← Book details Zafin Wuta Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 9

CHAPTER 35-40

Zafin Wuta Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 17 min read

Ajiyar zuciya Pahpah ya saki lokacinda Sulaima ta kashe wayar, kallonshi farin mutum da ke zaune kan sallaya tai tare da girgiza kai sannan ya ce.
"Mudin haskenta ya sadu da
anka tabbas
arshen wahalarsa ya zo, ita ka
aice za ta iya karya wannan mugun sihirin, sannan kuma ta bashi garkuwa da izinin ubangijinmu."
Shiru Pahpah yai tare da zurfafa a cikin tunanin yanda zai sadu da wannan tauraruwa me haske, wacce zata zamo tsanin takawar Fauzan ta hanyar samun lafiyarshi.
"Ka tashi ka je, kana tare da nasara, ka ri
e Allah domin shine ka
ai zai tallafa maka."
Wani abin al'ajabi da bammamaki, mutumin na gama maganar sai ya
ace
at kamar be ta
a wanzuwa a wajen ba.
Tsam Pahpah ya tashi ya fice cikim tsoro, direct wajen motarshi ya nufa, bayan ya shiga ya saka drivar ya ja da sauri suka bar wajen.
MUBEENAH AGEGE
Can cikin barci ni ke jiyo muryar Mama sama-sama, ban bu
e ido ba sai juyi da na sake yi ina shirin gyara kwanciyata, sai na ji an jijjiga ni da
arfin gaske ana fa
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, jama'a Mubeenah wai lafiyarki
alau kuwa? dan Allah ki tashi hakanan, rana har ta fito amma kin gagara tashi, tun asubahi nike tashinki."
Zaram na tashi zaune tun lokacin da na ji salatin da Mama ta saki, cikin sauri na bu
e idanuwana, amma abin mamaki shine, sun bu
e tar amma sam bana ganin komi, sake kai hannuna nai ina shafa idon dawa, amma abin al'ajabi sai naji ashe a bu
e suke.
"Allahu Akbar, kaji
udirar Ubangiji mabuwayi gagara misali, me hanawa kuma me bayarwa, Wallahi Allah Mama idanuwana basa ganin komi, duhu nike gani, zo ki duba ki gani."
Nai maganar cikin jinjina
arfin buwayar Ubangiji, me bayarwa kuma me hanawa aduk lokacin da ya so, idan ba Ikon Ubangijiba waye zai baka alokacin da ya so, kuma ya amsa a lokacinda ya so?.
"Ke Mubeena ban son iskanci, ta gidan ubanwa ke baki gani, alhalin ga idanuwanki nan tarrrr ma sha Allah, ki daina wasa ki taso muje kiyi sallah lokaci na wucewa."
Mama tai maganar ta na hana kanta gasgata cewa da nai bana gani.
"To Mama bara in tashi."
Nai maganar ina
arin tashi, amma mi ta tabbata dai bana gani sam, dan kuwa ina taka
afata ban sauke ta a ko ina ba sai cikin kwanon da nike aje ruwa idan zan kwanta, cike da razani na janye
afata nai baya ina salati.
Sak Mama ta yi, ta kasa ta
uka komi domin kuwa ko ta so ko kar ta so ya tabbata bana gani.
Maganar Abba ce ta yanke min jimamin da na shiga.
"Ke Halima! wai har yanzu ita Mubeenar ba ta tashi ba, ki watsa ma ta ruwa manah, kinga rana ta soma yi, kuma ana jiranmu dan yanzu na sake yin waya da Hashimu ya sanar da ni cewa, me gidan ya dawo jiya cikin dare, muyi sauri muje dan...."
Maganarshi ta yanke ne lokacin da ya lura da Mama zaune da
as a
asa, kamar ma bata cikin hayyacinda dan ya lura da yanda la
anta ke motsawa.
"Halima lafiya dai ko? ko wani abun ta...."
