Sashe 3
Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Haba Sa'adiyya har kya tambaya ma menene zai ɓata min ciki ni da bani da ɓataccen ciki gareni ba, ni ai cikina sunansa komai da ruwanka dan komai na bashi karɓa yake, amma yau dai kin ga an saɓa lamba dan kuwa kashi nake ratatata, amma Imirana kin ganshi nan magana ma ta gagara"
"Sannu Inna "Cewar Imran .
"Riƙe abinka in dai duniya ce yau naka gobe ma ɗan uwanka kaima wani abun zai sameka ai"
"Babu abin da zai same ni"
"Imirana... Ƙaran da cikin Inna ya sake saki ne ya hanata ƙarasa maganar tata,
"Halima riƙeni kar in ɓata miki ɗaki dan ba zan iya tafiya ba ma, haka Sadiya ta kamata ta kaita bayin ta jirata da ta fito a ƙofar bayin ma ta watsar da takalman nata haka Sadiya ta kamata ta mayar da ita, frige ta buɗe ta ɗakko maganin gudawa ta bata cikin ikon Allah sai kashin ya tsaya haka suka koma suka kwanta baccin wahala ya ɗauke Inna. Kafin baccin ua ɗauketa take ta tunanin abin da ta ci ya ɓata mata ciki haka, a nan tunanin furar da ta sha ya faɗo mata nan kuwa ta tuna ta tafi ɗakko ruwa ta bar furar a wurin hakan ya sanya ta yi shakku a kan gudawar tata haka kawai ta ji bata yadda da Imran ba "Tabbas Imran ne ya min wannan abun" Ta faɗa lokacin da ta ke kwance kafin baccin ya ɗauketa,
"Wallahi Imirana sai na rama wannan abin da ka min dan wallahi sai ka san Azumi ka yiwa hakan...
Duk wacce ta san san ta fitar min littafi ta siya ta mn mgn in bata kuÉ—inta,
Masu son a tallata musu hajarsu
mmn afrah 09030283375
[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: ```Wannan littafin kuÉ—i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
DAN ALLAH KAR WACCE TA SAYI LITTAFINA DAN TA FITAR MINI,IDAN DAN KI FITAR ZA KI SIYA KI RIƘE KUƊINKI HAJIYA BANA BUƘATA.```
1ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
WASHE GARI
Bayan Inna ta yi sallah ta fita duk da jikinta babu ƙwari, ta hura wuta ta ɗora ruwa, dan Sadiya cewa ta yi ta barta ta ɗora amma Inna ta ƙi dan a cewarta Sadiya ɗanyen jiki gareta na jego, shi kuma jikin jego bai son garaje haka dai ta rinƙa komawa tana iza wutar har ruwan ya tafasa. Bayan ta yiwa Sadiya wanka ta barta a bayin ta fito, haka ta haɗa ruwan wankan yaran amma da ta zo maimakon ta shiga can cikin bedroom sai ta ajiye a falo, haka ta kwaso komai da za ta buƙata ta dawo ta ajiye a falon. Husaini ta fara janyo gadonsa ta ajiye ta koma ta janyo na Hasan tana jan sunayen Allah a ranta. Imran da ke zaune yana kallonta ganin tana shirin tuɓe Husaini ya ce.
"Inna wai kina nufin a falo za ki wanki yaran nan? Bakya jin yadda ake sanyi ai cikin É—akin ya fi É—umi"
Banza ta masa ta cigaba da cirewa Husaini famfas, sai da ta gama tana shirin tsundum yaron a ruwa Imran ya sake mata magana a karo na biyu.
"Haba Inna ai da tausayi fa ace kin wankesu a falo baki ji har iska shigowa take ba"
Dakatawa Inna ta yi daga ƙoƙarin saka Husaini a ruwan ta kalli Imran a shelaƙe tana yatsina fuska ta ce.
"Wai ni kai ka ji na shiga harkar ka ne a yau? Ko baka san idan mutum ba ya ta taka ba ka rabu da shi ba" Ta faɗa tana harararsa dan tun da ta zargeshi da zuba mata abin da ya ɓata mata ciki sai take jin mugun haushinsa saboda irin yadda ta yi ta sawu bayi.
"Yau kuma Inna ke ce bakya son magana?"
"Kai ka kiyaye ni, na faɗa ba na son maganar, kuma da kake zancen wankan yara a falo to ina sane wai karuwa ta taka matar aure, a nan na yi niyyar zan musu wanka" Ta faɗa tana sanya Husaini a ruwan ta shiga yi masa wankan. Shi dai Imran bai sake magana ba ganin ta wani haƙiƙice tana magana. Sai da ta gamawa Husaini ta shirya shi tsaf ta kwantar da shi dan tun tana shafa masa mai bacci ya ɗauke shi.
"Bismillahir rahmanir rahim, li'ila fi ƙuraishin, aniyar kowa ta bishi, iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in" Cewar Inna lokacin da ta miƙa hannu za ta ɗauki Hassan.
"Ana tsoronka É—an mayya, ya ce daga ni har uwata" Imran ya faÉ—i karin maganar yana kallon Inna.
"Tsoro wajibi ne ai,har gwara wata wainar da ta wake, wani da ya laɓe jikin bango dan tsoro har da sakin fitsarin wahala" Cewar Inna tana cirewa Hassan kaya amma kuma gabanta n dukan uku-uku. Jin maganar da Inna ta faɗa Imran ya ɓata rai dan sai ta tuno masa da jiyan a ransa ya ce
"Fitsari ai ba ni kaɗai ba ke da kika yi arba da aljani kike saki fitsari a tsaye tafiya ma gagararki ta yi sai da rarrafe kika shige ɗaki, har da kwanan ƙasan gado" A fili kuma ya ce.
