← Book details Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 9

Sashe 4

Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_BK da 'YARMAMA suna ganin haka, suka fice daga gidan a guje, k'afa me naci ban baki ba, saida suka isa gida sannan suka tsaya suna numfarfashi, YARMAMA ta kalli BK tace "ashe Tukur d'an iska ne," BK tana haki tace "au ke se yau kika sani."😂_

Muje zuwa

Mune naku

*'YARMAMA*
&
*🅱K😘💋*
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU 🖤🖤*

*TRUE LIFE STORY*

STORY & WRITING

*MARYAM 'YARMAMA*
*👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*

&

*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*

Page 31-35

Washe gari ranar lahadi kenan, suna zaune ana hira sai ga Tukur ya shigo d'akin ya zauna, yaran gabad'aya sun saka Dady a tsakiya suna zuba shagwab'a, Tukur kuwa banda harararsu ba abinda yake yi.

Alhaji ya ciro key d'in mota ya kalli Tukur yana murmushi, sannan ya mik'a mishi yace " yau dai Allah ya yi na cika alk'awarin motar da na d'aukar wa kaina zan siya maka," Tukur ya mik'a hannu ya karb'i makullin motar tare da yin godiya, ba wani nuna tsantsar murna a fuskar shi sosai duk da kuwa irin motar da yake mafarkin mallaka aka siya mishi.

Yusuf da Alaweeya har suna had'a baki wajen fad'in " Dady mu sai yaushe zaka siya mana?"

Alhaji yai murmushi, sannan yace " duk tare na bada izinin ayo muku odarsu, ta Uncle d'inku ce ta fara isowa, kuma nasan taku tana hanya."

Cike da tsananin farin ciki mara misaltuwa suka ce " to Dady mun gode Allah k'ara maka bud'i."

Dady ya kalle su yace " ameen yarana, babu abinda bazan iya yi muku ba a rayuwa muddin inada halin yi, kuma wanda be sab'awa koyarwar addinin islama ba, maza kuje ku shirya mu fita, yau zan kaiku wajen da kuka fi so ku siya duk abinda kuke da buk'ata, daga nan ku turomin Mumyn ku."

Suka amsa da " to " kuma dukkan su suka tashi a tare kowanne yana rige-rigen zuwa shiryawa.

Tukur kuwa b'acin ranshi da tsantsar bak'in cikin da zuciyar shi ke ciki ya kasa b'oyuwa, sam ya tsani yaga Alhaji na fitar da kud'i ya bayar ko ya siya wani abu ya bayar.

Kuma ya tsani yanda yake shagwab'a yaran nan, ko menene suka buk'ata sai ya d'auki kud'i ya basu, hakan yafi komai k'ona mishi rai.

wata k'aramar tsaki yaja wadda sam be san da fitowarta fili har Alhaji yaji ba.

Alhaji ya kalli Tukur yace " d'an'uwa yadai, akwai abinda kake da buk'ata ne?"

Tukur yace " babu, sedai inada 'yar shawarar da zan bayar."

Alhaji yace " to ina jinka."

Tukur yace " gaskiya be kamata ana shagwab'a yaran nan haka ba, nan gaba ne abun ji, ka dena cewa duk abinda suka tambaya sai ka yi musu."

Alhaji ya yi murmushi, sannan yace " Tukur kenan maganarka hakane, amma yaran ka sunada kyakkyawar tarbiyya wadda nake Alfahari da ita a ko'ina, kuma abinda yasa nake basu komai shine saboda kar hanasun ya jefa rayuwarsu cikin wani hali suje suna nema a waje ta kowane hali, sannan dukiyar nan inada ita, menene amfaninta in har ban wadata iyalina da ita ba, ko kaga canjin d'abi'u ne ko canjin hali a tare dasu?"

Tukur yace " a'a gaskiya, ban gani ba," shi kanshi saida yai maganar sannan daga baya yai tunanin kar Alhajin ya fara zargin wani abu asirin shi ya tonu.

Shi kuwa Alhaji be fahimci komai ba, harga Allah shi dad'i ma yaji yanda ya nuna ya damu da rayuwar yaran.

Alhaji yace " naji dad'i yanda ka nuna ka damu da rayuwar yaran nan, hakan ya tabbatar min da cewa ko bayan ba raina zaka kula min da tarbiyar su."

