← Book details Yancin Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 11

Sashe 2

Yancin Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

RITT
*SURAYYERH B.ABDUL*
Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSAIN 80k*
*Special gift to my besty*
*UMAMATU UMAR ADAM*
___________________________________
KAINUWA WRITERS
ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*PAGE 2*
Bismillahirrahmanirraheem.
Sunjima sosai a tsugunne kafin abada umarnin mikewa.
Sarki Aliyu da iyalansa suna zaune akan wasu hadaddun kujeru masu tsananin kyawu gefensu bayi nayi musu fiffita sai kuma wasu a bayansu wasu a zaune a gabansu,waziri ne yamike tsaye tareda yin bayani kamar haka:
"Sanin kanku ne cewa a kowace shekara a masautar nan ana dibar bayi guda 50 a yanta su,,To ynz ma Allah yakawomu lkcn saboda haka ynz ba bata lkc za'a gabatar dasu,ihu mutane sukasa ckn farin ciki tareda jerowa masarautar kirari,,,tunda waziri yafara mgn kirjin muwadda yake bugawa tanajin ance ynz za'a fara kiran sunan wadanda za'a yanta kafafuwanta yayi mugun sanyi kamar zata zube amma ba dama,don babban laifi ne a masarautar sarki yana zaune ka zauna kaima.
Wani bafade ne yamike da zungureriyar takarda a hannunsa yafara kiran sunan wadanda aka yanta,,wajen yayi tsit kowa kirjinsa yana bugu saboda fargaba,,tuni muwadda tagama sarewa ganin an kirawo mutane 46 amma ba sunanta,wasu hawaye ne masu matukar zafin gaske suka shiga tsere a kuncinta,sosai zuciyarta take suya da radadi,bata kara tsinkewa da lamarin ba sai da taga ankira mutum ta 50 ubaidah,ihu suka dauka ckn farin ciki,,tuni wajen yakaure da kide
na farin ciki.
Zamewa tayi tafice daga wajen,ko gabanta bata gani dakyau saboda tashin hnkl,,can gefe da fadar tasamu wani dan dandamali ta zauna tareda hada kai da gwuiwa tasaki wani azababben kuka mai cin rai,,Babu abinda yafi damunta sama da kula da mahaifiyarta,inda akwai yanda zatayi jitake dauke mahaifiyarta zatayi su gudu daga Wannan bakar kasar,ynz haka zata kare rayuwarta a bauta??,,kuka take sosai harda sheshsheka tanajin wata muguwar kiyayyar masarautar zinari.
Tundaga nesa yarima yusufu yahangota kuma ya ganeta,,da kai yayiwa bayin da ke biye dashi alamar su koma,ba musu suka juya,,tsayawa yayi akanta yanajin yanda take garsheken kuka,runtse idonsa yayi saboda kukan yana taba ransa,zama yayi kusa da ita ckn daddarar muryarsa me sanyi yace *MUWADDAAAT*,,dasauri ta dago tareda ja da baya tana kalle
,,Ajiyar zcy tayi ganin ba kowa a wajen,,ckn sanyin murya me cike da tsoro da rauni tace "Don Allah yarima ka taimakamin ka tahi kar nashiga matsala",,, murmushi yayi ckn tsokana yace " Kinhiya tsoro muwaddatt to sai me don anganmu???ynz dai fadamin me kikewa kuka???,,,,mikewa tayi tsaye idonta har yaciko da kwalla,ckn raunin murya tace "Bakomai", tana kokarin barin wajen,,dasauri yasha gabanta tareda kallonta ido ckn ido yace " Baxan iya yafewa zuciya ta ba indai har naganki ckn damuwa kuma nabakki a cknta,saboda haka ki fadamin abinda akai miki ko kuma kiyi murmushi nagani,,babu yanda ta iya dole tayi murmushin da ke kara mata kyau tana mamakin karamci irin na yarima yusufu bakamar sauran yan gdnba,shima murmushin tareda fadin "ko kefa,ni ynz zamuje kilisa ne ina tunanin kafin badawo kin tahi ne??daga mai kai tayi alamun eh,tanayi tana waige
don Allah Allah take yatafi kar wani yagansu,,sallama yai mata yatafi,Ajiyar zuciya tayi don ita har ga Allah batason yarima yana rabarta don babban tashin hnkl ne a wajenta.
Ubaidah ce ta hangota dasauri takaraso wajenta tareda rikota ckn tausayi tace " kiyi hkr kinji muwadda??Allah yasa haka shiyafi alkhairee,,, Hawayen fuskarta ta share ckn rawar murya tace "Ubaida ynz a haka rayuwar iyata zata kare babu cikakken me kula da ita???karki manta ni kadai fa gareka,,Wlh bantaba tsanar wasu mutane ba sama da ba masarauta....dasauri ubaida tarufe mata tareda juyawa tana kalle
