← Book details Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 15

Sashe 12

Yar Zaman Wanka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai kuwa yau sai na ɗosana ɗuwaiwukana a kan kujerun nan" Haka ta ƙarasa wajen ta zauna a kan kujerar har da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jin una ma nan gidan Malam ne da kuwa kakarsu ta daɗe da yanke saƙa.

Daga can wajen gidan wata mota ce ta faka a ɗan nesa da gidan, wasu maza matasa majiya ƙarfi suka fito su biyu, suka bar wanda ke tuƙawa a ciki.

"Kar fa ku yarda wani ya gan ku, ku bi a sannu, kun ga dai yanzu da sauran haske a gari magriba bata kai ga yi ba, dan dai ma unguwar masu hannu da shuni ce kowa yana cikin gidansa tun da shi me gidan ba ya ƙasar shi da matarsa, kuma Oga ya sanya an zo an ɗauke me gadin to ku tabbatar kun ɗakko tsohuwar nan kar ku bari a samu matsala, daga it sai ƴan aiki a cikin gidan, wallahi kar ku bari a samu matsala dan Oga ya ce ba ƙaramin kuɗi za a karɓa ba idan muka kawo masa tsohuwar nan domin Alhajin zai iya bayar da ko ma nawa ne idan ya ji an kama mahaifiyarsa dole ya bada kuɗin fansa idan ya ji za a aikata barzahu in bai bada kuɗi mai tsoka ba" Cewar wanda ke mazaunin direba cikin muryar dabanci

"An gama za mu yi duk yadda za mu yi mu kawo ta" Suka faɗa tare da juyawa suka nufi gidan, ta baya suka zagaya suka fara leƙen gidan daga wasu ƴan ƙofofi da aka yiwa gidan kwalliya da shi suna so su samo yadda za su shiga, duk da ba me gadi dan Ogansu ya sa an kama shi dan ma kar su zo ɗaukan tsohuwar su tafi ya kira me gidan ya faɗa masa, a kira ƴan sanda a sanar da su amma in suka ɗauketa kafin a gano hakan sun sanar masa sun kuma gargaɗeshi a kan kar ya sanarwa ƴan sandan. Hango Inna suka yi zaune kan kujera a wajen shaƙatawa ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

"Baaba ai ka ga tsohuwar ma a araha tana zaune ba sai mun sha wahala ba wajen shiga can cikin gidan"

"Wallahi kuwa ai kawai mu gewaya mu shiga gidan" ÆŠaya ya faÉ—a, haka suka gewayo dan zuwa su shiga ta get É—in gidan.

Inna da ke zaune ta É—akko alkakinta ta gutsura ta mayar a ranta ta ce.

"Kin ga Azumi tashi ki tafi, kar masu gidan su fito ki shiga uku dan ba makawa sai yadda hali ya yi" Ta faÉ—a tana tasowa dan ta tafi.

"Kai dakata mu laɓe gata nan ma za ta fito daga gidan, tsuntsu daga sama gashashshe" Cewar ɗaya yana janyo rigar ɗaya suka dawo suka laɓe.

Inna da ke tafiya hankali kwance tana ƴar waƙarta
"Duniya ba wurin zama ba, da ka cuta ƙwara a cuceka, yau taka gobe ta ɗan...

Raf ɗin da aka yi da Inna da bata ma lura da samarin ba shi ya dakatar da ita daga ƴar waƙarta, bakinta suka danƙe da hannunsu suna waige-waige irin n marararsa gaskiya, cikin azama suka rinƙa ƙoƙarin kai Inna inda motarsu take, amma Inna sai turjewa take tana neman gagararsu. Idanun nan nata kwa ya fito ƙulu-ƙulu sai son tofa albarkacin bakinta take amma riƙon da bakinta ya sha ba na wasa bane.

"Kai Baaba wannan tsohuwa da shegen ƙarfi take, ka ga yadda take neman gagararmu" Cewar ɗayan yana huci kamar wanda yake kokawa da doki.

Sun kusan zuwa inda motar take ai Inna da ta ga sun doshi mota sai hankalinta ya tashi dan duk tunaninta Æ´an yankan kai ne za su tafi da ita su yanke kan nata.

"Wayyo Allah na, wayyo Malam wayyo Tasalla ku kawo min ɗauki gani a hannun ƴan yankan kai, Malam da Tasalla duk da na san kun min nisa amma dole in kira sunanku dan na san idan na kira Sunan Imirana sai dai su gundule min har ƙafafu dan wallahi baƙin halinsa ba zai sa ya taimaka min b mutumin da ya tsane ni, bari in ƙwaci kaina dan ba zan yarda a cire min kai ba in mutu in barwa Tasalla Malam ta zauna ita ɗaya" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ja wani uban birki, aikuwa aka shiga turumurtu ita da su, har sai da na cikin motar ya ga Inna na neman ta gagaresu ya taso cikin hanzari rai a ɓace yana zuwa cikin ɓacin rai ya ce.