Bai
arasaba ya ji ni na fashe da matsanancin kuka ina fa
"Abba kana gani na ko, wallahi Abba ni bana ganinka, na zama makauniya, bana ganin komi sai duhu, dan Allah zo ka kama hannuna ka kaini waje inyo alwala banyi sallah ba".
Wa ta iriyar ashar Abba ya kutuntumo ya watsa wa Mubeenah, sannan ya
aura da fa
"Ke abu ta kazar ubanki, ubanki ya hwa
a ya afka ya zunduma cikin makantarnan, ni za ki mayar tsohon banza, na rantse da girman Allah sai kin bu
e idonan, ni za kiyi wa ba
in ciki Mubeenah, ni!! ni!!! Mubeenah."
arashe maganar ya na ta
une fuska kamar zai saka iho, ya riga da ya gama tsala lissafin yanda rayuwa zata canza mai, ya gama sada
arwa a yau zai zama
aya daga cikin masu ku
in a arear unguwar Agege, amma lissafinshi na neman roshewa ganin halin da Mubeenah ke ciki.
Mama ce ta tashi tare da kama ni ta fitar da ni idanuwanta na zubarda hawaye, ni nasan kaf duniyata ba zan samu me sona kamar Mama ba,
auna tattali gami da kulawa a wajen ta ka
ai nike samunsu, ita ce ka
ai bangon da zan jingina inyi kuka kuma ta rarrasheni cike da kulawa ha
i da tausayi.
Ruwa ta zuba a buta ta kama hannuna muka nufi bayan gida, can inda tasan ina tsayawa ta aje ni tare da ajiye butar inda tasan bazan zubar ba, sannan ta fice ta bani waje.
Tsarki na yi kamar yansa na saba, sannan na tafo bango a hankali na fito waje ina sake tabbatarwa kaina na zama makauniya, banyi aune ba na ji wani abu ya ja ni, nai baya-baya na fa
a akan kayan zuba ruwanmu, ji kake "Tinjim." na afka cikin babban bahon ruwa da yake
arami ne bashida tsawo sai fa
Abba ne ya taso daga
akin Mama dan ganin abin da ya faru, sai kuwa yai tozali da ni kwance male-male a cikin bahon ruwa.
"Yau ni Iroro na ga jarfa, ke dan malafar ubanki shine zaki rasa insa za ki fa
a sai cikin baho, wato ne dole sai kin tabbatar min da cewa ki na min ba
in ciki, yo ba
in ciki manah, sarai kin san wahalar da nike sha wajen samo ruwanan, kina can kina barcin asara na je na samo wai dan kiyi wanka idan zamu je gidan da za kiyi aikatau."
'Aikatau', na maimaita kalmar a zuciyata, sai kuma na zabura na tashi zaune ina lalube ina fa
"Abba bara inje inyi sallah sai in shirya idan har zasu
auke ni a haka da makantata ni na amince zanyi aikin."
Nai maganar wani irin karsashi da
warin gwuiwa na zo min.
ALHAMDULILLAH, MUN KUSA GAMA FREE PAGE, SAURA PAGE BIYU.
GA WACCW TA SHIRYA KARANTA LITTAFIN ZAFIN WUTA GA ACCOUNT A
ASA.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY.
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR
ZAFIN WUTA
Follow the
channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,
MATSANANCIYAR DAMUWA,
KUNCIN CUZIYA,
SADAUKARWA,
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.
WRITING BY
MARYAM STAR
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau
"Jajirtattu mu ne
arfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu fa
uwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!"
THE NOBLE WRITER'S TEAM
(
DEDICATION IS OUR STRONG
Typing...
PAID BOOK 500 ONLY
CHAFTER 40-45
Tsit Abba yai jin maganar da nai, sai kuma ya was he baki tare da fa
"Yauwa Mubeenah, ko ke fa, to yanzu kiyi sauri ki shirya zuwa anjima bayan Ummanku ta gama abin kari sai kiyi mu kama hanya dan mu isa da wuri." ya
arashe maganar tare sa taimakamin na fito daga cikin bahon jikina na tsiyayarda ruwa, sake zuba min ruwa yai a buta sannan ya dam
amin a hannuna ya na ta rarrashina gami da lalla
awa, sai naji jikina yai sanyi
alau, duk da ba ganin shi nike ba amma a iya maganar da yai min na fuskanci lallai ya ji da
in maganar da na fa
a, sai na shiga zargin kaina akan
in bin umirninsa da nike a baya, wata
ila hakan ne ya saka ya tsaneni saboda kafiya da ba
in taurin kai irin nawa.
