← Book details Yancin Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 11

Sashe 4

Yancin Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

RITT
*SURAYYERH B.ABDUL*
___________________________________
KAINUWA WRITERS
ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Dz book completely goes to *HASSAN 90k& HUSSEIN 80k*
*Special gift to my besty*
*UMAMATU UMAR ADAM*
*PAGE 4*
Sallama amarya taiwa me martaba ta fita bayan sun gaisa da me babban daki,, sbd tasan idan daya daga cknsu tazo wajen me martaba kuma ba ranar girkinta ba mgn zasuyi .
Zama tayi kusa da me martaba tareda fadin "Barka da hutawa ranka ya dade".
Amsawa yayi da kai saboda Apple dake bakinsa,,ckn kissa tace " Me martaba Ashe dana yakusan dawowa amma ba labari nafara shirin tarbarsa???,,,murmushi yayi sosai da yakular da me babban daki kamar ta makeshi saboda takaici,,ckn annashuwa yace "Auuu dannaki bai fada miki ba??? ai kunfi kusa ke da shi tunda gashi ma harya fada miki yanzu,,haushi ne yakara kamata ganin da tayi dagayin zancen yarima sameer me martaba sai wani washe baki yakeyi,,basarwa tayi tace " Me martaba nazo neman wata alfarma ne a wajenka",,juyowa yayi ya fuskanceta sosai tareda fadin "Inajinki",, Ajiyar zcy tayi tace ", Don Allah me martaba ina neman Alfarmar a fito da kuyanga muwadda daga kurkuku saboda..... Keeeee halima kinsan Abinda kike fada kuwa????,,Me martaba ya fada a tsawace sai da gabanta ya fadi,,,lkc guda annurin fuskarsa ya gushe,ckn fushi yaci gaba" Anya kuwa ba shaye
kika faraba halima???Don nasan bazaki manta wane ni ba da kuma dokata a kasarnan,,narantse miki da Allah babu wani mahaluki da zaiyi laifi nayanke hukunci akansa wani dalili yasa nafito dashi karyane!!! Ai Wannan tozarci ne da wulakanci ace sarki kamata yayi magana biyu,,saboda haka indai kinsan Wannan banzar maganar ne ya kawoshi fitarmin daga daki!!!! Yakarasa tareda nuna mata kofa a fusace,,,Kuka tafarayi ckn kissa da makirci tace "Haba me martaba,,yarima yusufa yanacan fa kurkuku yasa an kulleshi saboda ita ,a cewarshi wai ai tare sukai laifin kuma yace bazai taba fitowa ba har sai kwanakin da aka dibar mata yayi,,Haba me martaba ka dubafa kamar yarima yusufu danka ya kwana a kurkuku ai.......To saime????badai shi yazaba ba???To bari kiji wlh ko shekara na dibarwa kuyanga muwadda yace shima zaiyi babu dalilin da zaisa na fito da ita saboda shi,,ke waima natambayeki mene ne hadin ta dashi???? Ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa har abada.
Ni bansan wata alaka da ke tsakanin su ba,,kuma ma mene zai hadasu kuwa???Tausayi kawai tabashi,,ynz me martaba haka zai zauna a kurkuku cinnakai da komai na cutarwa a ciki???
Daga kafada me martaba yayi yace " Shi yaso hakan ai,,kinga ni zanshiga daga ciki,,yakarasa da mikewa yabar parlourn,, kwafa tayi ckn bacin rai tana fadin ",Inda wancen shegen ne me girman kai ai da zaka fito da ita saboda shi,,kai tsaye kurkuku ta nufa fuskar nan a hade kuyanginta na biye da ita.
