← Book details Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 15

Sashe 11

Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"I mana" Inna ta faÉ—a tana kwashe duk yadda aka yi da Abdallah da ya zo barka da matarsa.

"Inna haka aka yi ashe haÉ—e su kika yi, kai abokina ba dama" Ya faÉ—a yana dariya

"Kai dai bari yo shi ma Imiranan ranar nan fa suma ya yi saboda Hassan ya sawaya ya zama miciji a jikinsa" Ta faɗa tana dariya. Haka suka sha ta dariyarsu har cikin Abid yana ƙullewa dan ya ma manta Imran na jiransa a waje. Sai can ua tuna ya musu sallama ya sanya hannu a aljihu ya ɗakko dubu ɗaya ya miƙawa Inna. Hannu ta sanya ta karɓa tana washe baki.

"Haba Abid ai da ka barshi hidimar ai ta yi yawa " Cewar Sadiya cikin jin nauyin Abid.

"Lah ba kamai ai...

"Rabu da ita kawai in banda baƙinciki meye wata dubu ɗaya dan ya bani kyauta zaki wani haƙiƙice kina cewa ya yi hidima ai dama kowa ya san ya yi hidima musamman da ya fi mijinki da bai san ya siye zuciyar mutane da kyauta ba sai baƙin hali da na zuciya fal ransa" Ta faɗa tana sanya dubun a cikin ƴar pos ɗinta.

Dariya Abid ya yi jin abin da Inna ta ce haka kawai shi ds a ce za a barshi da Inna da ya huta d shiga damuwa ko ɓacin rai, saboda ita bakinta ba ya shiru kuma bata gajiya da abin dariya duk da ita tana yin komai dan raha ne.

"To Inna sai kwana biyu"

"Kwana biyu fa Abida sai ka ce an maka baki, yanzu sai ka iya kwana biyu baka zo mun gaisa ba, ai baka ji daÉ—in da na ji ba da ka bani bugun Abujar nan"

" To Inna idan na samu dama da lokaci zan ke leƙowa "

"To nagaode sosai" Ta faɗa lokacin da ta fito har ƙofar falon Abid ya sanya takalminsa ya fita.

"Oh ɗan nan da kirki yake Sa'adiyya ya fi min mijinki Imirana sau miliyan ma" Cewar Inna lokacin da ta zauna a kan kujera tana ƙara ganin atamfarta.

"Inna dan Allah kike iya bakin ki idan abokan Imran sun zo kin ga ko a fuska ya nuna ba ya so kina shiga shirginsu" Cewar Sadiya cikin lallaɓawa dan ta san Inna hukuma ce sai da lallashi.

"Ikon Allah, lallai Halima wuyanki ya fara isa yanka sauran kuma a gwada wuƙa a tabbatar, yanzu sabibi da Allah ni kike faɗawa wannan maganar to ni da banda ma gaisawa da muke a ɗan taɓa hira ina ni ina su, ni fa kawai dan na ɗaukesu ɗaya da ku ne tamakar jikokina in ba haka ba me ma zai haɗa ni da su, in kuma baƙincikin ɗan abin da zan ke samu kike yi to duk da babu wanda ya taɓa bani wani abin arziƙi in ba Abida ba"

"Abid Inna" Cewar Ashrof.

"Ke ki kiyaye ni, in ma Abu zan kirashi ina ruwanki"

"Ki yi haƙuri Inna" Cewar Sadiya.

"Da haƙurin ta mutu sadakar nawa kika bani?"

"Allah baki haƙuri"

"Haƙuri kaya ne naɗa gammo ki ɗauka"

Bayan fitar Abid Inna ta ce ta gaji da zaman cikin gidan fita za ta yi ta zagaya ƙafadunta dan ciwo suke mata, gidan Hajiya Amina za ta je. Haka ta musu sallama ta fita ta sha wata atamfarta mae kyau, ta saka ɗan madinanta ta kama hanya ta fita, har Sadiya ta bata kuɗi ta hau ɗan sahu amma ta ƙi karɓa wai ita ta fi son tafiya a ƙasa saboda kalle -kalle.

Hanyar gidan Hajiya Amina ta kama, har sai da ta je gidan bayan ta gama kalle -kalle da ratse -ratse. Haka ta je gidan Hajiya Amina suka gaisa ta ɗan jima sai kuma ta kamo hanya ta taho gida dan Hajiyar ma sai da ta yi ta yi da ita a kan ta zauna idan aka yi sallar magariba ta yi sallar sai ta tafi, amma Inna fafur taƙi zama dan ta fi so ta taho ido na ganin ido. Saboda ta fi so ta taho ido na ganin ido dan ta ga gari gari ma ya gan ta.

dan haka ta kamo hanyarta ta taho riƙe da ledar da Hajiya Amina ta zuba mata bakilawa. Tana tafe tana kalle-kallenta tana ƴar waƙarta a hankali, tana cewa.

"Carman dudu carman duduwa , carmagade, akwai wani baƙo a gidan mai gari, carmagade, ba duka ba ya lakuci, carmagade, in duka wa zai bashi ne, carmagade, aradu ta Allah ba zan bashi ba" Tana cikin yin waƙar ne ta hango wani ƙerarran gida mai shegen kyau tun daga nesa gidan ya birgeta. Dan dama ba ta hanyar ta bi ba a tafiya yanzu kuma sai ta canja hanya dan ta sake ganin wasu sabbbin abubuwa ba irin wanda ta gani a tafiya ba.

"Ikon Allah masu gidan nan kuwa sun san ana wahalar kuɗi kuwa a duniya, an ya kuww sun san sunan wani abu wai babu, ace wannan gida kamar ba a duniya ba" Ta faɗa tana tsaye tana ƙarewa gidan kallo.

