← Book details Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 15

Sashe 15

Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Halima wai duk a gaban idona fa ake sarrafa ki kamar wata injin kaɗin taliya, amma kin kasa kataɓus ki ƙwaci kan ki so kike sai sheɗan ya masa linzami ya haike miki da ɗanyen jegon, wallahi ki kiyayi biyewa ɗa namiji Sa'adiyya ina rabaki da kiwon kyalle kina kyalle ta haihu, , ni nan yanzu na ƙwaci kaina daga hannun maza ƙartai uku, bayan haka harda yaudarar kayan marmari amma ke a hannun namiji ɗaya kin kaya ƙwato kan ki kin barsa sai waricinsa yake a kan ki, sai ka ce wata matar shige, ai matar shige bata daraja amma ke kuwa da ba matar shige ba kya biye masa"

Ganin Imran ya kwantar da Sadiya a kan gado Inna ta saki ihu me haÉ—e da kuka.

"Dan Allah Imirana na roƙeka dan darajar iyayenka ka rabu da yarinyar nan, kar amana ta ci ni, duk wacce taje ZAMAN WANKA tamkar an damƙa mata amanar me jego ne a hannunta, so kake ka je ka sa ƴar mutane ta yi ciki da goyo, ka farke mata ɗinki a shiga uku, bayan ɗinki bakwai Amina uwarka ta faɗa min an mata a mafitar ɗa (HQ) Sai ka ce wata ƙwarya amma kake neman maida hannun agogo baya, dama duk abin da aka yi da jaki sai ya ci kara, kuma ai dama abin kirki bai gaji kare ba, in ya yi ma dukansa ake"

"I luv u baby) Cewar Imran cikin wata murya da ya yi da gangan.

"Ƙarya yake miki wallahi yaudara ce kawai irin ta maza, duk da ban san fassarar abin da ya faɗa ba, amma na san magana ce me daɗi dan na ga a kan gado ya yi maganar kin san kuwa maza kalamansu basa tashi sai suna neman biyan buƙata to a nan za ki ji kalaman soyayya har da na siyarwa"

"Ina sonki masoyiya" Cewar Imran shi ma yana ƙoƙarin hayewa gadon, sai da ya hau gadon ya kife a kan Sadiya ɗare-ɗare, kicinyar tashi Sadiya ta shiga yi amma ya hanata.

"Lahaula wala ƙuwata illah billahi aliyal azim, Imirana kan ruwan cikinta za ta hau a gabana" Inna ta faɗa tana sauri ta yi taku ɗaya biyu sai gata a gaban gadon a sukwane, aikuwa ta shiga kiran Imran da ƙarfi tana cewa.

"Imirana kai, kai Imirana tasata (ÆŠaga ta) tasa Æ´ar mutane, wallahi ban bari ka yi wannan aikin da na sani, azo ayi abun kan ji alawo, sai daga baya ake wallahi tallahi" Ta faÉ—a tana jan rigarsa, amma Imran ko gizau be yi ba, cikin sauri ta juya ta bar É—akin har tana haÉ—awa da gudu -gudu ta yi tsakar gida gabaÉ—aya a gigice take.

Imran kuwa ya ɗauka kunya ce ta sanya Inna ficewa daga ɗakin dan haka sai ya fara ƙoƙarin tashi, ai sai ya fara jiyo ƙaran gudun Inna kidif-kidif kamar an biyo ta, da sauri ya koma yadda yake ya yiwa Sadiya rumfa.

"Bari dai na yi maganinka na yi maganin sheɗan ɗin da ya rufe maka ido kake neman aikata aikin da na sani" Cewar Inna da ta dawo ɗauke da taɓaryar da ta ɗakko a kicin, ɗaya hannun kuma muciya, Sadiya da yake ita ce a kwance Imran kuma ya baiwa Inna baya bai ga abin da ta ɗakko ba, sai Sadiya ta ce cikin ƙaraji.

"Abban twins tashi taɓarya" Ta faɗa tana turashi da ƙarfi da hannunta dan ta san kaɗan daga aikin Imna ta ɗaga taɓarya da muciyar nan sa rafkawa Imran dan tsaf za ta sauke masa su a gadon baya ta je ta lahantashi a shiga uku a zo ana a'i ina indo. Imran turawar da Sadiya ta masa sai gashi a gafe rigingine a kan gadon, hango Inna ɗauke da madokai ta iyu kukan kura za ta hau kansu ya sanya ya yi wata adungure ya dira daga gadon sai gashi ba shiri tsaye a kan ƙafafunsa. Sadiya kuma da sauri ta tashi zaune ta miƙe tsaye dan dama ita dan ya mata nauyin kuka ne kuma ya hana ta ƙwatar kan ta amma dama da ba za ta yarda ta yi wannan abin kunyar ba a gaban Inna ta barwa kanta abin gori da abin faɗa marar iyaka a wajen Inna Azumi.

Ita ma Sadiya dirowa ta yi daga kan gadon ganin duk da Imran ya ɗaga ta amma Inna kamar bata fasa abin da ta yi niyyar yi ba, ganin da gaske tana shirin farmusu da taɓarya da muciyar ya sanya Imran yin wani uban tsalle ya bi ta bayan Inna ya fita daga ɗakin a sukwane, Sadiya ma da gudunta na bara ta fice suka bar Inna a ɗakin tana sababi tare da rufa musu baya cikin gudu -gudu sauri -sauri.
Chapter 15 · 0% Book details