Sashe 1
Zuciyar Mugu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU*🖤🖤
*TRUE LIFE STORY*
WRITING BY
*MARYAM 'YAR MAMA*
*ZAMANI WRITER'S*
&
*BILKISU Z. Ya'U (🅱K)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
_Bismillahir rahmanir raheem_
_*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH (S.W.A) DA YA ARA MANA RAYUWA DA LAFIYA, YA UBANGIJI MUNA GODIYA A GAREKA👏*_
_*YA UBANGIJINMU KA YI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)*_
*KAMAR YANDA KUKA GANI A SAMA👆 WANNAN LABARIN YA FARU DA GASKE, ZALUNCI, BUTULCI, CIN AMANA, YAUDARA, TSANTSAR TAUSAYI, DUK A CIKIN WANNAN LABARIN, SAI KU BIYO MU DOMIN JIN ABINDA YA K'UNSA.*
Page 1 to 5
Alhaji Balarabe nera shahararren mai kud'i ne, nagartaccen mutum ne, mutum ne mai yi wa mutane hidima, wanda sam dukiyar shi bata rufe mishi ido ba, akwai taimakon na k'asa da shi, baya k'yashin fitar da dukiyar shi ya taimakawa talaka, ga kyauta a tak'aice dai Allah ya had'a mishi duka biyun, ga dukiya me tarin yawa, ga kuma hali na k'warai.
Alhaji yana da mata d'aya mai suna Hajiya Jameela, suna da yara biyar, akwai Yusuf, sai Alaweeyya, sai Seeyama, sai sadeeq, Sai auta me suna Aisha.
Alhaji da Hajiya wato iyayen su Alaweeya suna matuk'ar k'aunar yaran su, ko kad'an basa yarda wani abu ya tab'a yaran, suna samun kyakkyawar kulawa daga cikin gida yar a waje, idan suna cikin gida babu abinda suke yi na wahala komai se a yi musu, kuma babu abinda suka nema suka rasa komin tsadar sa, a waje kuwa, duk inda zasu saka k'afa to da masu tsaron su, a tak'aice a koda yaushe kuma a ko'ina yaran suke suna k'ark'ashin kulawar mahaifin su.
Wannan tsantsar k'aunar ita ta haifar da shak'uwa mai tsanani a tsakanin yaran da iyayen, dukkanin su yanzu haka suna karatu a fitacciya, kuma shahararriyar makarantar da ta yi fice saboda kyanta da kuma shahararta, masu karatu cikinta kuwa sai 'ya'yan manya, wato 'ya'yan attajirai, wannan kenan.
Yau Asabar ranar hutu ce, Dadyn su yana gida ba inda ya je, zaune yake tsakiyar yaran shi, banda zuba mishi shagwab'a ba abinda suke, Alaweeya ce tace " Dady dan Allah a fita da mu, mu yi shopping," Seeyama tace " A'a Dady wajen wasa zaka kai mu," Yusuf yace " Dady rabu dasu sarakan son yawo kawai, " Aisha auta cikin maganarta ta yara tace " Dady dan Allah muje zansha sweet, wanda ka siya mun sun k'are, suna cikin magana kafin Dady yace komai sai ga Mumy ta shigo falon inda suke zaune ta k'araso itama ta zauna, kallon yaran ta yi, sannan ta kalli Alhaji tai murmushi, tace " Dadyn mu me ake tattaunawa ne ba'a nemeni ba?" Dady yai dariya, sannan yace " yaranki ne suka dage a fita dasu yau su yi siyayya," Mumy tace " ai kai ka saba mana da hakan, duk lokacin da kake gida kana fita da mu, dan haka yau ma a fita da mu ko muita yi maka kuka ko ba haka ba yarana? " ta juya tana tambayar yaran, kamar had'in baki a tare suka amsa suka ce " yes Mum. "
Dady ya yi dariya yace " wato kece kika shagwab'a min yara koh? "
Mumy tace " wa, ni? ba ruwana kai ne ka shagwab'a mu dukkan mu har da ni," Dady ya kalli yaran yace " to yanzu abinda za'ai kowa yaje ya d'auko litattafan shi gaba d'aya ku biya mun d'aya bayan d'aya, duk wanda ya karanta lafiya lau to da shi zamu tafi," da gudun arzik'i suka tashi gaba d'ayan su, zuwa d'auko litattafan nasu banda Yusuf da Mumy, Dady ya kalli Mum da Yusuf yace " Ku bazaku bimu ba kenan? "
Mum tace " au wai har da ni?"