Ban san sanda bakina ya furta. "Abba dan Allah ka yafe min duk abin da nai maka, bazan sake ba, na yi danasanin wanda nai maka a baya, nasan da ace na bi umurninka da na auri abokinka da yanzu nima kana so na kamar yanda kake son su Yaya Habiba, daga yau bazan sake sa
ama umuninka ba in sha Allah."
Kasa
e Abba yai jin maganar da nayi, sai jikinshi yai sanyi, duk wanda ya ta
a zuwa gidanmu koda na wuni
aya ne, to yasan rashin jituwar da ke tsakanina da Abba, tun ma
ota na zuwa bada ha
uri idan yana dukana har takai da suk girman unguwarmu babu me ko kallon inda muke idan wani abu ya ha
o ni.
Bai ce komi ba sai juyawa da yai ya shige
akin Umma wacce dukkan abin da ke faruwa akan idonta, indai wajen iya la
e da jin
wam ne, to Umma ita ce kan gaba, bata yarda gulma ko tsugudidi su wuce ta, a haka ma wai dan a Legos muke ta na tsoron
an iskan unguwarmu, dan abu
alilan sai ka ji ance ansakawa mutum taya an
one shi
urmus, musamman idan wani abu ya ha
a yare da hausawa.
"Wallahi kar ka yarda da abin da ta gaya maka, yaudara ce kawai, so take tai mana ba
in cikin cin arziki shiyasa ta kulle idon, yo ita makantar haukace da zata sameta lokaci
aya, ade bincika zaka samu wani abun ta shafa dan ba
in munafurci irin nata." Umma tai maganar ta na shanye
ananun idanuwanta irinna kwararrun
an gulma da munafurci.
"Ubanta ya zurma ya afka ya zunduma ya fa
a cikin shafawa ido wani dan makancewa, ita yanzu dan kutumar abu ta kazanta har ta yi wayon sanin makirci, to aniyarta ta bita, na fi
arfin ta yaudare ni wallahi, zan gwada ma ta ba abanza nike zaune a legos ba, nima tantirin kaina ne, iskanci sai de mu koyawa wasu badai mu a koya mamu ba." Abba yafi cikin tada jijiyoyin wuya, daga jin abin da Umma ta fa
a shikenan har ya yarda ya hau kai ya zauna daram,dama ba tun yau ya saba irin haka ba, sau da dama hakan kan kasance, lafiya lau za'ayi magana da shi amma da zarar Umma ta ce ba haka ba babu bincike ba lissafi zai hau kai ya zauna akan yanda ta ce hakanne gaskiya.
Mamace ta zo ta kama ni ta kaini
aki tare da yimin shimfi
a da saka min hijabi, al
ibla ta fuskantar da ni tare da bani umarnin yin sallah.
Ina kabbara Sallah wani irin rauni ya baibayeni, sai na ji ina bu
atar tsiyayarda damuwata a gaban Mahallicina me rahama, nasan zai sau
amin ta wani
angaren, aiko na shiga zubda hawaye masu zafi yayinda nike gabatar da Sallah cikin nutsuwa da kamala, kuka me
arfi ya kubcemin lokacinda na du
ar da ga
ina a
asa nakai sujjadah, kuka da addu'a nai sosai har sai da naji nauyin da ya tokaremin
irji ya sauka sannan na
ago naci gaba da Sallar cikin karsashi har na sallame, bayan na kammala azkar na hau karatun al
ur'ani me girma, da yake harda ce da ni, dandanan nisha
i ya baibaye, tabbas karanta littafi me tsarki babbar rahamace, babu abin da yake saka ni nisha
i kamar inji ina karanto littafi me tsarki tiryan-tiryan.
