← Book details Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 15

Sashe 14

Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ku shiga mota mu tafi, ɗaya ya shiga gaba ni da ɗaya mu shiga baya ɗaya kuma ya tuƙa" Ta faɗa tana saurin shiga motar ta zauna dan tunowa ta yi da aljanin da ta gani a bayi , hakan ya sanya ta ji wani mugun tsoro dan bata manta karonsu ba. Haka suka shiga suna zazzare ido saboda tsoro Inna kuwa da ta shiga baya ta zauna a setin kujerar direban ta ɗaga ƙafafunta ta ɗora a kan wuyan direba, a haka yake tuƙin rai duk ba daɗi wuyansa ɗauke da ƙafar aljana.

Haka ake tuƙin sun yi dif kamar ruwa ya ci su suna shigowa cikin gari ana fara kiran sallar magriba, dan haka wani wurin mai saida kayan marmari Inna ta nuna musu.

"Maza ku tsaya ku cikawa sarkin aljannu leda da kayan marmari san wannan ledar da kuma sa ta faÉ—i lokacin da kuka kinkimeni kamar kun samu tukunya alkakinsa ne da bakilawa, to yanzu ku ramawa kura aniyarta in ba haka ba kuna komawa gidajenku za ku ga an mayar da ku dajin da muka baro yanzu, in sau dubu za ku komo nan sai an maida ku"

"Za mu siya ma" Suka faɗa suna ɗakko kuɗi kowa ya bayar aka cikawa Inna ledar viva da kayan marmari masu yawan gaske, dan cewa ma ta yi gorubar bature ta fi yawa (Apple) Haka aka ɗakko kayan nan aka sanya a mota, har ƙofar gidan da suka ɗauki Inna suka dosa za su kaita amma sai ta ce, dama ai ita aljana ce kuma ba a nan take ba, nan ta ce bangon duniya za ta je amma sai sun kaita kan bola ta nan za ta bi ta tafi, haka ta rinƙa nuna masa hanya, a haka dai suka kama hanyar gidan Sadiya sun kusa ƙarasawa sai ta ce su ajiyera a wajen wata bola saboda a nan za ta bi ta koma hanyar aljannunsu, ita kuma ta yi haka ne dan kar a a je wucewa ta ƙofar gidan Sadiya Imran ya ya ganta a motar ya tona mata asiri dan kaɗan da aikinsa.

A dai dai bolar suka tsaya, wanda ke zaune a mai zaman banza ya fito da sauri ya buɗewa Inna ƙofa ta fito aka miƙo mata ledarta shaƙe da kayan marmari.

"Gashi iya" Ya faɗa yana durƙusa gwiwoyinsa a ƙasa.

"Ku ajiye a nan sarkin aljannu zai sa dogaransa aljannu su zo su É—auka" Cewar Inna a fili a zuciyarta kuwa cewa ta yi.

"Yo Ina dalili zan hau bola da abun da zan ci"

Ajiyewar ya yi, gabaɗaya suna jin tsoro Inna kuwa dosar bolar ta yi tana addu'a a zuciyarta dan kar ta je ta yi gamo da magribar nan. Suna ƙoƙarin jan motar suka ga Inna ta fara wata girgiza da sauri ya ja motar suka bar layin a sukwane.

Sai da suka yi tafiya me nisa suka tsaya kowa ya kama gabansa dan sun ce sun bar garkuwa da mutane daga yau, sbd angamo da aljanar da suka yi yau, shi ma Ogan bayanin da suka masa a waya bayan barinsu wajen Inna ya sanya an maida me gadin kuma sun fasa É—akko tsohuwar da suka yi niyya dan suna ganin kamar idan za su É—akko ta aljana za ta iya rikiÉ—a su É—auki aljanar a maimakon matar dan haka shi ma barin garkuwa da mutanen ya yi ya koma ya kama sana'a.

Inna kuwa tana ganin gilmawar motarsu ta gefen ido, sai ta É—an dakata, sai da ta tabbatar sun tafi sanna ta baro kan bolar da sauri ta suri ledar kayan marmarinta, tana ta waiwaye tana cewa

"Ja'irai ƴan iskan ƙarya yo me na manta gashi na samu kayan marmarina ko banza ai na ƙwaci kaina, da yanzu ina can wataƙila ma wani daga cikinsu ya far mini tsakar dare tsofai-tsofai da ni, ya je ma ya goga mini cuta mai karya garkuwar jiki" Ta faɗa tana shigewa gidan Sadiya, sai da ta sanya ƙafarta a cikin gidan tsoron aljanin gidan da ya tsorata ta rannan ya faɗo mata, tana fatan kar dai yana jin yadda ta yaudari samarin nan, ya zo da dare ya tambayeta dalili.

"Assalamu alaikum, gafaranku dai masu gida" Cewar Inna lokacin da ta shigo gidan amma gidan shiru kamar ma babu kowa.

"Ikon Allah kun ji ina Halimar take ta barni ina ta faman rafka sallama" Ta faÉ—a tana shigowa tsakiyar falon amma babu kowa sai su Hassan da ke kwance kan gadajensu suna bacci.

"To ko dai bayi ta shiga, kenan Asharofa har ta tafi gida, to ai shikenan" Ta faɗa har lokacin ledar kayan marmarinta na riƙe a hannunta.

Imran da tun sallamar Inna ta farko ya jiyo ta amma Sadiya bata ji muryar Inna ba, hakan ya sanya ya riƙe hannun Sadiya da ke shirin fita ya hanata ta fita kuma ya yi hakan ne saboda ya yiwa Inna abin da za ta kunyata. Sadiya kuma da yake ta ga yana ta ƙuncin rai sai ta kasa tafiya ta dakata, tsaye suke a tsakiyar bedroom ɗin, ya riƙe hannunta babu wani abu da ya ce kuma bai mata komai ba duk da tana ɗan tsoron yanayin nasa dan ta san shi bai iya riƙe kansa ita kuma jego take babu damar yin hakan.

