Sashe 7
Yancin Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
RITT
*SURAYYERH B.ABDUL*
Dz book completely goes to *HASSAN 90k &HUSSEIN 80k*
Special gift to my besty
*UMAMATU UMAR ADAM*
*____________________________________*
KAINUWA WRITERS
ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*PAge 7*
Tsananin mamaki ne yakama gimbiya jalila ganin irin kallon da muwadda take musu bako kiftawa kuma babu alamun zata gaishe su,,ckn jin haushi da tsana gimbiya jalila da daka mata tsawa da cewa keeee!!!!!,,,A firgice muwadda tadawo hayyacinta,,rikicewa tayi dasauri ta zube ckn rawar murya tace "Barkanku da fitowa gimbiya da yarima,Allah ya huci zuciyar ku,ayimin afuwa",wani mugun tsaki gimbiya jalila taja tanufi dinning yayinda tuni yarima sameer ya saki hannunta ya karasa don ko kallon muwadda baiyi ba tun shigowar su,ganin haka yasa muwadda ta karasa zuciyarta tana lugude kamar zata faso kirjinta ta fito saboda rashin samun mafita,hannunta yana rawa tajanyo plates tashiga saving dinsu,hadadden dambun shinkafar da akaiwa gimbiya jalila wanda yaji vegetables an yanka nama kananu
,,yaji mai sai tashin kamshi yakeyi,shi tazuba musu gabadayansu,,ckn mugun takaici gimbiya jalila ta daga hannu ta zabgawa muwadda mari wanda saida taga giftawar stars jinta yadauke na wucin gadi saboda azabar mari,,ckn fada da murya kasa
wadda ita a wajenta ta masifa ce saboda tsabar jin kai tace " Ke wacce iriyar muguwar dakikiya ce mara hankali???,,mtsww ke kam ai ko kwakwalwar dabba tafi taki amfani,,narantse da Allah idan bakiyi wasa ba saina wulakanta ki,sai na maidaki abar kyama a idon duniya,shegiyar yarinya me idon mayu saikace mayya,saboda jakanta a gidan ubanki kika taba ganin prince dina yaci dambu???,dasauri muwadda tashiga gyada kai,ckn rawar jiki ta tsugunna tashiga basu hakuri.
Duk abinnan da ke faruwa yarima sameer bai kp dago ya kallesu ba,tamkar babu shi a wajen,hasalima wayarshi yake dannawa hankali kwance,sai dai hayaniyar tasoma hawar masa kai,shikam a wajensa ai muwadda batada darajar sa zai ko kalleta ko laifi tayi sai dai yasa a hukunta ta,shifa ko kamarta ma bai sani ba.
Wani irin mugun bakin ciki ne Yakama muwadda na wannan wulakancin da cin kashin da ake mata,,a boye ta share kwallar tausayin kanta da mahaifiyarta,wata zuciyar ce tace mata kibashshi yaci mana idan ma ya mutu Allah yagani bake bace kuma koda sun kasheki kansu sukaiwa,,wata zuciyar ce tace mata nahaifiyar ki fa???Kin ajiye me kula da ita???jitai kanta yamata wani irin masifar nauyi tare da sarawa da yakeyi kamar zai tsage,ganin tarasa mafita ne yasa ckn sanyin jiki tajanyo cooler green rice din tashiga zubawa a wani hadadden plate me shegen kyau,cooler miyar ta janyo ta bude sosai kirjinta ya buga wanda yasata rike kanta da sauri saboda yanda yake mata barazanar tarwatsewa,har wani Abu ne me daci ya tsaya mata a makoshi,,wata dabara ce ta fado mata lokaci guda,amma tana tsoron aikata ta dukda ita kadaice mafitar da zuciyarta tabata ynz,don ko giyar wake tasha bata isa taje tace me babban daki ce tazuba magani a miyar ba,tasan karshe dai abin kanta zai dawo saboda haka dole ta aikata ta batada zabi,dagewa tayi dakarfi tasaki atishawa sai miyau a ckn miya,ba gimbiya jalila kadaiba har yarima sameer saida yadago ya kalleta karon farko,lkc guda tsanar muwadda ta tsarga zuciyar shi,gimbiya jalila kuwa saboda tsananin bacin rai tarasa wani irin hukunci yakamata tayiwa muwadda kallonta kawai takeyi,,jikin muwadda ne yadauki rawa don tasan yau dai kashinta ya bushe ,batai auneba saijin saukar cooler miyar tayi a kanta gabadaya ta wanke mata fuska,batasan lkcn da tasaki kara ba saboda zafin miyar tareda Jan yajin daya shigar mata ido,dakarfi gimbiya jalila ta fuzgi kitson muwadda daya ta jijjiga da karfi ta fincikeshi yafita saiga kan muwadda yana zubar jini,,kuka muwadda takeyi sosai saboda tsananin azaba amma dukda haka gimbiya jalila bataji ko digon takaicin muwadda yaragu a ranta ba,muwadda batai zatoba saijin saukar bulalai tayi ta ko ina saboda idonta yana rufe,gimbiya jalila ce tasa aka kira mata gardawan bayin suke dirkar muwadda tamkar jaka,,ihu takeyi tanason yin magana amma ta kasa saboda tsabar azaba,numfashinta ne yafarayin sama
kawai saita zube a sume .