da addu'ar Allah yasa ba wanda yagansu,,ckn sanyin murya tace " kidaina irin magannan muwadda,Allah yana sane da iya kuma..... Shiru tayi sakamakon jin sanarwa da akeyi daga ckn masarauta na ana neman kowa da kowa ynz a fada,Ajiyar zuciya muwadda tayi tanajin gabanta na faduwa,Jan hannunta ubaida tayi suka nufi ckn fadar data cika tayi dankam,,Sarki Aliyu yakame akan kujerarsa fuskarsa a hade ynz sabanin dazu da akwai dan annuri,lkc guda jikinsu yayi sanyi kowa yana tsoron abinda yafaru,,waziri ne yamike shima fuskarsa a hade yace ina *KUYANGA MUWADDA??*,,,wani irin masifaffen bugawa kirjin muwadda yayi tamkar zai fado kasa,,karfin hali tayi ta fara tafiya don zuwa gaban fada,,da kallon tausayi ubaida tabita tareda goge hawayen da ta zubo mata na tausayin rayuwar kawar tata kullum cikin matsala,,duk inda muwadda ta gifta sai an bita da kallo har takarasa gaban fada ckn girmamawa ta tsugunna ta sunkuyar da kanta,,wani bafade ne ya taso hannunsa dauke da wata zabgegiyar bulala tanata kyalli,tuni tausayin muwadda yakama daya daga cknsu,,ckn fuskar rashin imani Wannan bafadan yacewa muwadda "Keee baiwa yar gdn matsiyata kinsan mene ne laifinki ????.
Ckn dakiya muwadda ta girgiza kai.
Wani bafade ne yamike dauke da takarda a hannunsa ya karanta kamar haka:" Kuyanga muwadda ta karya doka ta takwas a gidannan karo na farko,an kamata da laifin tsayuwa da yarima yusufu har tana yimasa murmushi saboda haka zata karbi hukuncinta ynz".
Zaro ido mutane sukayi ckn tsananin tausayin muwadda don sunsan babban laifi ne sosai Wannan a masarautar nan.
Tunda bafaden nan yafara bayani har yagama muwadda bata dago kanta ba,banda tsananin suya ba abinda zuciyarta takeyi tuni idanunta suka kame babu alamun hawaye,,Wannan bafaden ne yacigaba da bayani "Kuyanga muwadda zata karbi bulala 20 ynz take,sannan zatayi zaman kurkuku na mako daya.
Sai a lkcn hawaye ya zubowa muwadda saboda tsananin tashin hankalin wane ne zai kula da iyarta???,Dayan bafaden nan me dauke da bulala ne yashiga laftar muwadda babu tausayi sai da yaimata bulala 20 cifff amma ko motsawa batayi ba,, haka akasa wasu bayi mata sukajata a kasa suka nufi kurkuku da ita,,babban daki ne me tsananin duhu ga tarin sauraye da cinnakai,,suna tafiya muwadda tasaki wani gigitaccen kuka tareda zubewa a kasa tana birgima tareda fadin " Nashiga uku!!ya Allah ja kawomin agaji,,iyata bata iya mikewa komai ni nake mata,,wane zai samo mata abinci??wane zai kaita bayi??wazai debe mata kewa??Ya Allah ka taimakamin ka taimaki iyata,kabata juriyar rashina na kwanakin da zanyi a wajen nan,,,haka tadinga kuka tamkar ranta zai fita babu abinda yake kara tasar mata da hankali sama da yanda rayuwar mahaifiyarta zata kasance babu ita.
***************
Tafiya take ckn sassarfa har takaraso kofar shiga part din,da hannu taiwa bayinta alamun su tsaya,kai tsaye tashiga ckn parlourn,wata dattijuwar mata ce fara me matsakaicin kyau zaune akan wata hadaddiyar kujera tanashan fruit din da ke gabanta,kana kallonta kasan tana tsananin ji da mulki da isa,ita kanta matar da tashigo ynz saida ta russuna mata dukda cewa kana kallon shigarta kasan itama jinin sarauta ce,matar ce tayiwa bayin umarnin fita,zama tayi kusa da dayar matar race "Me babban daki akwai babban labari fa".
Ajiye tufar hannunta tayi tareda facing matar tace " Fadamin labarin me??".
Nan da kwana 8 *YARIMA SAMEER* zai dawo kasar nan.
Tuni fuskar matar nan ta fadada da murmushi sosai wanda kana kallonshi zaka tabbatar na tsantsar mugunta ne.wa.*Y
{Historical fiction}
Chapter 2 · 0% Book details