Tana zuwa masu gadin wajen suka zube suna kwasar gaisuwa,batareda ta amsa ba takalli babban cknsu cikin raini da nuna isa da gadara tace " Budemin kofa",,mikewa yayi jiki na rawa ya budemata,,dagawa kuyanginta hannu tayi alamun su dakata ita kuma ta shige,,,a xaune ta sameshi yanacin abincin da ake bawa yan prison din,,dasauri ta karasa hankali a tashe ta dauke kwanon abincin ckn tsananin bacin rai da jin haushi tace "Meye haka wai kakeyi yusufu????Ko ka haukace ne???Wane dan iskanne yakawo maka Wannan wulakantaccen abincin kaci??Kawar da kanshi yayi batareda yace mata komaiba,,haushi ne yakara kamata a tsawace tace " Baka jina ne zakamin banza ina maka mgn???",,Dakyar yabude baki yace "To mama me kikeso nace miki???,,Tambayar ka nayi wane dan iskanne yakawo maka Wannan wulakantaccen abincin????,,Murmushi yayi yace " Mama wulakantacce fa kikace???Karki manta abincin da mutane sukeci ne fa kuma ai nima mutum ne kamar su sannan....Dalla rufemin baki sakarai kawai!!!Wai ni anya kuwa ba sauyo min kai akaiba da na haifeka,,yaro kwata
kamar ba jinin sarauta ba,, to wlh kafin na sabamaka ka taso mutafi daga wajennnan akan wata banza mara gata,,ckn kosawa da mgnr ta yace mamaaaa haba Don Allah wai yaza'ai muyita mgn daya???Nace miki babu inda zanje sai satin ya cika Don Allah kiyi hkr ki banni,,,Ckn takaici take kallonshi tamkar ta makeshi sbd takaici,,rasa abinyi tayi kawai sai tayi kwafa tafice a fusace,,binta yayi da kallo a fili yace "Kiyi hkr mama wlh zan iya komai akan muwadda!!! *{Tofaaa}*
Ita kuwa tana fitowa ta kalli ma'aikatan gdn a tsawace tace " Uban waye a cknku yakaiwa yarima wancen dan iskan abincin????,,,Ckn tsoro babban su yace "Wlh ranki ya dade da kanshi yaje dakin girki ya ebo,,wani mugun takaici ne yasake rufeta ganin danta na cknta yarima da Wannan aikin tozarcin,,,A fusace tabar wajen tamkar zata tashi sama.
Iya na zaune ta zubawa kofa ido tana jiran sallamar tilon yarta amma shiru gashi har lkcn dawowarta yawuce kuma tasan muwadda batada tsaye
ko ina burinta tazo gd,,,sallamar ubaida ce ta dawo da ita daga duniyar tunaninta,,gabanta ne yafadi sosai,, dasauri tace " Don Allah ubaida kar kicemin wani Abu Mara dadi yasamu muwadda na bazan juraba wlh",,,Hadiye miyau ubaida tayi ckn tsananin tausayinsu,,kakalo murmushi tayi tace "Kayyyy iyarmu babu komai fa,,zama tayi gefen iya tana fadin muwadda tana lpy gimbiya jalila ce tasata wani dan aiki amma anjima zata dawo,,mikewa tayi tace " Iya nasan yanzu kina bukatar ki kewaya bari na taimaka miki,,ba musu iya tamike ta dafa ubaida takaita bayi,,,rufe ido tayi ta gama abinda zata yi sannan takamota suka dawo daki,,,kwanan da ke gefenta tadauko tace "Iyaa ga abinci kici natawo miki dashi daga gd,,budewa tayi taga shinkafa da miya hadda nama,,murmushi tayi tace " Bakya gajiya da dawainiya ubaida,sannu Allah yai miki albarka,,amma abincin sai muwadda tadawo zamuci,,dasauri ubaida tace "A'a iya ai shiyasa ma ta turoni saboda tace hankalinta bazai taba kwanciya ba tabarki ckn yunwa kici kawai ki rage mata,,shiru iya tayi kamar me tunanin wani
Abu,zuwacan kuma sai tafaraci,,ruwa ubaida ta ebo mata tasha sannan ta shimfida mata dadduma ta rada sallar magriba a zaune Don lkcnta yayi kuma dama tadauro alwala.
Bayan iya tagama azhkar ta juyo ta kalli ubaida data idar da tata sallar ynz,,ckn damuwa tace " Anya kuwa ubaida bakina boyemin wani Abu bane??? Muwadda fa bata taba kaiwa hakaba,, dn Allah ki fadamin idan wani Abu ne yafaru, takarashe kamar zatayi kuka,,,riko hannunta ubaida tayi ckn taushin murya da lallashi tace "Wlh dgsk nake miki muwadda tana lpy sai dai tana kurkuku,,ckn matsanancin tashin hnkl iya taja da baya tareda dafa kirji murya n rawa tace kurkuku!!!!!!u.*'Y
{Historical fiction}
Chapter 4 · 0% Book details