← Book details Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 15

Sashe 2

Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Imirana lafiyarka kuwa kake ta sheƙa amai da talatainin daren nan ko laulayin ciki kake?"

Jin muryar Inna ya sanya Imran jin wani tashin zuciyar hakan ya sanya ya cigaba da ƙwaƙulo wani aman"

"Kai dai ka san jarabar da ka ci kake amai" Ta faɗa tana surar buta ta shige bayi ta ɗan kara ƙofar jin gudawa na neman zubo mata, ga tsoron aljanin jiya a ranta ga kuma gudawa da bata da haƙuri ko jinkirin fitowa.

Ƙaran yadda Inna ke sakin kashi ya sanya Imran jin gabaɗaya duniyar ta masa zafi, haka ya kunna famfo ya wanke fuskarsa da bakinsa ya kora aman ya kashe fanfon ya lallaɓo a hankali ya dawo ɗaki dan gabaɗaya ji ya yi ya galabaita da aman da ya yi, haka ya dawo falo ya kwanta, amma daga ya rufe idonsa bakinsa yake gani cike da goron bakin Inna haushi da takaici ya ishe sa. Bare da ya ki ta shige bayi ta daddage tana sakin gudawa ko ƙaƙƙautawa babu ƙaran kashin sai amsa kuwwa yake masa a kunnuwansa. Inna kuwa jin bata jin ƙaran aman Imran hakan ya bata tabbacin ya bar wurin, cikin sauri ta yi tsarki, ta ɗauki ruwa a cikin kwantainer da ake ajiyewa a bayi ta yi floshing ta fito tana jan ƙafa dakyar. Falo ta shigo ta zauna daɓas a kan kujera, Imran yana jin shigowarta, ya runtse idanunsa da ƙarfi dan ba ma ya son ganinta bare ya tuna mafarkinsa da ita.

"Imirana, Imirana, Imirana? Ta kira sunansa sau uku amma bai amsa ba kuma bai buÉ—e idon ba.

"Kai dai wannan yaro da mugun hali kake wallahi, kana ji ina kiranka amma ka ƙyale ni, dama maganin gudawa zan ce ka bani idan kuna da akwai a gidan" Banza ya mata.

"To ta Allah ba taka wallahi Imirana, ace ina maka magana amma ka ƙyale ni dama kana sheƙa amai ma dana maka magana ka ƙyale ni ... Kafin Inna ta gama magana ta ƙara jin cikinta ya bada wani ƙululuuu da hanzari ta tashi ta fita ta sanya takalmi a baibai ƙafar dama a ta hagu ta hagu a ta dama ta nufi bayi duk da tana jin tsoron aljani amma kashin da ua matso ta ba zai ruƙu ba kuma dai ganin Imran idonsa biyu ya rage mata tsoron.

Sai da ta kwashe mintina sannan ta dawo tana zuwa za ta cire takalmi ta ga yadda ta sa a juye.

"Kai Allah raba bawa da wahala gauro a teburin mai shayi, ni Azumi matar Malam yau na ga takaina wallahi, tsabar ruÉ—ewar da na ji cikina ya yi ashe takalmin ma baibai na sa"Ta faÉ—a tana zaunawa a kan kujerar falon.

"Kai dai wannan yaro baka da imani kana ganin yadda nake sawu wani kan wani zuwa bayi amma ba za ka iya ce min sannu Inna ba" Ta faɗa tana kallon Imran da ke zaune ya dafe kai. Kafin ya bata amsa ta ji cikin ya murɗa alamar gudawar ta taho aikuwa ta matse ƙafafuta ta zauna ta ce

"Kai ina dalili hallaw wani kashin ne ke shirin fitowa to babu inda zani kuma ciki ka gaji da ƙuginka ka barni, yo daga dawowata ace wani kashin ya taho bayan yanzu kafin in dawo sai da na tsaya na tsage shi tas, na tabbatar na gama babu wani saura" Ta faɗa tana ƙara matse ƙafafunta tare da zaunawa daram tana danna saitin mazaunanta a kujerar dan kashin ya koma sai wani gaba take tana baya kamar wacce take kan lilo wai duk dan kashin ya koma.

Amma da yake gudawa ne ko alamar komawa bai yi ba, haƙori ta sanya ta danne harshenta da ƙarfi sosai idanunta suka firfito , ai babu shiri Imran sai ganin Inna ya yi ta yi bakin ƙofa a sukwane, takalmin ma a hannu ta ɗauka dan kashin dab yake da zubowa.

Imran dariya ya fara har da ƙyaƙatawa yadda ya ga Inna ta fita da gudu-gudu tamkar an biyo ta.

"Wa ya faɗa miki barno gabas take, ai faɗa da mahaukaci ba daɗi, wallahi ba dai ni kika rufe a ɗaki da miciji ba na miki magiyar duniyar nan kika ƙi buɗewa har sai da na gama galabaita da shiga tashin hankali sannan kika buɗe ni kak rinƙa min dariyar na yi fitsari a zaune wai na rakuɓe a jikin bango kamar ƙadangare, son matata ta raina ni, ai dama na sha alwashin sai na rama dan bashi kika ci gashi nan yanzu kina karɓar sakamako" Imran ya faɗa yana dariya tare da tuna muguntar da ya yiwa Inna da dare wacce ta sanya ta gudawa.

Yadda Imran ya yi ya sanya Inna ta samu ruÉ—ewar ciki. Kafin su kwanta da daddare bayan kowa ya watse lokacin da Imran ya dawo sai ya tarar da Inna zaune a falo da kwanon furarsa a gabanta za ta sha, wani haushi da takaici ne ya sanya ya kasa cewa komai dama ga haushinta da ya wuni yana ji ta rufeshi da miciji a É—aki yana ta tunanin hanyar da zai bi ya rama sai ji ya yi ta ce.

