← Book details Yar Hutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 19

Sashe 12

Yar Hutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ya ja motar ya tafi gida, yana parking ana kiran sallan Maghreb,,, ya shiga part din shi da sauri, ya fada toilet ya sakar wa kan shi shower, yayi wanka hade da alwala. Ya zira farar jallabiya saboda ba ya saka kowace kamar jallabiya face Fara.

Ya fesa turaren Sa Mai sanyin dadi,, ya nufi masallaci. A hanya ya hadu da Abba sai suka jera tare zuwa masallaci.

Ba su dawo ba sai bayan sallar isha'i. Suka samu mummy zaune a kan sallaya Ta idar da sallah Tana karanta 40 rabbana.

Suka zauna suka jira Ta iddar,,, sai ta ce masu "let's head to the dining table, suka mike zuwa dining ta Yi serving din su. Suna ci suna hira, har Abba ya Lura haidar ba ya cin abincin sosai,,,, sai ya ce "son,,, what's wrong with you? You are not eating.

Sai yace "it's nothing Abba, don't mind me.

Ya debi abincin ya Fara ci amma Bai Yi nisa ba ya tashi yana fadin ai ya ci abinci a gidan khalil.

Sai mummy ta ce, yanxu har Ka iya cin abincin a gidan khalil Ka dawo ba tare da Ka ci nawa ba?

Sai ya ce sorry mummy, he insisted so I had to. Kin San abincin ki ya fi min Na kowa dadi.

Sai ta ce toh shikenan na daga maka kafa haidar...

Sai haidar ya ce toh Bari in tafi part dina, I have unfinished work kuma gobe Monday...

Toh haidar Allah Ya tashe mu lafiya,, don't forget your ablution and adhkar before you sleep.

In shaa Allah mummy.

Yana shiga ya kulle ko ina ya cire jallabiya ya saka pj's din sa ya hau gado.

Ya ji zuciyar shi babu abin da yake bukata kamar ya ji zahra a tare da shi.......

Muje zuwa

Taku har kullum, yar mutan Kagara 😎
*YAR* *HUTU*

*BY* *YAR* *MUTAN* *KAGARA*

*PAGE* *45* */* *46*

Zara da gudu takarasa shiga gidan su tana fama rusan Kuka daddy mummy da khadija dasuke cin abinci da gudu suka fito har suna ture juna "mummy tarungume yarta tana kuka,

Daddy yamatso yakama hannun zahra yakaita parlon yazaunar da ita suma suka zauna yace mamana meyafuru? Meyamiki? Ina yakaimin ke'

Tafada jikin daddynta takara fashewa dawani kukan mai cin rai, haka sukazuba mata ido tayi mai isarta tayi shuru don kanta.........

Khadija tabude fridge tadauko goran pure life mai sanyi tabude tamika mata sha sis takarba tasha sosai ta ajiye........

Daddy yace maman ina sauraranki.

Tagoge hawayen daya gangaro mata tace daddy general aliyu mutumin kirkine me kyautata ma jama'a mai tausayi nakasa dashi yana girmama kowa, bayashiga harkan wani bayatake hakkin wani,

Shimutun ne maison kyautata ma nakasa dashi yake daddy mummy kunga yadda kukaga haydar fari haka zuciyar shi take fara kal........

Duk abunda haydar ya aikata akaina wlh ninaja saboda ba halinshi bane kuma taimakon rayuwana yayi sbd shi mai adalci ne.......

Tashiga basu labari tun farkon haduwan su a round about kala rashin mutuncin da tamishi dakuma lokacin bikin fadila da abu buwan dasuka faru lokaci harda marin da tamishi a bainar jama'a.......

Ai daddy rasa bakin magana yayi shi besan haka zahra ta aikata ma babban mutun haka ba acikin bainar jama'a, mummy tace ai duka abinda yamiki kekika saya kulmu ina fadamiki zahra kibar fitsara bashida fa ida....