auki lokaci me tsawo ina karatu, har sai da muryata ta disashe sosai sannan nai addu'a tare da shafawa nai zaune abuna ina nazarin rayuwa, wato Allah alhakim, wa ta hikimace ta ubangiji wannan makantar da ya
auramin, godiya nai a gareshi ta hanyar yin tazbihi harma da salatin Annabi, duk safiyar duniya da zan wayi gari da ciwo ko babu sai na yi tarin aiyuka kamarsu, share
akin Mama da na Umma, share tsakar gida, hura wutar
aura abin kari, wanke-wanke, wankin kayanda aka
ata, idan ka cire kayan Mama hatta na Abba nice zan wankesu kullum ranar duniya, a
alla Yaya Sumayya na daka kaya kala uku duk rana, haka zan ha
a in wanke, wani bin Abba ya na zundumamin zagi Umma kuma na mita haka zan zage inyi aiyukana babu me cemin sannu sai ma zagi da nike sha wajen Abba, amma nice yau zaune a
aki ina hutawa kamar yanda kowa ke yi, babban abin da yai min da
i be wuce yanda yau bazanje shago ba, sam bani son zuwa shagonan saboda
an iskan da ke wajen, amma banda damar daina hakan, sai gashi yau babu zuwa shago saboda lalurar makanta.
Ban san na
auki tsawon lokaci ina tunani ba sai da Abba ya kwa
o min kira, firgigit na farka daga duniyar tunani da na lula, da laluben hanya har na kawo
ofar
akin.
"Gani Abba."
"Amshi wannan kunun ki shanye sai kiyi sauri kizo muje."
"To Abba nagode."
Na fa
a tare da lalubawa har na kai inda hannunshi ya ke na amshi kofin kunun, juyawa yai abinshi, ni kuma na zame na zauna a wajen tare da kafa kofin a baki na shiga shan kunun, ina son abu me ruwa sosai hakan ya bani damar shanye kunun duka.
Lalubawa na sake yi ina bin bango har nakai wajen jakar da nike ajiye kaya, da lalube ba bu
e ta na
auki kedar thank you wacce nike ajiye a gefen jakar, laluba
asan jakar nai harna lalubo wa ta
ar siririyar chain, dan
e shi nai a hannuna kamar wani zai
wacemin, sannan na saka hannuna na kakka
e jakar tawa na janyo ta zuwa jikin bango na aje nima na zauna zaman shiru, har yanzu zuciyata ba ta daina dokawa da matsanancin
arfi ba, kuma ina jin wani irin sanyi me kashe ga
i ya na baibaye ni, ga wa ta iriyar kasala me sakar da ga
i da ta saukomin.
Shiru nai ina sauraran bugun zuciyata harna tsawon lokaci, ban san adadin mintunan da na kwashe ba, sai da na jiyo muryar Abba ya na fa
"Mubeenah, ke Mubeenah ki fito idan kin gama ke nake jira mu yi mu tafi lokaci ya na ja."
Zumbur ta tashi kamar dama jiran kiranshi nike.
"Abba dan Allah ka taimaka ka
aukar min jakar tunda bana ganin hanya."
Bai musa ba ya shigo ya
auki jakar tare da kama hannuna muka fito, bai saki hannuna ba sai ji nai ya na fa
"To Mubeena ga mutanen gidana zasuyi sallama da ke."
Murmushi nai sannan na ce.