"Oh ni Azumi ina can a ƙauye ina fama da ɗaki ɗaya a gidan Malam kullum ana bala'i da Tasalla to ina kuma ga na ganni a gidan nan ina ga kuma sai an mana tsakani da Tasalla dan kar take faɗawa mutane ita kaɗai ce matar gidan" Ta faɗa tana ƙarasawa ƙofar tangamemen get ɗin da ke buɗe, sai da ta tabbatar babu kowa mai gadin ma ba ya nan...

Masu son a tallata musu hajarsu MMN AFRAH 09030283375
[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin kuÉ—i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

"Aikuwa dai sai na shashshafa gidan nan da hannu na, a saka a baka ai ya fi a rataya, ko da a ce baka da rabon zama a cikin waɗan nan gidajen a duniya to kafin mu je aljanna mu samu rabonmu gwara dai na taɓa in ji, ai da hanau gwara mannau" Cewar Inna tana dosar wajen, hannunta ta kai jikin ginin ta shafa shi da hannu biyu kamar wacca ta samu ka'aba har da jingina fuskarta a jiki ta goga fuskarma a jiki hagu da dama.

"Na taɓa ka da alkairi gidan ƴan gayu" Tana ƙara shafawa. Haka ta rinƙa bin wurin tana ganin ginin tana gyaɗa kai alamar mamaki.

"Oh ni ƴasu mutane masu kuɗin nan ko a ina suke samun kuɗaɗe haka su yi ta baje hajarsu a duniya son ransu, ko kuwa rijiyar haƙo kuɗin garesu irin wannan gida, to mu da bamu dashi haƙuri ya ganmu, dan ma dai da daɗi saboda Malam ya faɗa mana cewa ko a lahira sai talaka ya riga me dukiya shiga aljanna, yo kai da baka da kuɗi ina ka ga tarin tambayoyin da za ka amsa dangane da ina ka samo kuɗi kaza, ta wace hanya ka kashe su" Ta faɗa tana kama haɓa har lokacin kaɗa kai take kamar ƙadangaruwa. Leƙa cikin get ɗin ta ɗan yi daga inda take tsaye ta yi dogon wuya tana so ta ga ko za ta hango me gadi, amma babu abin da take hangowa sai tarin fulawoyi masu matsanancin kyau.

"Ni Azumi da a ce zan samu shiga cikin nan ɗin ma ba tare da na zauna na yi rayuwa a ciki ba, da wallahi tallahi iya hakan ma na godewa Allah kuma na ji daɗi, yo in ban shiga na gani ba na kashe ƙwarƙwatar ido na ba me aka yi da maza, kawai shiga zan yi komai ta fanjama fanjam" Ta ce tana takawa a hankali cikin sanɗa ta durfafi get ɗin, tana shiga sai ta ga ashe ma babu abin da ta gani a waje motoci ne gasu nan wasu a lulluɓe wasu a buɗe.

"Ikon Allah na kwance ya faɗi wato dai a duniya ma akwai aljannar duniya, lallai masu gidan nan kun huta amma duk da haka ba za mu shiga sahun ƴan Allah baku mu samu ba" Ta faɗa tana leƙa cikin wata mota tare da shafawa.

"Tabbas idan na koma garinmu duk mai son in bashi labarin gidan nan sai ya biya ko da kuwa Malam ne, Tasalla kwa ko a da kuɗinta bata da rabo dan ba zan bata labarin nan ba" Ta faɗa tana ɗaga kai sama tana ƙarewa benen kallo ga wasu hazbiya a saman suna ta waricinsu. Haka ta rinƙa kutsa kai cikin farfajiyar gidan tana ta kallo abinta.

"Ni ai yau ta waru wallahi yawon buɗar ido dai da wasu ke biyan kuɗi suna hawa jirgi su tafi ƙasashen waje, to ni ga nawa yawon buɗar idon a nan babu ko sisina bare taro, yo da na san akwai gidaje masu kyau kamar wannan a kusa da gidan Halima ai nan da gidan Halima babu nisa da nan zan ke tahowa in na gaji da zaman gidan, da dai in ke zama da wannan Imiranan me baƙar zuciyar tsiya ga mugunta ai gwara in zo nan in wanke dauɗar idona" Ta faɗa tana bin bayan gidan daga can ciki.

"Anya kuwa Azumi kya ke fitowa kina barin Imirana daga shi sai Halima a cikin gidan, bakya ganin wani abu zai faru" Wani ɓangare na zuciyarta ya tambayeta.

"Kuma fa da hakan ne wallahi, kar in je in fito yawon buÉ—ar ido shi kuma ya je ya buÉ—e Æ´ar mutane a gida ya je ya rugurgujeta son ransa ya farke mata É—inki a shiga uku" Ta faÉ—a a fili tana saurin juyowa dan ji ta yi ma kallon ya fita daga kan ta duk da akwai Ashrof a gidan kuma Æ´an barka na zuwa amma sai take ganin Imran zai iya aikin Ashrof wani wuri dan ya cimma burinsa.

"Dole in yi maza ma in koma gidan dan yanzu komai ma zai iya faruwa amma in ina kusa dolensa ya ɗauki dangana ko ba ya so" Ta faɗa lokacin ta dawo hanyar fita, tana shirin ficewa ta hango wani wuri na shaƙatawa an jera faraen kujeru ga falawoyi kewaye da wurin.

sakin baki ta yi ya layar me tafiya tana dosar wurin a ranta tana cewa.
Chapter 11 · 0% Book details