Kar wata rana kiyi ladama....

To saiga zancena yafito kewai mahaifin ki yanada kudi zakitaka duk Wanda kikaso to ba ama Allah isgilanci wannan yazama izina a gareki.......

Daddy yace hakane hajiya gaskiya kikefadi duk nine na sangarta zahra banason baci rainta banaso inga tanemi abu bata samuba, kuyi hakuri insha Allah hakan baze sake faruwa ba kekuma zahra inason kinatsu kikyara halayenki da mu amalanki da jama'a,

Insha Allah daddy aini haydar ya kyarani

Nangari fa ya ajiyeni gidan wata iya mai dambu, ya aureni ne sbd yadau fasan abun danayi mishi kuma wlh seyarikeni da amana.....

Betaba chutardani ba.

Takoma jikin mummy tafashe da Kuka dan Allah kubashi hakuri yazo yadauke ni pls daddy

Kinason zama dashi eh daddy to karkidamu zanje insame shi to nagode daddy yashafa kanta badamuwa mamana yanzu kije kiyi wanka kici abinci sekikwanta kinji ko tam......

Ta tashi tashiga dakinsu bayan tafito wanka tasaka dogon rikan lace taje kitchen tadebi abinci kadan taci takoma daki.....

Haydar natsaka da aiki a office se secretary shi tashigo sir kanada bako wayene yace incema sirikinka ne,

Ok shigo dashi......

Yana shigowa yamike tsaye barkada zuwa alhaji yauwa general aliyu ya aiki alhamdulillah masha Allah.....

Naga kadawo min da zahra kuma tabani labarin abunda yafaru tsakanin ku abin dayasa ka aure ta da inda kakai ta duk tabani labari, da yanayin yanda ka kyautata mata, ka aureta ne dan ka dauki fansa kuma gashi ka dawo da ita lafia saboda yanayin kirkin ka. Yanxu ta zo min ne tana kuka........

Ita tafi son ta koma gidan ka wurin iya mai dambu indai har zaka rika zuwa kana dubata, a hakan ne na gane cewa zahra dai is in love with you... Kuma ai ka gyara mun ita duk rashin kunyan nan ta bari kuma duk na dauka laifi na ne ni na bata ta.......

Bcoz ni na nuna mata bata laifi duk abinda zatayi a wurina ba laifi bane, na nuna mata so na nuna mata duk wanda ta taka ba matsala bane ban nuna mata ta girmama kowa ba.........

Saboda duk ni na sangarta ta,..... Toh yanxu ya muke ciki??????

Naji duk abinda kace Alhaji
Eh nasan kaji amma ina jira inji abinda zaka ce, kaji abinda Zara tace, tace ko gidan iyan ne ka maida ita ba sai lalle gidan ka ba...
Sai haidar yaji ya kasa ce ma daddyn zahran baya son ta.
Sai kawai yaji harshen shi ya furta zan zo in same ta...........
*YAR* *HUTU*

*BY* *YAR* *MUTAN* *KAGARA*

*PAGE* *47* */* *48*

Ta tashi da gudu ta shiga daki, washegari tunda Zahra ta idar da sallan asuba ta shiga kitchen ta shirya musu breakfast mai rai da lafiya.

Ko da mummy ta fito qarfe bakwai domin shirya breakfast Sai ta samu komai a Jere a kan table,,, parlor ma a share sai tashin kamshi.

Hatta kitchen din ta ma a gyare fes, Duk abubuwan da a kayi amfani da su an gyara komai.

Mamakin ta bai karu ba sai da ta shiga dakin su Zahra, Sai ta sami Khadija kwance a kan gado Tana bacci yayin da ta ji motsin ruwa a toilet alamun Akwai Mutum a ciki.

Sai ta sauka ta koma falo Tana jiran fitowar Zahra,,, Ba da dadewa ba sai ga Zahra Na saukowa ta ci adon ta Cikin wani green material Ya karbe ta kamar a jikin ta a ka dinka.