"Mama nasan kuka kike yi, dan ina iya jiyo zafin zubar hawayenki a cikin zuciyata, dan Allah ki kwantar da hankalinki babu abin da zai sameni sai alkairi, ina ji a jikina wannan tafiyar ita ce zata zamo tsanin da zan taka wajen ganin na cimma muradai da mafarkaina, ha
a Mama ke uwace a gare ni, a duk inda nike zan kasance cikin kwanciyar hankali matsawar za ki ch gaba da yi min addu'a kamar yanda kika saba, zan yi kewar kulawarki a gareni, Allah ya baki ha
urin jure rashina uwa ta gari me maida
iyarta kamar sarauniya saboda soyayya da kulawa
Kuka ne ya kubcewa Mama me tsananin
arfi, yayinda na matso inda muke ta ri
e hannuna gam ta na fa
"Ibrahim ka ji tsoron Allah karka rabani da Mubeenah, wallahi ina jinta kamar
ar da na tsugunna na haifa, ka ji tausayin halin lalurar da ta ke ciki kabarmin ita, wallahi nayi al
awarin zan
auki dukannin
awainiyarta."
"To munafuka
ar ba
in ciki me ba
in hali, ai dama batun yau ba nasan kedin munafuka ce, yo munafuka manah idan ba munafurci da ba
in ciki ba, ina ruwanki da shiga sha'anin uba da
a, wannan ai kinibibine irin na fulanin ruga." Umma tai zaram ta fa
i jin maganar da Mama ke yi na neman yin tasiri a zuciyar Abba, dan ta lura kamar jikinshi ya
an yi danyi.
Cike da macin rai Mama ta saki hannuna ta juyo wajen Umma ta na fa
"Ke Umma ki kiyaye bakin ki
, kisan abin da za ki dinga fa
a, ina ruwanki, wa ya saka da ke, ban san shigar shigula, ki kiyaye ni wallahi kar ki bari in waiwayo ta kanki dan abi ba zai yi maki da
i ba, ina
aga maki
afane kawai dan a zauna lafiya amma badan ina tsoronki ba, daga yau kar in sake ji kin tsomamin wannan ba
in bakin na ki me kama da anzunguro kan kare ta taga, ki shiga hankalinki."
Mama ta yi maganar
acin rai da hasala na bayyana a fuskarta, yayin da Umma tai murus sai walimar idanu ta ke yana shege lahira, shi kanshi Abba mamakin Mama ne ya daskarar sa shi a tsaye, dan bai ta
a tunanin ta na da zafi har haka ba, lallai an
ure ha
urin damo, ya fa
i a zuciyarshi.
Juyowa ta yi wajen shi tare da fa
"Tabbas ban isa in hanaka zartar da hukunci akan Mubeena ba, amma zan tuna maka gaji tsoron Allah, wannan baiwar da kake wula
anta rayuwarka ita ce rufin asirinka, kuma amanace a wajenka, muddin ka zalunceta Allah ba zai barka ba, ka je ka yi duk yanda kaga dama da ita." Mama na gama fa
in hakan ta zo wajena ta dam
amin wani abu a cikin hannuna sannan ta shafa fuskata ta juya fuuuuu ta shige
akinta.
Da sauri Umma ta matso kusa da inda muke ta fara jan hannun Abba wanda ke ri
e da jaka ta ta na turamu waje wai kar Mama ta fito ta hanamu tafiya.
Ina tuntume da komi haka Abba ya ja hannuna har muka fice sannan ta saki hannunshi ta dawo cikin gida ta ka
a su Yaya Habiba zuwa cikin
aki suka shige harda kullo
ofa.
Ina tuntu
e da komi haka Abba ke jaye da hannuwana har muka shiga cikin unguwarmu sosai inda mutane keta hada-hadarsu su na kaiwa da komowa, a Legos babu
an zaman banza kowa fitowa ya ke ya nemi na kanshi dan rufawa kai asiri.
Munyi tafiya sosai kafin mu samu abin hawa, nan Abba ya lalubo wayarshi wacce ta ci duniya duk ta sha
auri da lobali ya lalubo number Yah Hashim ya kirashi dan ya yiwa me abin hawan kwatancin inda za'a ajemu.
Hawa mukai bayan mun tsadance muka tafi, har lokacin ban daina jin sautin bugun zuciyata ba a cikin kunnuwana, sannan sanyin jikina sai da
aruwa ya ke kamar wacce ta shiga cikin na'urar sanyi.