Tukur ya saki ajiyar zuciya tare da murmushi na jin dad'in Alhaji be kawo komai ba, a zuciyar shi kuwa fad'i yake gwara ka rik'a tuna mutuwar kam dan kana gaf da tafiya, a fili kuwa cewa yai " Yaya ai yaranka kamar yaran da na haifa ne."

Alhaji ya mik'e sannan yace "kaje ka shirya, zamu fita gaba d'aya."

Tukur yace "Alhaji kuje kawai akwai aikin da zanyi ne da na biku."

Alhaji yace "to ba damuwa, bari naje na shirya kafin su fito su fara rigima, Tukur yai dariyar yak'e, sannan yace " ok gaskiya kam gwara ka shirya kafin su fito."

Alhaji na juyawa Tukur ya bishi da wata harara wadda shi ya barwa kansa sanin dalilin yinta.

Washe gari ranar litinin kenan, Alaweeya ta tafi makaranta, bayan an taso su kan hanyarta ta dawowa sai wayarta ta fara k'ara alamar ana kiranta.

Ganin wanda ke kira yasa ta d'aga tare da karawa a kunne, can d'aya b'angaren Tukur yace "kina ina?"

Alaweeya tace "gani a hanya zan koma gida, nan ya fad'a mata yana da buk'atar ta dai-dai wannan lokacin, ta tsayar da napep d'in, bayan ta sallami me napep d'in ne sannan ta kwatanta mishi, dai-dai inda take.

Babu b'ata lokaci kuwa sai gashi ya iso a cikin sabuwar motar da Alhaji ya siya mishi.

Nan da nan ta shiga Tukur yaja sai bakin wani had'ad'd'en hotel me matuk'ar kyau da tsada.

Parking suka yi, sannan suka fito daga motar suka shiga ciki.

Alhaji ne zaune cikin k'ayataccen office d'inshi yana cike wasu takardu, wayar shi ta d'au k'ara alamar ana kiran shi, bayan ya d'aga ne ake shaida mishi ana jiran shi yanzu bak'in shi sun iso suna hotel yaje ya same su suyi meeting d'in a can saboda suna so in an gama da wuri su koma yau d'innan.

Bayan ya gama wayar ne nan da nan Alhaji ya aje duk wani Abu da yake yi ya fito ya shiga mota aka jashi sai hotel d'in da bak'in shi suka sauka a ciki.

A dai-dai lokacin da motar Alhaji ta kutso cikin harabar hotel d'in a dai-dai ta su Tukur da Alaweeya zata fito ita kuma.

Alaweeya ta saki salati tare da zaro ido, tace " na shiga uku Dady!!! yau asirinmu zai tonu ," Tukur ma ya kalli inda take kallo yaga Alhaji, shima ya zazzaro idanu.

Muje zuwa

Mune naku

*YARMAMA*
&
*(🅱K)😘💋*
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤*

*TRUE LIFE STORY*

STORY & WRITTING
by

*MARYAM YARMAMA*
*👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*

&
*BILKISU Z.Ya'U(🅱k)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*

Page 36-40

Kasa sukayi dakai ,sukaja motar a matukar guje,wanda Alhaji kawai kurar motar yagani.

Dariya Alaweeya tayi najin dadi ta kalli tukur kaunarsa nakara shiga ranta tace"uncle Allah fa ya taimakemu'saimu canza hotel".

Dariya tukur shima yayi azuciyarshi yana "ai gobe goben nan ubanki zai je lahira kuma anan zaki fuskanci wulakanci" afili kuma yace"aikwa tamkar kinsani".

Adaidai kwanar layinsu tukur ya faka motarsa ,Alaweeya tafito tana rausaya,shiko tukur yajuyar dakan motarsa yayi.

Yayinda Alaweeya ta kwankwasa bakin gate dinsu maigadi yabude mata yana kwasar gaisuwa ,amsawa tayi tashige babban falo ta zauna tana dariyar farinciki.

Momyce tashigo falon taci uban kwalya tana"su manyan arewa northern people,har antashi da school".

Tashi Alaweeya tayi ta rungumi momy tana"oh momy i really miss you so much".