Mummy ta sake baki Tana Kallon Zahra, da mamaki ta ke cewa "What am I seeing? Is this my Zahra or am I dreaming???

Zahra Na karasowa ta rungume mummy sannan ta durkusa har kasa ta gaishe ta.

Ita dai mummy har lokacin mamaki ne fal a fuskar ta,,,, ta sake cewa "this is unbelievable, Zahra is this you???? Sai ta daga hannu sama gami da cewa Allah nagode maka,,, Allah Nagode. Ban San wani irin godiya zan yi ma wannan Yaro Haidar ba.

Sai ga daddy Ya fito shi ma Cikin Shirin sa Na Zuwa aiki.

Ya ce wannan kamshin fa da ya cika min hanci tun ina Cikin daki Na menene????

Uhmmm Alhaji you won't believe it,,, Zahra ce fa,,, ka zo dining mu duba mu gani domin Nima Kai nake jira ka zo mu bude tare.

Suna Zuwa suka zazzauna,,, Zahra ta karaso domin ta yi serving din su. Tana bude kulolin daddy Ya ce "wai wai wai mamana yanxu ke ce kika yi wannan? Toh yi sauri ki zuba min duka Ni sai Na ci.

Ta zuba ma daddy kunun gyada da alele wanda ya ji kwai da nama.
Suna ci suna santi,,, Zahra kuma Tana Dariya.

Daddy Ya ce Gaskiya Haidar yayi min kokari domin Ya gyara min manana.
Sannan Ya sace zuciyar mamana,,, Zahra ta yi saurin rufe fuska Tana murmushi.

Bayan ya gama ya goge baki da tissue Ya Mike Ya ce mamana wani delicious za a shirya mana da lunch.

Sai ta ce daddy kar ka damu zan shirya maka favorite din ka.

Sai ya ce Toh mamana sai Na dawo. Mummy ta Mike ta raka Mijin ta har wurin mota ta yi masa fatan alkhairi ta dawo.

Khadija da sauri ta sauko da night gown a jikin ta,,,
Mummy ina Cikin bacci na ji wani kamshi ya daki hanci na har ya hana Ni bacci. Na ce Toh dole sai Na sauko na ga me ke faruwa a kitchen din nan.

Mummy ta ce Hmmmm Khadija Nima haka na farka na ji wannan kamshin, Zahra ce ta tashi yau tun asuba ta hada mana breakfast har Kala uku. Ga su nan a dining suna jiran ki.

Khadija ta zaro ido "Toh mommy 😳Yaushe Zahra ta iya dafa ko ruwan tea da za ta yi breakfast har Kala uku,,,,

Gani ya Kori ji, Je ki gani da idanun ki sannan ki ci.

Ta karasa table ta bude kulan farko sai ta ga farfesun fresh fish hadi da wani daddadan kamshi ya daki hancin ta.

Da gudu ta koma daki ta yi brush ta dawo .

Ta zuba farfesun, ta na kaiwa bakin ta sai ta ji kamar Tana yawo a iska sabida Tsabar dadi.
Ta na ci Tana lumshe ido

Sis Dan Allah fada min, Yaushe kika koya girki har kika iya???

Uhm, Ai duk aikin iya ne da Anty suwaiba domin iya Akwai iya girki,

Kuma duk a sanadiyyar general na iya wadannan abubuwan duka.

Khadija ta ce ai kuwa da Haidar ya zo tuntuni ya dauke ki ya koya maki hankali,, ,amma duk da hakan Mun gode ma Allah mun gode ma Haidar.

Zahra dai Kawai murmushi ta ke yi. Kuma inda a ce da ne,,, da ta Hau khadija da fada.

Lokacin lunch ma ta fada kitchen ta shirya abinci.

Haka rayuwa ta cigaba, kullum Zahra Na kitchen Tana shirya varieties of food saboda ta kware.
Chapter 12 · 0% Book details