai suci a falo.

Autace ta kalli tuwon tafashe da kuka don tunda take a rayuwarta bata tabacin tuwoba

Momy ta kyalleta tace "lafiya auta saidai fa kiyi hakuri babu abinda ya rage a gidannan sai garin tuwo shima nayaune kawai".

Siyama cike da tausayawa takalli sadeek da yusif da suke ta laftan tuwon ko ajikinsa tasa hannu itama tafaraci...momy tace auta jeki kiramin alaweeya tazo taci abinci...aguje auta ta tashi tanufi hanyar dakin alaweeya....ji sukayi an cillo auta daga sama bene bakowa bace fyace karuwar uncle tukur tasha attachment taci bleeching tana kallon yanda auta humaira ta fado daga kan bene ta yamutse fuska .

Dasauri sadeek da momy suka nufi inda auta take kwance babu alaman numfashi a tattare da ita ga jini yana zuba a hancinta harda kunnenta.haka yayi daidai da fitowar alaweeya daga dakinta .takama karuwar uncle da kokowa saida tawa budurwar tukur dukan tsiya harda jini da majina sannan ta barta..aguje tasakko batare data damu da cikin dake jikinta ba.tadauki auta tana kuka tafice waje su momy suka rufa mata baya..wajen motocin gidan suka nufa amma babu key ko daya nan suka tuna ai tukur ya kwace duk key din motocin gidan.

Gate suka bude suka fita suka hau adaidaitasau sai asibitin da alhaji yake kaisu suka nufa..

Cike tausayawa likitan yakalli momy yana "matar alhaji ce wannan oh duniya,Allah yajikan alhaji".

Kuka momy tasa mai tsuma rai har haka shiga da auta emergency.sai bayan awa biyu aka fito da ito akan gadon marasa lafiya ana turota kanta da hannunta daure da bandages aka turata zuwa dakin marasa lfy ,likitan ne yafito yace momy ta biyosa ,momy da alaweeya ne suka biyosa suka zauna a office din.cike da mamaki likitan yakalli cikin alaweeya daya fito.domin daga ita sai dogan riga ko dankwali batasa ba,gashinta yayi buzu buzu yace "a .a dama alaweeya kinyi aurene".

Sunkuyar dakai alaweeya tayi tana share hawaye yayinda momy itama tayi shiru .
Likitan ya kawar da zancen da cewa "ku kwantar da hankalinku zata samu sauki karayace kawai da buguwar kai datayi wanda tana bukatar tasamu hutu sosai..karku damu da kudin magunguna ,kubarshi domin alherin da alhaji yamin bazan taba mantawa dashiba.

Godiya sukayi harda kuka
Sati uku suka shafe a asibitin sannan suka koma gida..domin auta tasamu sauki har tana iya tafiya.

..zaune suke a falon sunyi shiru bama t.v balle suyi kallo domin tukur ya siyar .kowa yana tunanin rasuwar Alhaji mai dauke musu kewa,abba mai jansu ajiki mai sasu farinciki

Alaweeya ce take yanke farce tana tuna abbanta da yanda yake kaunarta .duka taji yasauka a bayanta juyowar da zatayi taga uncle ne ga budurwarsa abaya ta rike kugu...

Suma momy suka bisa da kallo

Mune naku

🅱k
Nd
Yarmama😍💋💋
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤*

*TRUE LIFE STORY*

STORY & WRITTING
by

*MARYAM YARMAMA*
*👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*

&
*BILKISU Z.Ya'U(🅱k)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*

Page 66-70

Bata ankaraba taga uncle ya mareta dafe kunci tayi tana karemai kallonta kafin tayi wani kwakkwaran motsi tukur yasa kafa yayi ball da ita yanata jigganta harda taka mata ciki.kuka take tana bashi hakuri ta kiran sunan Alhaji

"Wayyo dady meyasa ka tafi kabarmu da azzalumi?meyasa kabashi amanarmu,dady ka dawo !ka dawo"

Tukur yana huci yace "ai baki ga komai. in karasaki banza a banza in huta,akanme zaki dukarmin matar dazan aura saikace kinsamu jakarki". siyama dake zubda hawaye tace "au ita budurwar taka ba jefo auta tayi daga kan upstair ba,danma Allah yasa auta tanada saurin numfashi a duniya".

Wangalau yusif yayi zuciyarshi na taffasa ga momy sai kuka take yabude baki.abinka damai karfi..yayiwa tukur naushi har jini yana zuba a hancin tukur ,kara tukur yayi ya taba jinin dake hancinta ya kalla yaga ai jinine.tuni yakama yusif da kokawa ,momy dai suna zaune suna kallon duk abinda ke faruwa...da tukur yaji duka iya duka tuni ya arce dakinsa budurwarsa ta rufamai baya..

Karar alaweeya sukaji dake kwance a kasa.ihu take tana rike cikinta ga jini yanabin kafafunta😭😭....cike da tashin hankali momy ta rike alaweeya tana "alaweeya lafiya,bleeding kuma,yusif ku taimaka mu kaita asibiti".

Suka ciccibi Alaweeya suka fito da ita bakin titi tanata bleeding(zubar da jini)tamkar anbude famfo sai jijjiga takeyi idon nan nata ya koma fari fat.

Adaidaita biyu suka tara suka nufi asibiti da ita ,cikin gaggawa aka amshesu akayi emergency room da ita.

Momy sai kuka suke domin yanda sukaga halin da Alaweeya takr ciki dole zuciyarshi ta karaya.

Likitan ne ya fito duk yahada gumi ya kalli momy yace"kune iyalan Alhaji margayi bala Alaweeya tana son magana daku duka".

Duuuuu momy sukabi bayan likitan suka shiga dakin da aka kwantar da Alaweeya.halin da alaweeya keciki ya isa yasa a zubar mata da hawaye har yanzu bata daina bleeding ba saidai ta daina jijjigan.

A hankali momy suka karasa bakin gadon .momy ta rike hannun Alaweeya data kura mata ido tana mata murmushi tace"Alaweeya dafatan kin fara samun lafiya,Allah ya tashi kafadunki".

Murmushi Alaweeya tayi duk da tanajin zafin ciwon a hankali ta kalli momy tace"momy karki damu zamu hadu ko ba yanzuba,inaso inga Alhaji inason zama dashi,don Allah ki yafemin duk abubuwan dana miki,yanda nakeji a jikina tamkar bazan rayuba nidai na yafewa kowa".

Kuka siyama ta fashe dashi tana"haba aunty Alaweeya kidaina fadar haka zaki mike da yardar Allah".

Alaweeya tayi yar dariya mai cike da ciwo ta mikowa auta hannu alamar tazo zuwa auta tayi Alaweeya tace "auta zanyi kewarku,ina da tafiya mai nisa a gabana,ina sonku i wish happy family forever.Alaweeya ta kawarmusu da hawayensu tahanyar basu abin dariya".
Chapter 7 · 0% Book details