A daidai farkon shiga BANANA ISLAND aka sauke mu, Abba ya sake kiran Ya Hashim, kafin ya zo sai da muka
auki mintuna atsaye, tun ina jin da
in tsayuwar har ta gundure ni, hakan ya saka nace cikin sanyin murya.
"Abba dan Allah ka samo mana inda zamu
an zauna, na gaji da tsayuwa wallahi."
Waige-waige ya shiga yi kamar me neman wani abu, wa ta bishiya me kyau ya hanga a gefenmu, hakan ya saka ya ja hannuna muka je can muka zauna ya na mitar jimawar da Hashim yai be zo ba.
ungurmin daji ne me cike da munanan halittu iri daban-daban, wa ta iriyar guguwace me ha
i da
ura ta taso da iska me tsananin
arfi, saboda tsananin
arfin iskar guguwar sai da halittun da ke wajen suka shiga neman wajen
uya, sauti marar da
in ji me kama da tsawa me firgitarwa ne ya cika dajin gaba
aya, a daidai wajen wa ta tshohuwar bishiyar kuka me rassa da jijiyoyi da yawa wannan guguwar ta tsaya, a hankali yayyafin ruwa ya fara sauka a cikin guguwar da ke
acewa ta na komawa ruwa, farace tas tas farin har ya yi yawa kai da ganin irin hasken nata kasan ba dai mutum ba sai dai jinsin aljannu, fara ce kuma doguwa me yalwar ba
in gashi da tsananin tsawo ta bayyana fuskarta a murtuke, idanuwana sun ka
a sun sauya launi zuwa launin shu
i me haske, cike da
acin rai ta bu
e murya cikin amo marar da
in ji ta kwala kiran.
"Zizzau! Zizzau!! Zizzau!!!."
A yanda ta ke magana sautinta na fita da amo me tsoratarwa, bakinta kuma na feso da feshin ruwa masu zafin gaske, wannan bishiyar kukarce ta shiga girgiza da tsananin
arfi, kafin wani haya
i ya bayyana wani ba
in gajeren aljani mumunan gaske ya bayyana, du
awa yai cike da girmama ya fara kirari gami da fadanci.
Dakatar da shi wannan aljanar ta yi cike da facin rai ta ke fa
"Waye wanda ya aikeka yin aiki akan go
iyata? tabbas za ka fuskanci hukunci me tsanani saboda sa
a umurnina da kuma karya dokar da na gindaya muku akan aiki da wa
acan butulun bil Adaman wa
anda basu san komi ba sai cutar da
an uwansu da ya
a zalunci a doran
asa, yanzu-yanzu da
arfin ikon ubangiji na baka izini kaje ka karya aikin da kai, sannan kuma kadawo ka kai kanka wajen ruwan hukunci."
Bata jira abin da zai ce ba ta
acewa daga wajen, nan take ruwan ya
auke gaba daya kamar be ta
a wanzuwa ba.
Cikin hanzari wannan ba
in aljanin yai girgiza tare da
acewa
at, bai bayyana a ko ina ba sai akan bishiyar da Abba da Mubeena suke zaune su na hutawa.
Shuuuuuuu, wani abu ya gifta ta gefen idon Mubeenah, yayin da ba
in haya
SAURA ONE PAGE MU KAMMALA FREE PAGE INSHA ALLAH, BAN YI AL
AWARIN CI GABA DA SHARE KAMAR KULLUM BA, AMMA WAJIBINE INTURAWA DUK WACCE TA BIYA KU
I SABODA HA
INTA NE.
09136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TA KU HAR KULLUM MARYAM STAR
Follow the
channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,
MATSANANCIYAR DAMUWA,
KUNCIN CUZIYA,
SADAUKARWA,
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.
WRITING BY
MARYAM STAR
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau
"Jajirtattu mu ne
arfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu fa
uwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!"
THE NOBLE WRITER'S TEAM
(
DEDICATION IS OUR STRONG
Typing...
PAID BOOK 500 ONLY
Chapter 7 · 0% Book details