"Sa'adiyya ba dai baccin magriba kike yi ba" Cewar Inna tana dosowa bedroom ɗin da ƙarfin gwiwarta, Imran da ya ji takun tahowarta ɗakin ya yi saurin janyo Sadiya jikinsa ya rungumeta, hakan ya yi dai dai da bankaɗa labulen da Inna ta yi.
Ledar kayan marmarin ta saki ta faɗi ƙasa, ta fara rafka salati, tana tafa hannuwa kamar wanda ta ga mazinata turmi da taɓarya. Sadiya da ta ji maganar Inna ta shiga ƙoƙarin raba jikinta da na Imran, aikuwa Imran ya riƙe ta ƙam ya ƙi sakinta dan yanzu yake so ya ga yadda tsohuwar nan mai tsuru-tsurutun tsiya za ta yi, dan shegen shishshiginta da zalama ne ya sanya ta zo masa wani ZAMAN WANKA dole ya nuna mata bashi da kunya ko ta tattara komatsanta ta bar masa gida ta haƙura da ZAMAN WANKAN.

"Imirana, kai Imirana, wai Imirana ba magana nake maka ba" Cewar Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.

"Wannan an yi taƙadarin yaro wataƙila ma ba ya cikin hayyacinsa, sai na yi da gaske zai ƙyale ƴar mutane yo ban da jaraba ma yarinya tana jego amma ba zai ƙyaleta ba"

Sadiya duk kunya ta kama ta sai kiciniyar ƙwace kanta take, amma Imran ya ƙi bata haɗin kai nema ma yake ya haɗe bakinsu amma sai kauda kai take"

"Na shigesu ni Azumi me idanuna ke gani, Imirana riƙe da Sa'adiyya ko shamaki babu a tsakaninsu, yanzu ba za ka saka ta ba Imirana ko dan kunya ta ma ai ka saketa, amma ka runƙunƙume yarinyar da jego take ɗanye sharaf, ai abin da kunya yin tsirara a gaban uban miji" Inna ta faɗa kamar ta saki ihu dan jin nauyin yadda ta gan su, gashi kunya duk ta kamata amma tsegumi da kuma son ganin ƙwaƙwaf dan kar a yi katoɓara ya hanata tafiya daga ɗakin.

Imran kuwa jin yadda Inna duk ta rikice sai ya sanya hannunsa ɗaya ya riƙe ƙugunta ɗayan kuma ya kai wajen ƙirjinta a ransa yana cewa

"Ai tun da gane -gane gareki wallahi sai kin ga abin da ya fi ƙarfin ganinki, wa ya ce miki ana shiga tsakanin ma'aurata?" Ya faɗa a ransa.

" Na shigesu ni ɗiyar me daddawa jiƙar me barkono yau ina ganin abu , yo Imirana banda fallasa auren bashi ya za a yi ka rungumi me jego, tabbas shi yasa ba a baiwa kura ajiyar nama nima da gangan ne na fita na barku a gidan in ban da tsautsayi zagin mahaifi ai dama ba a bar mutum kamar Imirana ba da mace a cikin gida, yo me nema a duhu ne ya samu a sarari" Ta faɗa tana ɗan tako ƙafarta ta matso cikin ɗakin, dan so take ta san yadda za ta yi ta ƙwaci Sadiya kar a yi abin kunya.

Har lokacin nan da Inna ke ta karaÉ—i Imran ko niyyar sakin Sadiya be yi ba so yake ya ga iya gudun ruwan Inna za ta fice ta basu wuri ko kuma za ta cigaba da tsayuwa kamar an dasa ta har sai ta ga abin da zai turewa buzu naÉ—i.

"Yau na tabbatar da waye kai Imirana, dan tabbas gani ya kori ji, ni kaɗai na san abin da ya faru da ni a fitar nan tawa daga gidan nan, kuma ni na san abin da hannu na ya damƙa (Al'aura) ya Allah kai ka san karatun kurma Allah ka tsare min idanuna da gani na daga abin da zai ɗaga min hankali, yo banda ƙaddara ma ni da ba na ƙaunar ganin mazaƙuta in ba ta Malam ba, me ya kaini na taɓa mazaƙutar maza har uku da hannuna, ji nake kamar na sa wuƙa na gundule hannun nan nawa da ya taɓa al'aurar da ba halalinsa ba" Cewar Inna tana sakin kuka, dan gabaɗaya sai ta ji birnin ta fita a ranta yau ta haɗu da maza da abin da ta musu kaɗai ne ya ƙwace ta gashi kuma yanzu ta dawo gida ta tarar da wata katoɓarar.

Imran kuwa furucin Inna ya sanya dariya ta kusa ƙwace masa, amma haka ya daure ya cigaba da ƙoƙarin kai hannunsa wajen ƙirjin Sadiya ita kuma tana ƙoƙarin bige hannunsa.

"Amma wannan yaro an yi me wankekken ido, bayan ƙwaƙumarta da ka yi babu shamaki tsakaninku, hallaw na shanunta kake so ka damƙo, to wallahi dai ka bi duniya a sannu a gaban idona baka jin kunya kake waɗan nan abubuwa kamar wanda uwarsa ta ce jeka ka ganiz shi yasa ashe ko zamana baka ƙauna a gidan na kafi so a barka ka ci karenka ba babbaka, ai dama idan ka ji makaho yana cewa a yi wasan jifa to tabbas ya taka dutse"

Imran juya Sadiya ya yi yake neman kwantar da ita a kan gado.
Chapter 14 · 0% Book details