Sashe 4
Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gabaɗaya jikin Hassan ɗin ya fara sawaya, Imran da ya lura da hakan ya ƙame a zaune tamkar soja, gabaɗaya ya tsorata da lamarin yaron dama da ace ba ɗansa bane babu dalilin da zai sa ko hanyar da yaron yake ya bi amma kuma addu'a ta rigayi fata yaron ya fito ta tsatsonsa ne dan haka yanzu babu yadda zai yi amma a ransa ya fara tunanin bin shawarar Inna ta kaiwa Hassan bakin ruwa dan gaskiya ba zai iya da wannan tashin hankalin ba, gashi mahaifiyarsa ta faɗa masa cewa Hassan mutum ne kawai baiwa ce da Allah ya masa.
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Inna da Imran kowa rai fal tsoro kamar farar kura, ganin jikin yaron ya rikiɗa ya zama miciji kansa ne kaɗai na mutum, hakan ya sa Inna sakin wani fitsari ganinta riƙe da miciji da kan mutum. Sakin uban jikin ta yi ta kama kan kaɗai ta riƙe sai uban jikin ya shige cikin ruwan.
"In..In..Innaaa riƙeshi da kyau kar ki je ki sake shi a ruwan nan ya shaƙi ruwan a hanci da bakinsa ya masa illa ko ma ya mutu" Cewar Imran yana wani zare ido kamar ya ce as ya zura da gudu.
"Ni da zai mutu ma da kowa ya huta" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.
"Haba Imirana ai na yi jarumta ma da na iya riƙe kan dan na tabbata da kai ne da tuni ka sakashi a ruwan in limewa ma zai yi a ruwan ya lume"
Gabaɗaya kallon ikon Allah suke sai da Hassan ya koma miciji dukansa, har lokacin Inna tana riƙe da kan,hannunyenta riƙe da wuyan micijin, kallonta kawai Imran ke yi so yake ya tashi ya gudu ya barta amma ƙafafunsa sun ƙi bashi haɗin kai, dan duk jikinsa karkarwa yake dan ko jiya ya ga matuƙar ƙoƙarin Inna da ya rufe ta a ɗaki da micijin, dan da ta rufeshi ji ya yi kamar ya mutu saboda fargaba da tsanani tsoro, ga wani mugun tashin hankali da ya tsinci kansa a ciki yanzu kuma ga ta riƙe da kan miciji.Inna da ke ta hawaye tana jan majina a hanci ta ce.
"Wallahi da ace wannan ba ɗan Halima bane da tuni na daɗe da cikawa rigata iska, na haƙura da ZAMAN WANKAN a ce abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kamar cin tuwon kishiya, kullum jiya i yau, na rantse da Allah da tuni na koma inda na fito gwara gorin Tsalla ya kashe ni dan na san iyakaci ta ce koroni aka yi"
Duk surutun nan da take Imran ba fahimta yake ba so kawai yake ya tsere.
"Imirana, matso ka riƙeshi, sai ka zungureshi irin yadsa Halima ta masa jiya ya dawo mutum" Cewar Inna tana kallonsa.
"Am, uhm, wato Inna ki bari wato ainashin Sadiyar ta fito sai ta zungureshi ai kin san da yake a cikinta ya rayu shi yasa ita in ta taɓashi zai dawo"
"Zancen banza ma kenan, wato haka zan yi ta riƙe da wannan abu... Sai kuma ta yi shiru ta kasa ƙarasawa ganin micijin ya kafeta da ido. Imran ma ya ga hakan sai ya yi saurin aro jarumta ya miƙe tsaye dan kar fa micijin saran Inna zai yi ya san kwa tabbas idan ya gama da Inna kansa zai dawo shi kuma bai shirya mutuwa ba. Inna ganin ya miƙe sai ta gama gane abin da yake shirin yi hakan ya sanya ta tuno da abin da ya mata jiya da dare da kuma alƙawarin cewa sai ta rama da ta yi, hakan ya sanya ta gama shirya abin da za ta masa, musamman da ta tuna cewa Hajiya Amina ta ce wani malami maƙocinta ya ce duk yadda yaron zai zama miciji babu abin da zai yiwa kowa ba zai yi sara ba, sai dai shi miciji ganinsa ma abin tsoro ne gashi da kwarjini musamman wannan Hassan ɗin da girma yake yi sosai idan ya sawaya.
Wata dariyar ƙeta ta yi a ranta, tunawa da irin muguntar za ta masa hakan ya sa ta saki kan micijin da ta riƙe da hannu biyu ta riƙe da hannu ɗaya ɗayan kuma ta miƙa ta damƙo harshen rigar Imran, idanu ya zaro ganin abin da Inna ta yi wani faɗuwa gabansa ya yi da mugun ƙarfi dan ya san matsawar suka haɗa hannu da Inna to tabbas ba za a kwashe da daɗi ba, dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka hannu ya sanya zai fincike rigar amma sai ya ji ya kasa domin Inna ta mata riƙon kazar kuku kamar ma ba tsohuwa bace ta riƙe sai ka ce wani ƙaƙƙarfan ƙaton ne ya riƙe masa.
"Ka zaci za ka iya ƙwacewa ko, to ko uwaka Amina na riƙe sai dai ta saduda saboda ƙarfina da naku ba ɗaya bane kuna nan binni kuna cin kayan daɗi wanda basa riƙe ciki ni kuwa ina can ƙauye ina cin tuwo da danbu wanda suke gina jiki"
"Haba Inna bayi fa zan je in shiga ya kika riƙe ni"
"Tusugunno za ka yi ba fitsari ba, ban da rainin wayo ni zaka buÉ—ewa ido to wallahi sai dai ka saki fitsarinka a tsaye kamar saniya, dan ba zan sake ka ba, ni ma nan jigilif nake da fitsarin kayana jargaf kamar na yi iyo a ruwan maliya"
Imran ganin Inna na janyo shi ya sa ya kakkafe tana jansa yana togewa, haka ta janyoshi ta dawo dashi kusa da ita ta ce.
