← Book details Yancin Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 11

Sashe 5

Yancin Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

RITT
*SURAYYERH B.ABDUL*
Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSEIN 80k*
```Special gift to my besty ```
*UMAMATU UMAR ADAM*
___________________________________
KAINUWA WRITERS
ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*PAGE 5*
Duk yanda ubaida taso ganin iya ta kwantar da hankalinta abin ya faskara,,don rudewa iya tayi sosai tadinga kuka tana surutai tuni wani zazzafan zazzabi ya rufeta jikinta yahau rawa,,da gudu ubaida taje gida tadauko wani maganin zazzabi tabata,bata jimaba bacci ya dauke ta.
Tagumi ubaida yazuba ckn tsananin tausayin rayuwarsu muwadda,a fili ta furta Allah ya kawo karshen Wannan kuncin rayuwar taku.
Iya fa tariki ce sosai baji ba gani,,babu yanda ubaida bataiba amma inaaa ko abinci iya taki ci sai aikin kuka da kiran muwadda na,,dole ta kyaleta,sai da akayi kwana biyu taga yunwa tana Neman hallakata sannan taci shima kuma kadan.
A bangaren muwadda ma zancen daya ne,,ta rame sosai saboda tunanin mahaifiyarta da rashin sanin halin da take ciki,, tasan dole iya zata shiga mummunan yanayi,,taci kuka tamkar ranta xai fita,,bacci kam sai dai barawo,,sosai kiyayyar masarautar zinsari ta karu a ranta.
Babu yanda me babban daki bataiba akan taga yarima yusufu yafito daga kurkuku amma kekam yaki,,dole ta kyaleshi tana aiko masa da abinci amma shima yaki ci,,sosai take takaicin halin yarima yusufu,,a cewarta bata taba ganin shashashan yarima kamar sa ba.
Yau satin muwadda daya a kurkuku kuma yau ne za'a fitar da ita daga kurkuku,,hakanan kuma yau ne ake shirye shiryen dawowar yarima sameer daga south Africa gobe,,,a Daren ranar duk satar bacci haka yaga muwadda ya kyale har garin Allah ya waye.
Tana zaune ta hada kai da gwuiwa tana sana'ar tata taji an bude kofar,,dasauri tadago kanta taga wani bafade yana bude kofar kurkukun,,mikewa tayi tamkar wadda aka tsikara tayo wajen kofa,,ckn tausayawa yace mata jeki an sallameki gobe sai a kiyaye,,ko karasa jin abin da yake fada bataiba tafice da gudu burinta kawai taganta a gida ko ganin gabanta batayi da kyau bata Ankara ba taji tayi karo da mutum,,dagowa tayi idonta yasauka akan gimbiya jalila,,dasauri muwadda ta zube jiki na rawa tafara bawa gimbiya jalila hakuri,,wata kuyanga ce tadaga hannu zata zabgawa muwadda mari gimbiya jalila ta daga mata hannu,,kallon wulakanci da kaskanci take jifan muwadda dashi,,kamar wadda akaiwa dole tace "Tashi ki wuce",,, ba muwadda kadaiba hatta sauran kuyangin sai da suka cika da matsanancin mamaki,,godiya muwadda tadingayi har saida gimbiya jalila tawuce sannan taci gaba da gudunta tafice daga masarautar.
Gimbiya jalila kuwa abinda yasa ta kyale muwadda saboda tana farin cikin Prince din ta zai dawo gobe shiyasa zuciyarta take kyall.
Kamar kullum yau ma ubaida na zaune tana lallashin iya sai ga muwadda tafado gdn da wani matsanancin gudu kamar wacce aka jefota kai tsaye ta nufi iya ta rungumeta tareda sakin wani irin matsanancin kuka,,itama iya tuni ta fashe da kuka,ido ubaida tasa musu ckn tausayi bata hanasu ba tasan ko tabasu hakuri a banza,,sai da sukayi mai isarsu sannan muwadda tazame jikinta tareda kallon iya ckn bakin ciki tace " Iyata kiyi hakuri don Allah da kuskuren da na aikata aka rufe ni,duk kokarina na ganin na kaurace masa sai da abinda nake tsoro yafaru,,iyata kalli fa yanda kika rame ai da bakisa damuwa a ranki ba tunda zan fito.
Murmushin takaici iya tayi tareda girgiza kai tace "Muwadda na kenan,, taya kike tunanin hankali na zai kwanta???Kalli fa yanda kikai wata iriyar rama sai haske kema.
Hawayen da ya zubo mata tashare tareda fadin " wlh iya ta bazan daina fada ba natsani masarautar zinari,,bantaba ganin azzalumai masu son kansu kamar su ba,,dasauri ubaida tace "muwadda tun ranar da aka rufeki fa yarima yusufu ma yarufe kansa yace ai tare kukai laifin,babu yanda me babban daki batai dashi ba yafito yaki hala ma yafito ynz bansaniba.