Dady yace " ai har da ke na shagwab'a, dan haka kema Allah sai kin yi karatu zamu fita da ke, ya kalli Yusuf yace kaima kaje ka d'auko naka litattafan."
Da yake Yusuf ya san be iya nashi karatun ba sai yace "Dady kuje kawai ni ba zan je ba," Dady yace " d'auko littafan ka karanta in baka iya ba to dole sai mun fita da kai tunda fitar ce yau baka so."
Sai da kowa ya karanta litattafan shi daga na boko har na islamiyya, Mum kuwa Qur'ani ya sata ta karanta, sannan bayan sun gama karatun dukkan su suka shirya harda Dady suka fita, ba su suka dawo gida ba sai da yamma wajen k'arfe biyar da rabi.
Suna dawowa bayan sun yi sallar magriba da isha'i sannan suka had'u suka ci abinci, suna cikin cin abincin ne sai wayar Dady tai k'ara, yana dubawa yaga Tukur ne ke kira, da saurin shi ya d'aga fuskar shi d'auke da murmushi, bayan sun gaisa Tukur yace " dama mun kammala karatu ne shine nace bari na kira in fad'a maka a turo min da kud'i zan taho gida nan da sati d'aya."
Dady yace " anya, ai shekarun da zasu d'aukeku har ku gama karatun basu cika ba da sauran shekaru Tukur fad'a mun gaskiya dai. "
Tukur yace " sun rage shekarun ne, in baka yarda ba ka tambayi abokina, gashi a kusa da ni."
Alhaji yace " shikenan Allah ya kaimu, zan turo maka da kud'in, zan yi maka transfer, suna kammala wayar yai mishi transfer a take anan.
Yaran gidan kuwa da ita kanta Mumy jikinsu duk ya yi sanyi jin Tukur zai dawo, da yake wayar Alhaji akwai k'ara, idan yana waya ana jin komai, shiyasa duk hankalin su ya tashi, in suna k'aunar dawowar shi to suna k'aunar mutuwar su haka.
_topha, wai wanene wannan Tukur d'in? Menene matsayin shi cikin wannan dangin? Meyasa kowa baya farin ciki da dawowar tashi? Ku biyo mu domin jin ci gaban._
Mune naku
*'Yar mama💃*
&
*🅱K😘💋*
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU*🖤🖤
*TRUE LIFE STORY*
STORY & WRITING
BY
*MARYAM 'YAR MAMA*
*ZAMANI WRITER'S*
&
*BILKISU Z. Ya'U (🅱K)*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
_Bismillahir rahmanir raheem_
Page 5 to 10
WANE NE TUKUR?
Tukur k'ani ne ga Alhaji Balarabe nera uwa d'aya uba d'aya, kuma tun yana k'arami yake zaune a hannun Alhaji Balarabe.
Tun Tukur yana jariri Allah ya d'auki ran iyayen su.
Alhaji Balarabe yana matuk'ar k'aunar d'an uwansa.
Gata kam na duniya babu irin wanda Alhaji bai wa d'an uwan shi tukur ba, tun baida komai har Allah ya azurta shi da dukiya me tarin yawa.
Lokacin da Tukur yai wayau Alhaji Balarabe ya sa shi makarantar boko da ta islamiyya, se dai tun yana yaro tukur baya ji, kuma sam baya maida hankali kan karatun shi, ga neman fitina da tsokana kala-kala.
Alhaji ya kammala karatun shi cikin nasara, domin yana gamawa ya sami aiki me kyau, wanda farawa da iyawa Allah ya sawa dukiyar shi Albarka taita bunk'asa.