"Wai dalla malamai meye hakan sai kun sa asirinmu ya tonu yanzu ban da abin kunya har wannan tsohuwar ce kuka kasa kawo ta mota tana ta mayar da ku baya " Ya faɗa yana hucin ɓacin rai a zuciye ya kama Inna wai shi nan mai ƙarfi aikuwa ta daddage ta cije a wuri ɗaya ta ƙi gaba ta ƙi baya ganin wankin hula na son kai su dare su uku amma sun kasa jan tsohuwa sai laya ya ce su mata cali-cali aikuwa cikin lokaci guda mutum biyu suka kamo ƙafar Inna sai gata an mata cali-cali biyu riƙe da ƙafar ɗayan kuma da saman kan har lokacin hannunsa a riƙe da bakin Inna, a haka suka saka ta a motar biyun suka saka ta a tsakiya, ɗayan ya shiga ya ja motar da uban gudu a sukwane suka bar layin. Tuƙi yake amma Inna sai uban bige -bige take a bayan motar ta hana samarin nan biyu sakat duk ta tara musu gajiya kamar wanda suka yi dambe. Sai da suka daddafeta da iya ƙarfinsu sai haki suke sannan ne suka ɗan samu salama amma kuma sun ƙulle mata idanu, da wani ƙyalle bakin kuma ɗayan ya rufe mata da hannunsa.

Hanyar bayan gari suka nufa duk ta tara musu gajiya, ba dan uban kuÉ—aÉ—e da Ogansu ya ce za a samu idan sun kamo tsuhuwar nan da na jaki za su lakaÉ—a mata su jefar da ita.

Tafiya suke amma Inna hankalinta a matuƙar yashe yake dan tana gani lokacin barinta duniya ya yi domin kuwa ta haɗu da waɗanda za su fille mata kai.

"Allah na tuba, ka yafe mini kura kuraina, ka sa ni a aljanna, ka haɗa fuskokinmu a gidan aljanna da malam, amma banda Tasalla ita ma a kaita aljannarta da ban amma ba wacce za mu zauna da ni da Malam ba " Cewar Inna a zuciyarta hawaye zubo mata gashi babu damar ƙugawa dan an yiwa bakinta rub.

A haka dai ta shiga shirya abin da za ta musu duk da tana ganin mawuyaci ne ta kuɓuta amma za ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin ta musu wani abin ko da zai ita kasancewa bata rama ba. Dama dai ta san zai yi wahala a ce ka rama abin da wanda ke shirin rabaka da duniya zai maka. Ganin ta tuno abin da za ta musu sai ta fara tunanin aiwatarwa. Hannun damarta da ke gefen wanda ke damarta, kuma a wajen cinyarsa hannun nata yake duk da ya riƙe ra amma kuma wajen kafaɗarta ne ya kama ya maƙalƙale, dan haka tsintsiyar hannunta ba a riƙe take ba, dibara ta yi ta miƙa hannun wajen inda al'aurarsa take.

"Yau zan yiwa mazaƙutarka (Al'aura) Damƙar da tun da ka zo duniya ba a mata ba, kai ko wanda ya maka shayi lokacin kana yaro ai ba damƙarta ya yi amma yau za ka gwammace kiɗa da karatu" Cewar Inna tana lallaɓawa da hannun har sai da ta ji ta je saitin inda za ta samu abin da take so, amma ba wai tana ɗora hannun a wurin bane, tunda hannun baya kai ga ɗorawa a wurin ba dan haka babu wanda ma ya san ƴar tsohuwa akwai abin da ta shirya, kawai tun da sun ga sun samu lagonta na maƙureta a tsakaninsu sai basu kawo komai ba.

Laɓɓanta na baki ta shiga buɗawa a hankali yadda wanda ya riƙe bakin ba zai ankara ba dan ganin da suka yi ta saki jiki ta daina haure -haure da ƙoƙarin ƙwatar kanta sai ya sassauta riƙon bakin dama dan kar ta yi ihu ta tona musu asiri ya rufe bakin bare kuma yanzu da suka bar cikin gari suka doshi jeji inda ko ta yi ihun babu mai ji bare a ceceta ko a kawo mata ɗauki, sai da ta gama aunasu su duka biyun ta daddage ƙarfinta na bara ta damƙe gaban ɗayan(Mafitsararsa) Ɗayan kuma ta gantsara masa cizo, a tare suka saki wani uban ƙara mai firgitarwa, wanda hakan ya sanya direban ya taka wani uban birki dan ganin me ke faruwa suka saki ihu mai ƙarfi haka a tare bayan sun san suna cikin yanayin da suke buƙatar sirri duk da a jeji suke amma ya dace su kiyaye abin da zai zama tonuwar asirinsu, yana jan birkin ya waiwayo, har lokacin Inna tana riƙe da mazaƙutar ɗayan ɗayan kuma tafin hannunsa yana tsakanin haƙoranta ta musu mugun damƙa. Kowanne sai jijjiga yake kakar ya hau doki yana sukuwa saboda tsabar azaba dan wanda Inna ta damƙi mafitsararsa har balls ɗin ta haɗe ta damƙe. Ihu suke da iya ƙarfinsu suna neman ɗauki, gashi kuma saboda tsabar azaba sun kasa tunanin ɗaukan mataki ko yunƙurin ƙwatar kansu, dan burinsu kawai ta sakr su. Direban kashe motar ya yi ya juyo yana ɗura musu zagi, ashar yake surfa musu saboda bai san me ke faruwa ba, kuma bai lura ba dan wanda ya riƙewa Inna baki har lokacin hannun na a yadsa yake kamar ya riƙe mata bakin, direban kuma bai san an samu juyin mulki ba yanzu Inna ce riƙe da hannun me riƙon bakin a gefe ɗaya kuma ta damƙe mazaƙuta abinta.
Chapter 12 · 0% Book details