"Imirana har an dawo kai wai baka da aiki sai zaman gida kamar mace, baka je ɗan yawo ba cikin abokai ku ɗan zanta, kai kullum a gida, haba ina dalili kai ɗan zaman majalissar nan ma na maza baka yi, daga an yi sallar isha'i sai a ganka ka shigo gida zunƙwai-zunƙwai ka kama ƙofa ka garƙame, ina ga masu barka ma da suke zuwa da dare gidan suke samu a rufe" Ta faɗa tana tashi ta fita.

Shi dai bai ce komai ba, kallonta kawai yake yana ji kamar ya rufeta da duka har sai ta daina motsi. Tana fita wata dabara ta faÉ—o masa da sauri ya buÉ—e hannun frige inda ake ajiye magunguna, ya É—akko wani magani da aka rubuta masa kwanaki da ya kasa tsugunno (Ya kasa kashi) Shi ne likita ya rubuta masa da ya sha sai cikin ya saka ya samu ya yi kashin, murmushi kawai yake ganin ya samo hanyar da zai rama abin da Inna ta masa da sauri ya É—auki maganin guda huÉ—u ya zuba mata a cikin furar ya gauraya ya mayar da maganin da sauri ya koma kan kujera ya zauna yana latsa waya kamar bai tashi daga wurin ba duk wannan abin da ake Sadiya tana bayi bata ma san Inna ta buÉ—e frige ta É—auki furar Imran ba.

Ana jimawa sai ga Inna ta dawo riƙe da kofi ta kalli Imran da ke danna waya ta taɓe baki ta zauna ta ƙara ruwa a furar t gauraya ta shiga shan abinta ba tare da ta san ami Imran ya zuba a ciki ba. Sai da ta sha sama da luday bakwai ta ɗago kai ta kalli Imran da ke latsa waya bata san ba yana ganinta ta gefen ido ba yana dariyar ƙeta a ransa.

"Imirana dan Allah zan baka shawara amma kar fa aka ce santin fura ne ya sa na faɗa, ka daure ka gine wancan filin na tsakar gida kai ma ka yi turaka irin ta maza amma ina dalili kana ɗaki ɗaya da matarka kuma ko yanzu ka zauna ina shan fura kana zaune hakan bai kamata ba" Ta faɗa tana ƙara cika ludan ta sha.

Wani kallo Imran ya jefa mata, ya cigaba da abin da yake.

"Ka huta tun da ba zaka gina ba, to wallahi idan Halima ta sake haihuwa na zo ZAMAN WANKA baka yi turakar ka ba kana shigowa gidan nan zan fara maka waƙa in ke cewa ɗan cikin mata baki ya koshiye ya ci tuwon mata gumba yake jira ɗan karannana wa zai baka" Ta faɗa tana rausaya kai kamar ƙadangaruwa.

"Za ki san duk wannan abin idan cikin ki ya ruɗe kika ringa zuwa bayi " Ya faɗa a ransa. Tana cikin shan furar ne Sadiya ta fito daga bayin wata kunya ta rufeta ganin Inna na shan furar Imran amma haka ta dake ta ƙyaleta gudun magana dan ta san yanzu idan ta yi magana sai cibi ya zama ƙari. Da wannan cakwakiyar suka kwanta to shi ne Imran ya yi mafarkin ya shiga bargon Inna shi ne da ya tashi yake kwara amai ita kuma hakan ya yi daidai da lokacin da maganin da ta sha a cikin fura ya fara aiki shi ne ta fara gudawa.

Yana dariya jin ƙaran tafiyarta ya yi shiru ya dake, haka ta shigo falon tana tafoya dakyar kamar ƙwai ya fashe mata a ciki.

"Wash kai mai za a yi da cutar kashi, haba ka rinƙa tsugunno babu ƙaƙƙautawa" Ta faɗa tana durƙuwasa a tsakiyar falon dan ji ta yi ƙarfinta ya ƙare, durƙusawa ta yi irin durƙuson masu naƙuda gwiwoyinta a ƙasa ta shiga ƙwalawa Sadiya kira dan duk abin nan da ake Sadiya tana ta shigar bacci.

Sadiya da ta fara jin kiran Inna sama-sama haka ta daure ta buɗe idonta ganin ƙwan ɗakin a kunne Inna bata kan gadon sai ta tashi zaune.

"Wayyo Sadiya ba kya zo ba in baki wasiyya dan ni na san lokaci ya yi, mu kuma haka Allah ya yi da cutar kashi za mu mutu, mu tashi a lahira muna ta tsula kashi, yo na ji an ce kowa da abin da ya mutu yana yi zai tashi a lahira yana yi, mu kuma haka za mu yi ta keta mutane a filin ƙiyama muna ɗoyi "Inna ta faɗa tana sakin kuka jin cikinta ya sake kiran ƙululuuu. Haka Sadiya ta taso ta fito a ranta tana jin haushi wannan ZAMAN WANKA ko jaraba ace bala'in safe da ban na rana da ban da daren ma ba a barka ka huta ba.

Amma kuma ganin Inna a durƙushe cikin wani yanayi sai ta nufe ta da sauri.

"Inna lafiya dai?"

"Ke ma dai Sadiya da shegantaka kike wallahi, yo ke da kika ganni na yi durƙuson naƙuda ma har kya tambaya lafiya, rabona da in yi durƙuson naƙuda tun lokacin hainuwar ubanki, amma yau cutar kashi ta sanya na kasa zama da ɗuwaiwukana sai durƙuso" Ta faɗa tana dafe ƙasa da hannuwanta.

"Subhanallahi! Inna me kika ci haka ya ɓata miki ciki?"
Chapter 2 · 0% Book details