"Ki yi ki wankeshi dai kafin ya sawaya, dan yana fara sawaya zan fice in garƙameki a falon irin na jiya"
Muƙut Inna ta haɗiye wani yawu da bata san lokacin da ya taru a bakinta ba, jin abin da Imran ya ce na sawayar Hassan, kallon yaronkawai take tana ƙiyasta yadda za ta yi wurgi da shi idan ya zama miciji a hannunta.
"Dan Allah Imirana ka sassauta muryarka kar fa yaron nan ya ji ka tuna masa ya sawaya, ni fa dama saboda gudun sawayar tasa na ƙi zama a cikin ɗaki na fito falo dan idan na ga ya ɗakko sawaya in bar maka shi in gudu" Cewar Inna cikin sanyin murya.
Dariya ya ƙyalƙyale da ita ya kalli Inna ya ce.
"Wai dama dibara ce kika yi Inna, taɓɗi lallai kuwa kin kama riɓaɓɓiyar igiya dan babu abin da zai hana ni gudu, miciji fa"
Inna Kallon Hassan take da yake wani miƙa hannunsa yana wani markwaɗewa ta ce.
"Haba Hasanunu daure-daure ka maida baiwarka ka ji ɗan albarka, idan na wanke ka, na gama shiryaka sannan uwaka Halima ta fito daga wanka sai ka sawaya in ma mesa za ka koma wato babban miciji sai ka koma, amma wallahi jiya ma ban ji daɗin karon ba tun da ka sawaya na rinƙa tsuma ga ubanka Imirana ya kulle ni a ɗakin ai ka sani dan kana ciki kaima har saman drower kaya na ɗane sai gani a ka ɗare-ɗare ba ka ganni ba lokacin ai mun haɗa ido da kai da ina saman ko?" Inna ta kai ƙarshen maganar tana rausaya kai kamar ƙadangaruwa, ta faɗa da alamar tambaya kamar dai yaron ya ma san me take cewa.
" To ka yi haƙuri ka ji, Inna Azumi ce matar Malam wallahi ZAMAN WANKA na zo wa uwarku Halima ka ga ai baƙon ka annabinka, ni da za ka bi ta tawa ma da ka tsaya a mutum ɗinka har na gama ZAMAN WANKANA na tafi in yaso idan na bar muku gidanku idan ka sawaya ka koma miciji kar ka dawo mutum sai ka yi sati guda ko ma wata guda iyayenka su yi ta famar tsere da kwanan zaune dan nasan dai ba wanda zai haɗa ɗaki da miciji ya yarda ya runtsa dan tsoro ba zai barshi ya yi ko da gyangyaɗi ba bare a kai ga bacci"
"Haba Inna wannan wace irin kuɗuba ce kike yiwa yaron nan?" Imran da bai san yadda aka yi ba ya miƙe tsaye sai ganinsa ya yi tsaye cankarkar a tsaye.
"Yo ba dole ba in masa kuɗuba ya bari sai na tafi saboda babu daɗi ni tsohuwa ina ganin tashin hankali muraran amma ku da yake da ƙwarinku kuma da sauranku, sannan ma ku kuka haifesa sai ku yi rayuwarku da shi a micijin"
"Dan Allah Inna ki bar wannan maganar ki wankeshi kawai"
"To" Ta ce rana tsunduma Hassan cikin ruwa tare da karanto fatiha da salatul fati"
Ganin ta sanya Hassan ɗin a ruwa sai hankalin Imran ya ɗan kwanta ya koma mazauninsa ya zauna yana haɗiye wani yawu muƙut.
Ta gama wanke wa Hassan kansa zuwa fuska ta ɗauraye tana cikin saɓa masa jikin, Imran sai kallonsu yake gabansa na faɗuwa dan shi ko kaɗan bai cire rai daga cewar Hassan ɗin ba zai koma miciji ba, ji yake kamar ya tashi ya fice amma kuma ba ya so Inna ta zargi wani abu haka dai ya daure ya zauna ba dan ya so ba.
A ɓangaren Inna ma haka abin yake wankan take masa amma kamar wanda ta riƙe wuta, tana wanke yaron ne dan dai ba yadda za ta yi, a haka ta juya bayan yaron inda yake fatar miciji ta shiga wankewa cikin tsoro dan gani take tamakar miciji take yiwa wanka, tana ta saƙawa a ranta cewar in ba lalura ba babu yadda za a yi ta haɗa hanya da yaron nan ba bare kuma har ta wankesa. Juyo cikin yaron da Inna ta yi sai gani ta yi ya koma kamar fatar bayan, idanu ta zaro har tana ɗauke numfashinta dan ta lura Hassan ya fara sawaya. Dakatawa ta yi da wankan ta ajiye sosan.
Imran da ya lura da yanayin Inna ya sauya amma dai bai san dalili ba dan bai ga abin da ta gani ba ya ce.
"Inna cigaba da masa wankan mana na ga kin ajiye soson kuma baki É—auraye masa jikin ba kin bar masa duk kumfa" Ya faÉ—a kamar wanda ke jira a ce masa kulle ya ce cass dan gabaÉ—aya a tsorace yake.
Shiru dai Inna bata tanka masa ba, tana ganin ikon Allah kawai tana jin kamar ta saki kuka ta yi ta ƙugawa jama'a su kawo mata ɗauki in ba ƙaddara ba ace tana riƙe da miciji, halittar da cikin mintu kaɗan za ta sareka ta yi ajalinka lokaci guda.