Mikewa yarima sameer yayi ckn takaici tabi takan muwadda ya taka mata hannu ya wuce don ko kusa baiji ko digon tausayinta ba,,gimbiya jalila binsa da kallo tayi batabi sa ba don tasan bama zai kulata ba,batai yunkurin sawa asake masa sabon girki ba don tasan bama ci zaiyi ba,,bayinnan tasa sukaja muwadda a kasa tamkar kayan wanki suka fita sa ita har lkcn bata farfado ba.
Gimbiya jalila zama tayi akan kujera bayan amfita da muwadda,itadai Allah yasani kwata
batason muwadda ta tsaneta kuma tarasa dalili,canja tunani tayi ta tafi tunanin abinda ke matukar damunta me sanyata kuka wato rashin haihuwa don matuka yana damunta kuma dole tadau mataki akan lokaci.
Bayin nan suna fita da muwadda suka jefata wani daki bisa umarnin gimbiya har zuwa lkcn bata farfado ba.
Bayan yarima sameer yafito kai tsaye bangaren me babban daki yanufa don yaji cewan yarima yusufu yana can,da sallama ya shiga ya isketa itada fulani suna hira,,zama yayi kan kujera shima ya kame,,gaishesu yayi suka amsa,me babban daki fuskarta dauke da murmushin mugunta tace "Dana nakaina ince dai kaci abinci ka koshi???",, Haka kawai ya tsinci kansa da cewa " Eh naci",Dadi ne yakara kama me babban daki tagama da yarima sameer, don haka tace " kuyanga muwadda ce ma tayi maka don ta iyata sosai",, Batareda yadago ba yace " Ok",dagowa yayi yace "ummana wai ina yarima yusufu ne??Naji ance yana nan.
Eh dazu yana nan amma yakoma bangarensa,mikewa yayi yai musu sallama yafita gabadayansu suka bishi da murmushin mugunta,,yana fita me babban daki tace " Saura kiris ka zama gawa don ubanka",,Dariya sukasa hadda tafawa saboda tamusu kyau,ckn dariya me babban daki tace "Bari nasoma murza ido yafara ja yanda zanci uwar kuka d'a zai mutu anjima",Nan ma dai dariya suka shigayi ckn nishadi.
Yana fita yanufi part din yarima yusufu bayinsa na biye da su,,suna zuwa kofar shiga suka tsaya shikuma ya shiga,baya parlour saboda haka kai tsaye ya nufi bedroom, yarima yusufu yana kwance haka kawai tunanin muwadda yakeyi yarasa dalili,shidai ya ajiye a matsanancin tausayin ta da yakeyi,yana ganin yarima sameer yashigo yamike da sauri ckn farin ciki yayi hugging dinsa,shima yarima sameer dadi yakeji don yana kaunar yarima yusufu sosai,zama sukayi a bakin gado yarima yusufu yace " yayana ina shirin zuwa gaishe ka sai gaka da kanka ni da nabari ka huta ne zuwa anjima,dan guntun murmushi yarima sameer yayi yace "Dole nazo ba duba lpyr kani na,naji dadi jikin sa saiki ma,haka suka shiga hirarsu gwanin birgewa,yarima sameer yajima sosai kafin yafito yanufi part din mahaifiyar shi amarya.
Tana zaune a hadadden parlour'n ta itada gimbiya farida da gimbiya maryam kannensa suna hira bayi kuma mata sunada hada
,yana shigowa bayin suka fice bayan sun zube sun mika gaisuwa,,wani kallo ya watsawa su gimbiya farida ba shiri suka mike sukabar parlour'n,,barareda amarya ta kalleshi ba tace " Akanme zaka korar min yara muna hira"fuskarshi yasaki tamkar ba shiba,murmushi yayi yazauna kusa da ita tareda dora kanshi akan kafadarta,ckn shagwaba yace "Ummina yunwa nakeji kibani abinci",, Sosai amarya takejin kaunar dan nata amma dole sai tayi alkunya,zame kafadarta tayi tana fadin " Jeka ga uwakka can me babban daki tabaka ko matarka",Noke kafada yayi irin na kananun yara wai shi a'a,murmushi amarya tayi tareda kawar da kanta,mikewa yayi dasauri tace "Waima tun dawowarka kaci abinci???,A shagwabe yace " Nidai banci ba naki nakeso",,Zaro ido tayi tamike tareda cire alkyabbar bikinta wani uban ubansun lace ne a bikinta onion colour riga da zani yaci uwar kyau,,sosai yaji dadi ganin umminsa tacire kunya dai yau tana masa girki,sosai yaji dadi saboda haka yabita kitchen din dake parlour'n yana tayata wani Abu,wani lkcn ta kulasa wani lokaci ta share shi,shidai yaji dadi kwarai a haka har suka gama girkin sai tashin kamshi miyar tumatir din take,yanata faman hadiyar yawu.*'Y
{Historical fiction}