Mamaki sosai muwadda da iya sukayi,,tabe baki muwadda tayi tareda mikewa tana fadin " Wannan kuma bangaren su ne bai shafe ni ba,,fita tayi daga dakin tanufi bandaki,,a ranta tana kara girmama matsayin ubaida a gunta don daga gani tana kula da mahaifiyarta tunda ko ynz da taxo akwai abinci me kyau a gaban iya duk da bata ci ba,,sai bayan maghriba sannan muwadda taraka ubaida hanya ta tafi gida bayan inna tagama shimata albarka,,ko a hanya haka muwadda tadinga yiwa ubaida godiya har saida tace "Idan kika cigaba damin godiya zanga kamar baki dauke ni yar iya ba nima" Sannan muwadda ta baryimata gdy.
Yau gabadaya masarautar zinari ta kacame da hidimar tarbar yarima yusufu,,zuwa ynz labari yabaza ko ina a garin,,mutanen gidan farin ciki tamkar bakinsu zai yage,yayinda wasu dayawa suke yake.
Su muwadda suna bangaren girki don ita dama aikinta kenan a bangaren gimbiya jalila kuma,, girkuna akayi sosai kala kala,,suna ckn yi saiga me babban daki,, zubewa sukayi sukahau gaisheta tana wani yamutsa fuska kamar taga kashi,,ckn gadara tace "idan wani tsautsayi yasa kukai kuskure a girkin dana wlh saina baku mamaki saboda haka ruwanku ne ku kula,,karasawa tayi tana bude kulolin abincin tana gani,,fakar idonsu tayi ta shammace su ta zuba magani a miyar tumatir din da akai masa don tasan yana sonta sosai kuma sai yaci,,daukar kular miyar tayi tana jijjigawa tareda fadin " Kun tabbata miyar nan dai tayi ko??"
Dasauri suka amsa mata da eh ranki ya Dade,Ajiye kular miyar tayi tana wani irin murmushin mugunta da samun nasarar babu wanda yaganta a cknsu gashi tayi abinta ckn kankanin lokaci,a ranta tace "Zakasan bakada wayau yarima sameer,,ficewa tayi daga kitchen din bayinta dake kofar ckn din suma suka bita.
Gimbiya jalila taci kwalliya sosai tamkar wadda zataje gasar kyau,,wani murmushi ne na musamman kwance a fuskarta,,kai tsaye fitowa tayi daga part dinta don zasuje tarbo yarima sameer ynz, kuyanginta na biye da ita,a fada suka hadu da me babban daki da yarima yusufu da gimbiya jidda da gimbiya farida tareda mufeeda daketa rawar kai tana zumudi,,fitowa sukayi aka bude musu motoci suka nufi airport tareda masu rakiyarsu anata busa algaitu da sarewa.
Shi kanshi me martaba farin cikin sa yagaza boyuwa,hakama amarya(mahaifiyar sameer),,sosai me babban daki take jin haushi kamar ta shake su saboda takaici.
Basu jima da zuwa ba jirginsu yarima sameer ya sauka,,baza ido gimbiya jalila tayi tana hangen Prince dinta,,can ta hangoshi yana takawa cike da tsantsar takama da nuna iko tareda ji da kai,, kyakykkyawa ne na gaban kwatance,fari tass me hade da rantsatstsen hutu da jin dadi,,duk karshen ji da kai na mace taga yarima sameer sai tayi sha'awar ace nata ne,kallo daya zakai masa ka fahimci yana da tsananin Jan aji,,yana sanye da kayan gidan sarauta da alkyabba wanda sukai masifar yimasa kyau,,bayansa da gefensa da gabansa duk bayi ne,sosai airport din takaure da busa,kowa yasan da dawowar yarima sameer yau,,masu saukowa daga jirgin Kansu sarewa sukeyi suna bashi hanya ckn girmamawa,,da gimbiya jalila idonsa yafara karo,ta kafeshi da idobckn matsananciyar kaunarshi kamar ta cinyeshi saboda axababben so,,murmushin shi me tsada yasakar mata ckn kaunarta sannan yakai dubansa ga me babban daki yasakar mata murmushi, a lkcn yakarasa saukowa,tuni bayi suka zube suna gaisuwa hadda wadanda ma ba nayi ba amma ko arzirin kallo basu samu ba,, da dan gudu gudu gimbiya jalila ta karaso ta rungume yarima sameer ckn tsananin farin ciki,,fuskarsa dauke da murmushi ya shafi gashin kanta sannan ya dagota yacireta daga kirjinsa yayi hugging din me babban daki daketa faman zabga yake amma kasan ranta jitake tamkar ta shake yarima sameer ya mutu ta huta,amma saita dake ta nuna masa farin cikin ta sosai,,gimbiya farida da gimbiya Jidda ne suka gaishe shi ba yabo ba fallasa ya amsa,,ckn tsananin iyayi mufeeda tace "Barka da dawowa ranka ya dade",Ai ko arzikin kallo mufeeda bata samu ba a wajen yarima, sai ma janyo gimbiya jalila dayayi jikinsa yacewa me babban daki " Mutafi gida mama",,Sosai mufeeda ta shaka don a gaban bayi yai mata haka,, kwafa tayi a ranta tace "Wlh sai ka raina kanka yarima ,ni da kai muzuba mugani.
Haka suka dunguma gabadayansu suka nufi gida.*'Y
{Historical fiction}
Chapter 5 · 0% Book details