"Sa hannu ka taɓa yaron nan ya dawo mutum"
Idanu ya zaro ya shiga girgiza kai yana roƙonta ta sake shi.
"Ka taɓa shi na ce, ya dawo mutum yo ban sa ma lalacewa ni da nake ɗorin ɗosano ma na taɓashi bare kai"
"Inna ki min rai dan Allah"
"Ranka yana hannun Allah" Cewar Inna tana ƙara damƙe rigar Imran sai da ya gama tsurewa sosai ta ga idanunsa sun fito sai zare su yake kamar wanda ya yiwa sarki ƙarya, aikuwa ta sanya ƙafa ta danne harshen rigar Imran, ta sanya hannayenta biyu ta ɗago Hassan a siffar miciji ta ɗorawa Imran a kan cikinsa da yake data janyoshi kwantawa ya yi reran, haka ta .
ɗora masa micijin kan micijin a wajen sai tin haɓar Imran idanun Imran cikin na micijin.
Imran hatta numfashinsa kasa shaƙa ya yi duk tunaninsa ma yadda aka yi Inna ta shammacesa har ta masa riƙon da ya kasa ƙwacewa.
"Ka sanya hannu ka shafa kansa ya dawo mutum in wankesa kafin uwarsa ta fito"
Ta faÉ—a tana kallon idanun Imran da ke kafe cikin na micijin dan ya kasa motsa ko da yatsansa ne bare ya iya É—auke kansa.
"Imran a mace ko a raye? Kai kamar ba namiji ba"
"Wallahi ko maza maza ne ni dole in É—auke wuta Inna wannan in ban mutu ba ma ai kwanana ne a gaba" Cewar Imran a zuciyarsa hawaye na bin fuskarsa.
Hannu Inna ta miƙa ta ɗan taɓa micijin aikuwa ya ɗan motsa ya kaɗa jela, Imran kuka yake kawai marar sauti.
"Ba ni ka sanyawa abu a fura ba na rinƙa sawu bayi kamar mahaukaciya sabon kamu, daga na dawo wani kashin ya dawo na koma bayin har sai da na dawo na kasa zama da ɗuwaiwukana, ƙarshe sai durƙuson haihuwa na yi, bayan rabona da in yi durƙuson haihuwa tun na naƙudar uban Sadiya amma sai gashi ka sanya tarihi ya maimaita kansa"
Ganin dai ba ya motsi sai Inna ta sake zungurin micijin aikuwa micijin ya fasa kansa kamar zai sari Imran diff kake ji jikin Imran ya saki, ashe suma ya yi, hakan ya yi dai dai da shigowar Sadiya.
Wani salati Sadiya ta saki tana yin kan Imran da sauri, hannu ta sanya ta zunguri micijin aikuwa sai ya dawo mutum tare da sakin kuka É—aukansa ta yi, ta É—ora a kafaÉ—a ta sanya hannu ta shiga jijjiga Imran amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.
"Inna garin ya haka ta faru" Sadiya ta faÉ—a tana sakin kuka cikin tashin hankali. Wata harara Inna ta jefa mata, ta kalleta ta ce to uwar Æ´an son miji ba mutuwa ya yi ba suma ya yi, kuma ba komai ya sumar da shi ba illa soyayyar irin ta uba da É—a "
Banza ta yiwa Inna ta ajiye Hassan a kan gadonsa da har lokacin bai yi shiru ba ta fita da sauri ta ɗakko ruwa a kofi tana zuwa ta sheƙawa Imran, amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, sai da ta ƙara masa ruwan sai ya sauke wata ajiyar zuciya ya buɗe idanun yana wani ƙiƙƙiftawa saboda bai gama dawo wa hayyacinsa ba, dariya Inna ta ƙyalƙyale da ita kallonta Sadiya ta yi cikin jin haushi ta ce
"Haba Inna ya haka mutum ya suma kuma kike dariya.
Dariyar dai Inna ta cigaba da yi sai da ta yi ta ishe ta sannan ta ce.
" Barni in dara Sa'adiyya wai baki ga yadda idon Imirana ya yi ƙulu-ƙulu ba, kamar an sanya goruba a cikin kwanon sha, ji fa yadda yake kwance magashinyan ko zaune ya kasa tashi"
"Wai ma garin yaya haka ta faru Inna dan Allah ki bar dariyar nan"
"Baki lura da kyau bane Halima kalli yadda na jiƙe da fitarin tsoro da wahala, to kalli wandom mijinki ma ya saki fitsarin shi ma, amma saboda ragwanta, Imirana har suma ya yi amma ni ina tsohuwa babu abin da na yi, wai fa ɗaukan Hassan ya yi ya ɗora a kafaɗa shi ne kawai Hassan ya koma miciji a kafaɗar tasa wannan ne dalilin da ya sa ya suma kin ga kwa dole na yi dariya ni da bakina Allah ba ya tsaga min ba a hana ni walawa sai ka ce wani kututturen icce"
Cewar Inna dan bata so Sadiya ta fahimci abin da ke faruwa.
Wani takaici ne ya tokarewa Imran jin abin da Inna ta faÉ—a, hakan ya sanya ya fara yunkurin tashi zaune dan shi bai ma san ya yi fitsarin ba sai da ya ji ta faÉ—a.