Bata gama rufe bakiba Alhaji yashigo yusif na biye dashi da gudu taje ta rungumeshi ga bodyguard sun ruko gana must go guda uku,direshi sukayi a falon suka fice yayinda Alaweeya tanufi wajen da Alhaji yaxauna ta rungumesa tanamai shagwaba.

Yusif ya kalleta ya mata hararan wasa yace"baby doll katuwa tashi daga cinyar dady,karki ballamai cinya,ko auta bata abinda kikeyi wallahi".

Momy tace "rabu da ita,ai tana gama graduation zamu fitar mata da miji tunda kullum acikin wulakanta samari take,hatta yayan senetors".

Alaweeya ta kalli Alhaji tamkar zatayi kuka tace"dady ka gansu ko".

Alhaji ya kalli momy yace "au tarar dangi zakuwa yata ko,dama yau da daddare akwai dan meeting din da xamuyi daku gabaki daya,yanzu wannan gana must go din da kuka gani kudine wajen miliyan goma sha biyar za'akai asibitoci da gidan marayu hatta gajiyayyu a raba musu na fidda zakka".

Cike dajin dady momy ta kalli Alhaji tana "Allah sarki dadynmu ubangiji Allah yabiyaka duniya da Lahira"......bata gama rufe bakinta ba tukur yashigo gidan a matukar buge yasha yabugu yana zuwa falon yafara ihu da sowa yana magana irin tayan maye.

Alhaji yaji hawaye yana kokarin zubomai ya kalli tukur yana"tukur yanzu kayi daidai ,meye amfanin wannan rayuwar".

Tukur yayi gyatsa cikin murya ta yan maye yace"Alhaji komai is normal,normal nake".

Tashi Alhaji yayi yakama hannunsa yakaishi dakinsa yaragemai kaysn jikinsa ya kwantar dashi barcine mai nauyi ya kwashesa,kallonsa Alhaji yadinga yi cike daso da kauna,yadinga kwararo adu'a yana tofamai.
Sannan yaja kofar yafice yasakko falon ya tadda su momy kowa yayi shiru.

Da daddare an hallara a falon harda tukur nasiha Alhaji yake musu yana

"Tukur kaine babba yanzu,kona mutu kaine zaka rike gidannan"tukur ya kalli Alhaji a ransa yana "aiko baka fadaba mutuwa gobe gobe".

Alhaji yacigaba yace"dukiya takuce dukanku,tukur yakamata kayi hankali ka nemo mata,.ka tuna duniyar nanba komai bane,kekuma Alaweeya bayan graduation dinki as barrister saiki fito da miji domin yanzu kin girma ,nasan bazaku taba bani kunyaba domin kunsamu tarbiyya daga uwa tagari,ilimin boko Allah yabamu hakama na addini kunadashi,nidai nasan ko yau na mutu banda hakki akan kowa".

Momy tace "Alhaji me kuma yakawo wannan maganar,bazaka mutuba muna tare pls kabar maganar nan".

Harara tukur ya dankara mata yatashi yana"saida safenku yahaye sama"

Wayar Alhaji ne yayi ruri dauka yayi ,murya ta Alhaji lawan wanda suke meeting tarene ya gayamai gobe sunada meeting karyazo da bodyguard kawai da driver zaizo saboda meeting din sirrine,batare da aiyana komai a ranshiba Alhaji ya yarda,haka kowa yamike suka junansu sumba kowa ya wuce makwancinsa suna kewar juna.

Tukur ne adakinsa yana zaune akan gado yana waya yace"sharp bullet karku kuskura ku barsa da ransa,tunda harda drivern muka hada baki ,shi karku kashesa kawai ku harbesa akafa kar mutane sugane,i repeat karfa asamu wata matsala yayana ne uwa daya uba daya eh".

Kashe wayar yayi ya kwanta ya kyalkyale da dariya yana"sabuwar duniya nakusa inzama billonier inyi facaka da dukiya".

Mune dai naku kullum

🅱k💋

Da yarmama💃❤
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU 🖤🖤*

*TRUE LIFE STORY*

STORY & WRITING

*MARYAM 'YARMAMA*
*👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*

&

*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*

Page 41-45

Bayan kowa ya tafi makwancin shi Tukur ya kasa zaune ya kasa tsaye, banda zirga-zirga cikin d'akin shi ba abinda yake.
Chapter 4 · 0% Book details