Lokacin da ya fara aiki ne Allah ya had'a shi da 'yarinya ta gari ya yaba da tarbiyarta da natsuwarta, had'i da iliminta, hakan yasa suna dai-daita kansu babu b'ata lokacin aka sa rana.
Bayan an sha biki amarya ta tare.
Tunda amaryar Alhaji ta shigo gidan nan hak'urin zama kawai take yi da tukur ga rashin kunya da nuna gadara a kan komai na cikin gidan.
Amma da yake hak'urarra ce bata tab'a kai k'arar shi wajen Alhaji Balarabe ba, se dai in ya yi a gaban Alhajin ya gani sannan zai kwab'a mishi, duk da bema cika yi mata ba idan Alhaji na gida sai baya nan, tunda yana d'an jin maganar yayan nashi.
Bayan 'yan kwanaki Alhaji Balarabe ya kai shi wata makarantar kud'i me kyau, se dai sam baya maida hankali a karatun, hakan yasa yai tunanin canza mishi makaranta a tunanin shi ko be gane karatun ne, sai ya zamana kamar ma 'yanci da dama ya samu na shek'e ayar shi, dan yanzu har shaye-shaye yake yi.
Haka rayuwar su ta ci gaba da kasancewa kwata-kwata Matar Alhaji Balarabe bata jin dad'in zaman Tukur a tare da su, gashi ya saka musu ido, ga kishi duk abinda Alhaji yai musu sai ya nuna kishi da hassadar shi a kanta.
Kuma ya tsani yaga Alhaji na facaka da dukiyar da Allah ya bashi, kuma baya k'aunar yaga yana taimako da ita.
A haka har Allah ya azurta su da yara har biyar, se dai har lokacin halin Tukur be canja ba, sai ya zamana tsangwamar har da yaran Alhajin yake yi mawa, ya tsani shak'uwar da suka yi da Alhajin, sannan makarantun da duk aka sa shi daga k'arshe koro shi ake yi, wad'anda suke da lambar Alhaji Balarabe kuwa sai su kira shi su fad'a mishi zai b'ata musu tarbiyyar yaran makaranta shiyasa suka sallame shi.
Alhaji ya yi fad'an har ya gode Allah, bayan kwana biyu Tukur da kan shi yazo wa da Alhaji magana akan yana so ya tura shi waje karatu, Alhaji yace bazai yiwu ba anan d'in ma ya aka k'are balle ya fita waje, sai Tukur ya nunar mishi da muddin ya kaishi can zai dage yai karatu, Alhaji yace in har yana so ya kaishi waje sai ya maida hankali anan ya gama secondary school d'in shi yaga ya fitar da sakamako mai kyau sannan zai yarda da buk'atar shi, koda Tukur yaji haka yace ya amince, aka saka shi wata makarantar, ikon Allah kuwa ya dage da karatu ba dare ba rana, kuma daga k'arshe kuwa ya fitar da sakamako mai kyau, hakan yasa dole Alhaji ya cika mishi alkawarin shi domin harga Allah a tunanin shi yanzu kuma yana son karatun ne, wannan shine dalilin fitar da shi waje, daga uwar gidan har yaran gidan tsoron shi suke ji sam basa farin ciki da dawowar shi, shi kanshi Alhaji ya ji sak'at da baya nan, amma ya zai yi naka sai naka, wannan kenan.
CI GABAN LABARIN
Muje zuwa
Mune naku
*'YAR MAMA*
&
*🅱K😘💋*
[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤*
*TRUE LIFE STORY*
STORY&WRITTING
by
*MARYAM YARMAMA*
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*
&
*BILKISU Z.Ya'U(🅱K)*
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
Page 11-15
Washegari Alhaji yasa driver yaje ya dakko tukur a airport,tukur kyakyawan yarone ajin farko,abinka da fulani farine kuma dogo mai faffadan kirji gashi da sexy eye,yanada tarin suma wanda kullum cikin gyara sumar yake,.yanayin shigarsama ya nuna tantirin yarone..